31

2.8K 89 3
                                    


*PAGE* 3⃣1⃣

Zarah part d'inta takoma, tana shiga bedroom dinta tamaida tarufe, saman gadonta tafad'a tafara rera wani sabon kukan, tausayin kanta da na iyayenta yakamata ganin yadda ake ci musu mutunci,

a ranar wuni tayi tana kuka saida tagaji dan kanta sannan tahak'ura tayi shuru.

yarima ko da yakoma wajen aikinsa zaune yake a office d'insa ya k'ura ma waje guda ido tunani kawai yake akan yanayin da yasamu zarah kukan da yatarar da ita tanayi har cikin ransa yakejinsa, tabbas yasan ba k'aramin 6ata mata rai akayiba dan d'an zaman da yayi da ita ya d'an fahimci halayyarta, dafe kansa yayi yace sumayya yaushe zaki canza, buga table d'in da yake gabansa da akayine yasa yadawo daga kogon y
tunanin da yalula,

ahankali yad'ago kai yakalli Dr khalil da yake tsaye gabansa, murmushi Dr khalil yayi yace ranka yadad'e kagafarceni tun d'azun naketa sallama naji shuru, kuma naga kayi zurfi cikin tunanin da kake.

murmushi yarima yayi sannan yace Dr khalil me yake tafe da kai?

Murmushi shima wanda aka kira da Dr khalil yayi sannan yace Dr patient d'in da kayima CS ne yafarka.

mik'ewa yarima yayi yai gaba Dr khalil yabi bayansa suka nufi Ward.



yarima ko da yadawo gida, ji yayi yanaso yaga zarah dan baisan halin da take cikiba ammah jin kansa yahana yaje room d'inta.

ko da sumayya tashigo dasauri yad'aga kai yakalleta dan yayi tunanin zarah ce, ganinta yasa yaji wani irin haushi baisan lokacin da yayi tsakiba.

sumayya gefensa tazauna tace my yarima ashe ka dawo?

yarima shuru yayi yakyaleta,
cikin jin haushi tace haba yarima kana fa jina ina maka magana
batare da ya kalletaba yace da ban dawoba ai da bazaki ganniba.
sumayya mamakine yacikata tace kaidai wlh wani lokacin bakasan..... d'aga mata hannu yarima yayi yace kar kidameni dan bana buk'atar yawan magana a wannan lokacin.
kan dole sumayya taja bakinta tayi shuru dan tasan halin gogan nata zai ma iya korarta.


Da dare zarah ce kwance saman bed d'inta har a lokacin tunanin cin mutuncin da su sumayya da mahaifiyarta sukayi mata, murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo sannan tace ya ubangiji kabani hak'urin jure komai wad'annan bayin naka zasuyi min ammah kar kabasu ikon cutar da rayuwata.

yarima ma a 6angarensa dakyar yasamu yayi bacci dan duk yadda zai rufe idonsa zarah ce yake gani lokacin da take kuka, saidai yakalli sumayya da take baccinta hankali kwance.



k'arar wayar zarah ne yatasheta daga baccin da takoma bayan sallar asuba, dakyar tad'auko wayar tayi picking batare da ta duba mai kirantaba, jin muryar Aysha yasa tace Aysha dafatan dai kuna lafiya?
Aysha cike da tashin hankali tace Aunty Zarah gamunan a hospital yaya rauda ba lafiya.

Zarah zumbur tayi tamik'e zaune tace me yake damunta ba dai cikinba?
Aysha fashewa tayi da kuka tace wlh CS za'ayi mata.
Zarah ma rikicewa tayi tace innalillahi wa'innah ilaihiraji'un tun yaushe kukazo?
Aysha tace tun jiya muna nan daman abbah ne yace kar afad'a miki.

Zarah kashe wayar tayi tare da kallon agogo, addu'a tashiga yi Allah yasa yarima bai fitaba, dasauri tatashi tasaka hijab tanufi part d'insa lokacin yarima yana shirin fita.

kallonta yake da mamaki, ahankali tad'an rissina tagaishesa, bata luraba da sumayya da take bayansa tana ta aika mata da harara,

yarima amsawa yayi yace ya dai?
Zarah kamar zatayi kuka tace dan Allah inaso inje gida?
me akeyi gidan?  cewar yarima da yake shirin barin d'akin.

Yarima SuhailWhere stories live. Discover now