*PAGE* 3⃣7⃣
bayan ta gama shirin fitowa tayi kuyanginta biyu suka take mata baya zuwa turakar dada, da sallamarta tashiga parlourn lokacin sultana sadiya da wasu mata ukkune sai dada kawai a cikin parlourn.
daga dada sai matan kawai suka amsa mata ammah sultana sadiya inba hararaba babu abinda take wurga mata har zarah tazauna k'asa cike da girmamawa tagaishesu nan suka amsa mata,
d'aya daga cikin matanne tace sannu 'yanmata kema kinzo kiga abun arzik'in ko?
sultana sadiya ce tayi karaf tace ko kuma tazo gulma ba, dada ce takalli sultana sadiya tace haba 'yarnan ko baki ganetabane? matar yarima fa ce,
murmushi sultana sadiya tayi tace ammah dada bakiga cikinmu tazo tazaunaba ko nan akwai sa'anta?
dada rik'e baki tayi tace oh ni.d'aya daga cikin matan ne tacema zarah matso kusa kiduba ashe surukace, murmushi zarah tayi sannan tamatso sama-sama taduba kayan tana jinjina kai dan k'arshen kud'i an kashesu a wajen anzuba kaya nagani nafad'a, kasa sakin jiki tayi ganin kallon da sultana sadiya takeyi mata dan haka tayi murmushi tace masha Allah, Allah yasa alkhairi,
gabad'ayansu suka amsa da Ameen sannan tayi musu sallama tamik'e tabar d'akin.daga nan tawuce part d'in iyayen yarima, lokacin da tashiga parlourn ummi ce da rahma sai Aunty husna (yayar yarima) zaune suna tattaunawa, gaba d'ayansu suka amsa mata sallamar da tayi,
ummice cikin sakin fuska tace oyoyo daughter,
murmushi zarah tayi tare da zama k'asa cikin girmamawa tagaishe da ummi,nan ummi ta amsa mata, sannan tagaishe da matar da taga tana kallonta, Aunty husna amsa mata tayi fuska sake, rahma ce tamik'e tace ummi bari inshiga daga ciki induba d'unkunan da aka kawo min, zarah ahankali tace rahma ina wuni?
lafiya kawai tace sannan tawuce tashiga bedroom d'inta.
Aunty husna kallon ummi tayi tace ummi wannan fa ammah ban santaba ko?
murmushi ummi tayi tace zarah ce matar yarima itace wadda akayi bikkin baku k'asar,
sannan ummi tace zarah wannan itace yayar yarima itace husna.
d'ago kai zarah tayi tad'an kalleta sannan taduk'ar da kanta.
dariya Aunty husna tayi tace ji wani kicifi miye nawani satar kallona? toh ai kin ganni nadai fi mijinki kyau.
dariya ummi tayi tace kindai fi sa ammah yarimana yafiki.
zarah k'ara duk'ar da kanta tayi cike da jin kunya.
Aunty husna tace haba ummi bama za'a ta6a had'amuba wannan d'an naki da jin kansa yayi yawa ko aurennan fa sai a wajenku nakeji kuma ko da nayi masa magana jiya da muka dawo yace min dai zai kawota,
ummi murmushi tayi tace ai my son abun nasa sai shi.
husna da take kallon zarah tace zarah halan ku ma yana yi muku miskilancin?
girgiza kai kawai zarah tayi alamun a'a
dariya husna tayi sannan tace kina dai karesane, yanzu dai nice babbar yaya dan haka kisashi yakawoki gidana kimin wuni.
ahankali zarah tace toh Aunty husna.
mik'ewa husna tayi tace ummi bari inshiga wajen dada,
ummi tace toh shikenan sai kin fito,
kallon zarah tayi tace zarah kigaishe da kishiyar taki tunda ita batazo muka gaisaba ko da kema d'in da sunan wajen ummi kikazo.
murmushi zarah tayi tace Allah Aunty husna bansan kinzoba da tun d'azun nazo, wucewa husna tayi zata fita tace bawani nan.bayan ta fita ummi kallon zarah tayi tace zarah kinshiga wajen su dada?
zarah cike da jin kunya tace eh ummi naje naga lefe Allah yasa alkhairi,Ameen, sannan tamik'e tace ina zuwa,
bayan kamar minti ukku sai ga ummi tadawo da wata leda saida tazauna sannan tamik'a ma zarah tace ga anko d'inki daman d'azun nake cema rahma zan aiketa takaimiki, zara kar6a tayi tace toh ummi nagode, nan zarah tabud'e hand bag d'inta tad'auko cheque d'in da yarima yabata tace ummi ga wannan ya bamu muyi hidimar bikki.murmushin jin dad'i ummi tayi tace aikam dai kin gode ki aje wajenki.
ummi daman na ashoben ne,
ummi murmushi tayi tace no ki aje, ni nasaimiki ashoben yanzu sai kishirya kije kikai d'inki ko kuma inturo miki madam zainab tazo ta aunaki dan ta iya d'inki sosai, sannan idan kina buk'atar wani abu sai kisa akaiki kisiyo.