2⃣9⃣Zarah ko da takoma part d'inta cike da tashin hankali ta aje kayan abincin nan tafara zagaye d'akin tana tunanin yadda akayi hakan takasance.
k'walama kuyangarta talatu kira tayi, dasauri talatu tazo tazube k'asa tace ranki yadad'e na amsa kiranki.
Zarah kallonta tayi tace talatu ya akayi abincina yakasance da yaji da gishiri alhalin ba haka nayisaba?
talatu da mamaki take kallonta tace ranki yadad'e ban ganeba?
Zarah nuna mata kulolin tayi tace d'and'ana kiji,
kad'an kuyangar tad'ebo takai baki dasauri tahad'e tana zare ido, kallon Zarah tayi tace ranki yadad'e wlh bansan yadda akayiba kuma tare da ke mukaje nakai, wlh ban zuba komai ba.
Zarah cigaba tayi da zagaye d'akin sai chan tace talatu na yarda da ke ba abinda kika zuba nima kaina nasan lafiya lou muka kai abincin, ammah toh wanene yayi min haka?
kallon talatu tayi tace zaki iya tafiya,
nan talatu taduk'a tak'ara kwasar gaisuwa sannan tamik'e taficce daga d'akin.Zarah zama tayi saman cushin inta tare da dafe kai duk yadda taso tatuno ko akwai Wanda yashiga d'akin bayanta ammah takasa, abun ya d'aure mata kai sosai, mik'ewa tayi taje tabud'e freezer tad'auko ruwan sanyi tasha.
A chan 6angaren yarima ko da suka fita key d'in motarsa yad'auka yaficce daga gidan, saida yabiya wajen ummi yaci abinci sannan yafita.
gimbiya sumayya ko da takoma part d'inta murna takeyi sosai nan take shaida ma kuyangarta yadda suka kwashe, cike da jin dad'i mairo tace ranki yadad'e indai kika dage toh dawuri zaki fitar da ita daga gidannan, Indai makircine babu wanda bamu saniba.
gimbiya sumayya jinjina kai tayi tace tabbas naga alamu ai, jakkarta tad'auko tafiddo kud'i tamik'a ma mairo tace ga wannan kyautace nabaki.
mairo duk'awa tayi takar6a tana washe baki tace ranki yadad'e duk ni kad'ai?
gimbiya sumayya yamitsa fuskata tayi tace indai kina tare da ni fiye da hakama zaki zamu.cike da jin dad'i mairo taduk'ar da kanta tace akoda yaushe ina tare da ke ranki yadad'e nagode, d'aga mata hannu sumayya tayi tace zaki iya tafiya, cike da jin dad'i jakkadiya tamik'e tafita.
gimbiya sumayya kwantawa tayi saman gado tana murmushin jin dad'i tace muje a karo nabiyu zarah zaki san ainahin wacece sumayya.
da dare zarah bayan ta shirya cikin shirin baccinta part d'in yarima tanufa,
a bedroom tasamesa lokacin yana kwance yana dannar waya ko kallon inda take baiyiba yacigaba da abinda yake, zarah ahankali tahau gadon takwanta daga gefensa tana kallon fuskarsa cikin siririyar muryarta ahankali tace dan Allah kayi hak'uri da abinda yafaru d'azun wlh nima ba'ason raina hakan takasanceba kuma insha Allahu zan gyara ba zan k'ara bari hakan takasanceba, sai a lokacin yarima yakalleta yaga idanuwanta duk sun ciko da k'wallah tausayinta yakamasa, ahankali yace shikenan komai ya wuce.zarah kanta tamaida saman k'irjinsa tare da rungumesa tana murmushi, cikin shagwa6a tace dagaske ka hak'ura?
murmushi yarima yayi a karo na farko yace eh,
zarah zuba masa ido tayi fuskarta d'auke da murmushi tace kasan wani abu?
yarima ma ido yazuba mata sai chan yace a'a.
shafa fuskarsa tayi tace idan kayi murmushi kafi yin kyau.
yarima jan hancinta yayi yace kin dai fad'ane.
zarah murmushi tayi tace dagaske nake bari ind'auko maka mirror kaduba kagani, tana shirin tashi yarima yarik'ota yace kibarsa kawai.
zarah komawa tayi takwanta tace toh yanzu ka yarda ko?
![](https://img.wattpad.com/cover/185049970-288-k834826.jpg)