*PAGE* 3⃣6⃣
Yarima wajen k'arfe goma na dare a agogonmu na Nigeria suka fito daga meeting d'in da suka shiga bayan ya koma masaukinsa wanka yashiga yayi sannan yayi shirin bacci wajen 11pm yahau godonsa yakwanta.
zarah ce tafad'o masa a rai sai a lokacin yatuno da ya ce zaya kirata, wayarsa yad'auko ya dad'e yana tunani kamar yakira kamar kar yakirata har ya yi tunanin ya'aje wayar kar yakirata sai kuma yatuna da shi yace zai kira dan haka yayi dialing d'in number d'inta.
zarah da take cikin bacci jin wayarta tana ringing yasa tajanyo wayar tayi picking batare da tabud'e idontaba tayi sallama cikin muryar bacci.
daga chan 6angaren yarima ahankali ya amsa mata,
jin muryarsa yasa zarah tayi saurin bud'e idonta tace ashe kaine?
kin d'auka wanene? cewar yarima.
uhm tun d'azun nake jiranka daga k'arshe bacci yad'aukeni.
murmushi yarima yayi sannan yace muna meeting ne bamu dad'e da fitowaba.
zarah 6ata fuska tayi cikin shagwa6a tace ammah ai darene,
yarima dogon numfashi yaja sannan yace wai ma ina kika samu contact d'ina da nake using da ita?
cikin shagwa6a tace au nadameka ko saisa kake tambayar inda nasamu contact d'in?
shuru yarima yayi nad'an lokaci sannan chan yace no bahaka nake nufiba naga bakyada contact d'inne.
zarah ma shuru tayi sannan tace kanaso kasani ne?
A gadarance yace no sanin baida amfani indai kinso sai kifad'amin.murmushi zarah tayi sannan tace ummi ce taturomin lokacin da takirani muka gaisa sai tatambayeni inada contact d'inka wanda kake using da shi india sai nace a'a, toh kaji yadda akayi nasamu.
A tak'aice yace ohk, yayi kyau.
toh yanzu yaushe zaka dawo?
jibi, cewar yarima cike da k'osawa da maganar, sannan yace kikwanta kiyi bacci dare ne.
zarah murmushi tayi tace Allah yakaimu mukwana lafiya.
Allah yasa cewar yarima tare da kashe wayarsa.
zarah bin wayar tayi da kallo fuskarta d'auke da murmushi tace yarima kenan ba dai miskilanciba, daga k'arshe aje wayar tayi tare da gyara kwanciyarta, murmushi kawai take ahaka har tayi bacci.A chan 6angaren yarima ma bayan ya kashe wayar murmushi yayi sannan kuma chan yaja tsaki tare da kashe gloves d'in d'akin yakoma yakwanta.
da safe zarah cike da nishad'i tafarka, dakanta tahad'a breakfast d'inta, bayan tagama list tayi na duk abinda zata buk'ata tabada asiyo mata, dan dakanta takeso tagirka ma yarima abinda zaya ci.
A ranar taje part d'insa tagyara ko'ina k'al takunna turaren wuta nan k'amshi yagauraye d'akin, bayan tagama fitowa tayi takoma part d'inta a ranar tayi snaks masu dad'i, dayawa tad'iba taba d'aya daga cikin baiwarta tace takaima ummi, sannan takuma d'iba tabada tace akaima dada.
dada da ummi sunji dad'i sosai nan sukaita sa mata alkhairi,
a 6angaren sumayya batada lokacin kanta kullum fita suke sayayyar bikki hankalinta kwance, ji ma take kamar kar yarima yadawo dan tasan idan yadawo zai sa mata ido a k'arshema zai dinga hanata fita.
da dare zarah ta dad'e batayi bacci ba tana ta shirye-shiryen tarbar yarima sai wajen 11pm takwanta cike da zumud'i ita kanta bata iya cewa ga dalilin da yasa take murnar dawowarsa.
A chan 6angaren yarima ma haka cikin ransa yanajin dad'in barin k'asar da zasuyi badan komai ba sai dan yakoma k'asarsa tahaihu sannan yana da burin ganin iyayensa musamman ma memartaba _(Nidai nace toh su matan naka baka son ganinsu ne?🤭)_
tun da asuba da zarah tayi sallah bata koma bacci ba, shirye-shiryen tararsa kawai take, girki tad'aura kusan kala ukku sannan tahad'a drinks suma kusan kala ukku wajen 12 tagama, saida taje tak'ara gyara part d'insa tatabbatar da komai yayi yadda takeso sannan tasa aka d'auki girkin da tayi aka kai part d'insa.
![](https://img.wattpad.com/cover/185049970-288-k834826.jpg)