*PAGE* 3⃣2⃣
Yarima bayan yagama duba folder d'in kallon su abbah yayi da suka zuba masa ido yace Allah sarki ashe appendix ne aka cire mata Allah yasauk'e Allah yabata lafiya, gaba d'ayansu kusan a tare sukayi ajiyar zuciya ganin asirinsu bai tonuba sannan sukace Ameen.
nan suka dinga kallon kallo kowa yanaso yasan yadda hakan yakasance ammah banda zarah da dama tasan komai game da hakan.
Yarima kallon Abbah yayi yace abbah indai ba damuwa inaso inmaida rauda hospital d'ina,
abbah Jim yayi sannan yace a'a yarima kabarta a nan kawai ai duk d'ayane kar muk'ara azamaka wani nauyi.yarima murmushi yayi yace abbah wlh duk abinda zanyi muku toh cancantarkuce tasa haka babu wani nauyi da zaku azamin ammah in kunfi son wannan asibitin toh lafiya lou tunda duk d'ayane fatanmu dai Allah tabata lafiya.
gaba d'ayansu sukace Ameen.
haka sukayi ta zama har wajen 5pm ammah bata farkaba daga k'arshe yarima yayi musu sallama yatafi tare da alk'awalin zai dawo da anjima sai sutafi tare da zarah.
zarah taji dad'i sosai da yarima yatafi yabarta, bayan tafiyar yarima ,abbah kallonsu yayi cike da mamaki yace ya akayi hakan takasance wadda akayima C.S ya akayi yakoma operation? anya kuwa wannan record d'in natane?
mama ma ajiyar zuciya tayi tace nima abinda nake tunani kenan me yahad'ata da appendix gaskiya bana tunanin file d'intane maybe mistake akayi aka bamu na wasu.
Aysha ce taduba suna tace lah Abbah wlh file d'in yaya rauda ne saidai abin mamaki record d'inta da aka canza,
zarah da tunda suka fara maganar zuba musu ido tayi batace komai ba sai chan tayi murmushi tace Alhmdllh naji dad'i da hakan yakasance.
gaba d'ayansu ido suka zuba mata abbah yace zarah anya wannan ba aikinki bane?
murmushi tayi a karo na biyu sannan tace mutunci da darajar iyayena shi nafi buk'ata a idon al'ummah dan natabbata idan aka gane halin da yaya rauda take ciki toh ba itaba hatta mu kanmu sai abun ya shafemu,
gaba d'ayansu kallonta suke mama tace zarah toh ya akayi hakan takasance?
zarah labari tabasu yadda sukayi da doctor
Abbah yace Alhmdllh gaskiya zarah kin taimaka mana, hak'ik'a kin siya mana mutunci a idon al'ummah kuma mungode Allah yayi miki albarka.
tabbas tabada gudunmawa a rayuwarmu saidai addu'ar gamawa lafiya kawai zamuyi mata, Allah yayi muku albarka "cewar mama""
gaba d'ayansu sukace Ameen ya rabb.
bayan sunyi sallar magrib zaune suke sun tusata gaba kusan sau ukku nurses suna shigowa suga bata farkaba,
hannunta da tafara motsawa yasa duk suka maida hankalinsu gareta, ahankali tafara bud'e idonta,
dasauri duk sukayi kanta
Aysha dagudu taje takira nurses.nan sukazo sukayi mata injection, rauda ido tazuba musu tana kallonsu suna tayi mata sannu, cike da dauriya tayi musu murmushi ahankali tace zarah kinga yadda Allah yanufa dani ko?
cikin da ban biye ma son zuciya nazubarba sai gashi Allah yak'addara ba rayayye bane babu dai rabon inji kunyar duniya, shuru tayi nad'an lokaci tana hutawa sannan tace aduk lokacin da natuna da rayuwar da nayi a baya ina jin takaicin kaina.
murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo tace saidai naso innuna ma su Alh munir kuskurensu nawulak'antani da sukayi suka nuna cikin banasu bane, naci burin ind'auki d'an inkai musu abinsu....zarah dasauri tasa hannu tarufe mata baki tace haba yayi rauda aikifa akayi miki kidaina yawan magana kuma yakamata kidaina mancewa da Allah masanine akan komai kuma yasan halin da bayinsa suke ciki, daman chan Allah yarubuta cikin ba rayayye bane babu rabon kiji kunyar abinda kika aikata nan gaba dan da ace kin haifi cikin toh duk lokacin da zaki kallesa sai fargaba da tsoro sun cikaki sai kin dinga tunanin idan yagirma taya zaki tunkaresa kifad'a masa ta hanyar banza kika samar dashi, ammah kinga ikon Allah dayake kin yadda da k'addara kuma kinyi tuba maikyau sai gashi Allah yataimakeki yakar6i abinsa shin wannan bai isa yazama ishara agaremu ba?
![](https://img.wattpad.com/cover/185049970-288-k834826.jpg)