*PAGE* 5⃣9⃣
Wajen k'arfe biyu su yarima suka dawo lokacin zarah tana a room d'insu tsaye gaban dreesing mirror tana kwalliya yarima yaturo k'ofan yashigo,
Dagudu zarah taje tafad'a jikinsa cikin wata irin siririyar murya tace sannu da zuwa my prince.
Rungumeta yayi sannan cikin kasalalliyar murya yace yauwa ya gidan?
'Dago kai zarah tayi suka had'a ido tace gida ba dad'i saboda baka nan ammah yanzu da kadawo yayi dad'i.
Yarima baisan lokacin da murmushi yasu6uce masaba yace tsokana ko?
Marairaicewa tayi tace dagaske fa.
Rik'o hannunta yayi yace muje parlour kiga abinda nasiyo miki,
Zarah bata musaba tabisa suka fito parlour.Babban trolly ne tagani aje koda yarima yabud'e cike yake taf da kaya, saman kujera yazauna yace duba kiga.
Zarah bin kayan tayi da kallo sannan tafara d'agawa d'aya bayan d'aya daga gowns ne sai English wears jibgi d'aya da sleeping dress, rigunan tafara d'agawa daga mai budad'en k'irji sai 'yar firit wadda bama zata rufe cibi ba, wasu ma sharashara ne, sai mini skirt da wando atak'aice dai dukkan kayan ba wanda zaka iya zama da su cikin gida bane, saidai in daga kai sai mijinkane.
'Dago kai tayi takalli yarima murmushi yasakar mata yace ya sunyi?
Itama zarah murmushi tayi tace sunmin kyau sosai.
Cikin jin dad'i yarima yace toh kije kigwada, zarah kallonsa tayi tace toh ammah ai kayan bazasu sanyuba cikin gidannan tunda bamu kad'ai bane.
Yarima jingine kansa yayi da kujera sannan yace zasu sanyu man in zaki fita ba sai kidinga d'aura zaneba.
Shuru zarah tayi nan taja trollyn tashiga bedroom da shi, d'auko kayan tayi tafara dubawa tana gwadawa a jikinta daga 'yar riga iya cinya, sai wacce bata rufe cibiba sai marar hannu, gunguni tafara tace inbanda abin Yarima ya za'ayi yasiyo min wad'annan kayan sai kace wata arniya,,,daidai ta d'auko wata zata saka sai gashi ya shigo.
Juyowa tayi takallesa yana tsaye bakin k'ofa ya hard'e hannuwa, murmushi suka sakar ma juna sannan tajuya tasaka rigar,
Kallon kanta tayi ta mirror rigar shara-shara komai na jikinta a waje yake ga iyakar tsawonta iya cinya.
Tana shirin cirewa sai jin yarima tayi ya rungumeta ta baya, lumshe idanuwanta tayi tana murmushi, yarima ta cikin mirror d'in yake k'are mata kallo, ahankali cikin kunnenta yace kinyi kyau baby.
Zarah bud'e idanunta tayi ta mirror suka had'a ido nan tasakar mai murmushi sannan tace nagode,
Gyad'amata kai kawai yayi sannan yajanye jikinsa daga nata, Zarah tana shirin cire rigar yace please kibarta.
Juyowa tayi takallesa sannan tace lunch fa zamuje kayi,
Duba agogon hannunsa yayi sannan yace no zan fara wanka before inyi lunch.
Ohk, bara inje inhad'a maka ruwan,
Yarima baice komai ba yawuce yad'auko towel,
zarah toilet tawuce tahad'a mai ruwan wanka lokacin da tafito ganin yana cire kaya yasa tafito takoma parlour.Zarah tana zaune yafito sanye cikin k'ananun kaya sunyi mai gwanin kyau.
Tsaresa tayi da ido tana kallonsa.
Ganin batada niyar daina kallonsa yasa yarima yace ya dai?Janye idonta tayi cike da jin kunya tare da mik'ewa tace bari incanza kaya muje kayi lunch, ta gefensa tatafo zata ratsa tawuce, jawota yarima yayi tafad'o jikinsa, wani irin kallo yake aika mata da manyan idanunsa kallon da yake kashe mata jiki sannan yace ba sai kin canza kayaba kisaka hijab da zane kawai sai muje.