*PAGE* 4⃣0⃣
Zarah sawa tayi Aysha taje gidansu khairy takira mata ita nan suka zauna suna ta hirarsu cike da jin dad'i da nishad'i.
Bayan sallar isha'i yarima ne ya iso k'ofar gidansu Zarah wayarsa yad'auka yakirata, zarah ganin maikiranta yasa tayi murmushi sannan tayi picking tare da yin sallama,
Daga chan 6angaren yarima amsa mata yayi sannan yace gani a waje,.zarah ahankali tace toh zaka shigo kugaisa da su abbah ko?
Jim yarima yayi sai chan yace kizo kishigo da ni, yana fad'in haka yakashe wayarsa.
Zarah mik'ewa tayi tayafa gyalenta sannan tace ma su abbah ga yarima nan zai shigo sugaisa, abbah yace toh badamuwa.Fitowa tayi waje tagansa zaune cikin motarsa ya jingine kansa a sit d'in da yake zaune sai yafiddo k'afa d'aya a waje inda d'ayar take cikin motar.
Takawa tayi ta isa inda yake tarik'e k'ofar motar tare da yin sallama.
Yarima bud'e idanuwansa yayi da suke lumshe yakalleta, ahankali ya amsa mata.
Murmushi zarah tayi tace sannu da hanya ya aiki?
Yarima saida yajanye idonsa daga kallonta sannan yace Alhmdllh.
Bismillah kashigo kugaisa, cewar zarah.
Ahankali yarima yafito daga motar yamaida yarufe chan kuma sai yabud'e yad'auko hularsa yasaka, kallon zarah yayi da tatsaresa da ido yace kallon fa?
Fuskar zarah d'auke da murmushi tace kayi kyau
'Dan guntun murmushi yarima yayi sannan yace kema haka.
Dariya zarah tayi tace ni kyaun mi zanyi ai kafini.
Yarima ma kallonta yake yace shikenan mushiga dare yakeyi,
Zarah tsayawa tayi tace wuce gaba sai inbiyoka.
Harararta yarima yayi yace gidankune ko namu?
Murmushi zarah tayi sannan tawuce nan yabi bayanta har cikin gida, da sallamarsa yashiga, nan suka amsa masa.Saman tabarmar da aka shimfid'a masa yazauna, cike da girmamawa yagaishe da abbah da mama suka amsa tare da tambayarsa mutanen gida.
Kansa sunne k'asa yace duk suna lafiya suna gaisheku.
Abbah yace masha Allah muna amsawa.
Sannan rauda da Aysha suka gaishesa, cikin sakin fuska ya amsa masu tare da tambayar rauda ya k'arfin jiki tace Alhmdllh yanzu ta warke.Mama kallon zarah tayi tace kikawo masa abinci man,.zarah mik'ewa tayi tace toh mama.
Murmushi yarima yayi yace Alhmdllh abarsa kawai a k'oshe nake.Kusan a tare su abbah suka mik'e sannan yace a'a yarima nan ma ai gidane bari mubaka waje kaci, nan suka wuce suka shiga d'aki, daidai lokacin zarah tadawo d'auke da kulolin abinci ta aje gabansa sannan tazauna gefensa, tana bud'ewa wani irin k'amshi yadaki hancin yarima nan tafara serving d'insa, bayan tagama kallonsa tayi fuskarta d'auke da murmushi tace bismillah,
Yarima d'aukar spoon d'in yayi yafara cin burabuscon sannan yakalli zarah da take wasa da gefen gyalenta yace ke bazaki ciba?
Kallonsa tayi tana murmushi tace ni naci d'azun,
Daganan Yarima yacigaba da ci, bai wani ci dayawaba yature plate d'in saidai kunun zak'in da yasha sosai,
Zarah kallon plate d'in tayi tace ba dai ka k'oshiba? Bakafa ci dayawaba.
Yarima kur6ar kunun zak'in yayi sannan yace kinsan banason cin abu mai nauyi da dare.
Zarah shuru tayi sannan takwashe kwanukan, bayan ta dawo Yarima kallonta yayi yace kije kiyi ma su abbah magana muyi sallama dare yakeyi.Zarah 6ata fuska tayi tace tun yanzu?
Banza Yarima yayi mata,
Ganin haka yasa tamik'e taje tasanar da su abbah, kusan a tare suka fito, sama-sama suka d'anyi hira sannan sukayi musu sallama, har wajen mota yaya rauda da Aysha suka rakasu, Yarima bandir d'in 'yan 1000 yad'auko yamik'a ma Aysha yace tasiya kayan kwalliya, godia Aysha tayi masa sannan suka tafi.Tunda suka kama hanya ba wanda yayi magana har suka isa gida, yana yin parking d'in motar daidai lokacin sumayya tafito daga 6angaren iyayenta, tsaye tayi fuskarta d'auke da murmushi tana jiran Yarima yafito, zarah ce tafara fitowa sannan Yarima, ganin zarah yasa fara'ar da yake fuskar sumayya tagushe ahankali tace ina Yarima yaje da wannan matsiyaciyar? Watau dakansa ma yake kaita anguwa? tsanar zarah ce taji tak'aru a cikin zuciyarta, batasan lokacin da suka iso inda takeba saidai ji tayi yarima ya ce kekuma daga ina kike?
![](https://img.wattpad.com/cover/185049970-288-k834826.jpg)