*PAGE* 5⃣5⃣Bayan sallar la'asar yarima zaune yake saman cushin daga gabansa table ne ya d'aura laptop d'insa yana dannawa yanayin yadda yamaida hankalinsa gabad'aya akan laptop d'in zai tabbatar maka da abu mai muhimmancine yakeyi.
Sumayya kamar anjefota tashigo d'akin ba ko sallama.
Yarima d'ago kai yayi yakalleta sannan yacigaba da abinda yakeyi,
Takowa tayi ta iso inda yake, tsaye tayi gefensa fuskarta a d'aure tace haba yarima gaskiya bakayimin min adalci.Yarima d'ago kai yayi yakalleta fuskarsa ba alamun wasa yace ke baki iya sallama ba?
Ta6e baki Sumayya tayi sannan tace a inda yadace ake sallama, nidai na fad'a maka kaji tsoron Allah, kuma inma laifi nayi maka ai na baka hak'uri.
Ture laptop d'in yayi gefe tare da d'ago kai yakalleta cikin 6acin rai yace ke matsalata da ke bakida isassar tarbiya yanzu haka ake magana da miji?
Sumayya kallonsa tayi cikin 6acin rai tace nice banda tarbiya? lallai yarima nagode, ammah inaso kasani ba babbar marar tarbiya sai wacchan d'iyar matsiyatar da ka auro wadda talauci yai mata..... yarima a fusace yamik'e tsaye, marin da ya wanka matane yasa takasa k'arasa maganar.
Da mamaki Sumayya take kallonsa tace yarima ni kamara?
Nunata yayi da yatsa yace anmareki ko zaki ramane? Wlh Sumayya kikiyayeni na fara gajiya da wannan haukan naki, kuma wadda kike kira matsiyaciya Wlh ta fiki daraja a idona dan kwatakwata yanayin tarbiyanku ba d'aya bane,
Sumayya fashewa tayi da kuka tace wlh ba zan yardaba sai na rama abinda kayimin kuma sai na fad'ama dada saboda wacchan matsiyaciyar ka.... yarima k'ara wanketa yayi da mari yace indai kika k'ara kiranta da matsiyaciya wlh sai na takaki cikin d'akin nan kuma inda sabo toh kin saba had'ani da su dada saidai inaso kisani babu wanda ya isa yasani inyi abinda banyi niyaba, harara yawurga mata sannan yace fita kiban waje ko yanzu in6ata miki rai, shashashar banza.
Sumayya tana dafe da kuncinta tajuya saida takai bakin k'ofa sannan tajuyo tace kasaurareni zaka san ka ta6a Sumayya,,,,tana fad'in haka tajuya tafita tabar d'akin.
Yarima komawa yayi yazauna tare da dafe kansa zuciyansa tana masa wani irin zafi, takaicin Sumayya ne yacikasa cikin ransa yace ina amfanin auren irin wad'annan mata,,, daga k'arshe mik'ewa yayi yaje yashige bedroom d'insa.
Sumayya koda takoma part d'inta kuka take sosai takaicinta duk akan zarah yarima yayi mata mari biyu,,,nan tsanar zarah tak'ara kamata ji take kamar taje takashe zarah kowa yahuta,
Haka tawuni tana kuka, kiran zinat ne da yashigo wayanta yasa tatsagaita da kukan da take har saida takusan tsinkewa sannan tayi picking.
Daga chan 6angaren zinat cewa tayi baby tun d'azun nake kiranki ammah bakiyi picking ba why?
Sumayya shuru tayi, zinat tace hello baby kina jina?
Sai a lokacin Sumayya cikin muryarta da tadashe saboda kuka tace sorry bana kusa.Daga chan 6angaren zinat dafe kanta tayi tace oh my god baby ke kullum bakida aiki sai kuka? Yanzu kuma wa yata6aki.
Sumayya cigaba tayi da kukan, cikin kuka tace dole kice haka zinat bakisan cikin halin da nakeba yau akan wacchan jakkar yarima yai min mari biyu.
Cikin d'aga murya zinat tace mari?
Sumayya cikin sheshek'ar kuka tace eh, wlh ba zan k'yaletaba sai na rama abinda yayimin akanta, inma saboda cikinta yaimin haka toh wlh sai na zubar da shi.
Ajiyar zuciya zinat tayi sannan tace baby kiyi hak'uri gobe zan shigo garin sai musan yadda zamu 6ullo ma lamarin dan wlh bazamu hak'uraba.
Koda Sumayya kuka take ammah kuma bai hanata murnaba, cikin jin dad'i tace dagaske kike baby gobe zakizo?
![](https://img.wattpad.com/cover/185049970-288-k834826.jpg)