*PAGE* 3⃣4⃣
yarima gudu yake sosai da motar tunani yake iri-iri cikin ransa da taimakon Allah cikin k'an-k'anin lokaci ya isa asibiti wani irin ajiyar zuciya yayi lokacin da yahango guards d'insa da motocinsa, wayarsa yad'auko yalalubo number d'in zarah,
zarah da suke zaune suna hira mamakine yacikata ganin yarima ne yake kiranta bin wayar tayi da kallo har saida takusan tsinkewa sannan tayi picking baibari tayi maganaba yace kina ina?
zarah saida gabanta yafad'i Jin yanayin maganarsa, ahankali tace gani a hospital
ohk, kifito kisameni gani a waje,, cewar yarima,,
yana fad'in haka yakashe wayarsa,
guards d'insa cikin sauri sukayo wajen da motarsa take yarima zuge glass d'in motar yayi tare da d'aga musu hannu alamun sukoma, cikin sauri duk suka koma inda suke
yarima kife kansa yayi a steering.zarah cikin sanyin jiki tamik'e ta ma mance da su mama suna wajen saida mama tace ina zakije sannan tajuyo tace mama yarima ne yake kirana, tana fad'in haka tafita tabar d'akin.
tana fita kalle-kalle tashiga yi tanaso taga inda zata gansa,
yarima d'ago kansa yayi yakalleta saida gabansa yafad'i ganin kayan da aka turo masa pic's d'inta sune dai a jikinta, wane glass d'in motar yayi sannan taganesa, nuni yayi mata da hannu alamun tazo tashiga.ahankali tatako ta iso tabud'e gaban motar tashiga, shuru sukayi gaba d'ayansu sai chan yarima batare da ya kalletaba yace ina kikaje?
wani irin fad'uwar gabane yaziyarceta ahankali tace ban fahimcekaba?
juyowa yarima yayi yawurga mata harara yace kar kisaki kinemi raina min hankali, da nace kizo asibiti ina kikaje?
zarah gabanta ne yashiga dukan ukku-ukku cikin ranta tace ba dai mutumin nan yasan inda najeba, kodai wani yafad'a masa?
muryar yarima taji cikin tsawa yace kiban amsa mana!
zarah dabarbarcewa tayi tarasa me zata ce masa,
wayarsa yad'auko yabud'o pic's d'in yanuna mata yace wacece wannan?zaro ido zarah tayi tabbas pic's d'intane a tsorace tace wa yaturo maka wannan?
wani irin kallo yayi mata yace ina tambayarki kema kina tambayata?
zarah girgiza masa kai tashiga yi nan k'wallah tacika mata ido, ahankali tace kayi hak'uri wlh ko da naje ba abinda nayi,
yarima d'auke kansa yayi daga kallonta yace daman nace akwai abinda kikayi? ni kawai tambayarki nayi me kikaje yi gidan kuma gidan uban wanene?
zarah fashewa tayi da kuka tace dan Allah kayi hak'uri gidan k'awata ne naje insha Allahu ba zan sakeba.
yarima kife kansa yayi a steering yanajin kukan zarah har cikin ransa, ahankali yalumshe idonsa yace zarah yaushe kika fara k'arya?
zarah tsagaitawa tayi daga kukan da takeyi dan duk a tunaninta yarima ya gane abinda taje tayi rik'o hannunsa tayi tace dan Allah kayafe min wlh ba zan k'araba,
yarima batare da ya d'ago kansaba yace fita kije kiyi ma su mama sallama kizo muwuce gida.
zarah batayi musuba saida tashare hawayenta sannan tafita daga motar, sai a lokacin yarima yad'ago yabita da kallo cikin ransa yace indai nace zan zargi yarinyarnan toh bazan ta6a yi ma kaina adalci ba dan batayi kama da mutanen banza ba.
zarah tana shiga kallonsu mama tayi fuskarta d'auke da murmushi tace mama daman yarima ne yazo shine zamu wuce,
mama tace ai daman k'ara kitafi tunda ai jikin rauda d'in da sauk'i,bud'e k'ofar da akayine yasa duk suka maida kallonsu ga k'ofar, yarima ne yayi sallama yashigo fuskarsa d'auke da murmushi,
gaba d'ayansu suka amsa masa, kujera Aysha tabasa yazaunq
cike da girmamawa yagaishe da mama, nan su rauda da Aysha suka gaishesa, ya amsa sannan yatambayi rauda ya k'arfin jiki?
murmushi tayi tace jiki Alhmdllh ya fara warwarewa dan inaji k'ila jibi zasu sallameni,
![](https://img.wattpad.com/cover/185049970-288-k834826.jpg)