*PAGE* 3⃣3⃣
yarima bayan yafito daga wanka yana cikin shiri ahankali yakai kallonsa ga coffee d'in da zarah ta aje masa, murmushi yayi cikin ransa yace wannan yarinyar bansan yaushe zata canzaba.
shigowar da sumayya tayi yasa yamaida kallonsa gareta taku take cikin isa taje bakin gadonsa tazauna,
yarima bayan ya gama shirinsa ko kallon inda take baiyiba yaje yazauna tare da d'aukar coffee d'in yafara sha, sumayya zuba masa ido tayi tana kallo cike da son mijin nata, sai a lokacin yarima yakalleta yace kallon fa?
murmushi tayi tace bakomai, naga kana ta shan coffee ne.
ko zaki sha ne?
me zai hana indai ka bani.
yarima batare da yayi magana ba yamik'a mata cup d'in.
kar6a tayi ahankali takai bakinta takur6a tare da lumshe ido, saida tak'ara kur6a sannan ta aje a bedside fuskarta d'auke da murmushi tace gaskiya kukun nan ya iya aikinsa, naji komai yayi daidai.
murmushi yarima yayi yace da ko ke zance kihad'omin.
'yar dariya tayi sannan tace haba dai toh ai amfanin kukun kenan ni bama zan iyayin irin nasaba gaskiya.
murmushi yayi a karo nabiyu yace sumayya yakamata dai kirage k'uiya dan son jikinki yayi yawa.kwantawa tayi saman gadon batare da tayi magana ba.
shima yarima shareta yayi sannan yakwanta tare da lumshe idonsa shikad'ai yasan abinda yake tunani ahankali murmushi yad'an kubce masa,
sumayya zuba masa ido tayi tana kallon yadda yake murmushinsa ahankali takoma jikinsa tarungumesa sannan tace yarimana komai naka mai ajine,
bud'e idanuwanwa yayi sannan yamaida yarufe ahaka bacci yayi awon gaba da su.wajen k'arfe tara zarah tafarka daga baccin da take a gaggauce tayi wanka tashirya tana shiga kitchen tatarar har anhad'a mata breakfast d'in da tasa kukunta suyi mata wanda zata kai asibiti, fitowa tayi tanufi part d'in yarima ammah da mamakinta tatarar wayam bayanan alamun ya fita, nan hankalinta yatashi saman cushin tazauna tare da kiran wayarsa saida takusan tsinkewa sannan yayi picking, cikin kwantar da murya tagaishesa daga chan 6angarensa ya amsa mata
shuru sukayi gaba d'ayansu sai chan zarah tace am daman dan Allah inaso inje hospital ingano yaya rauda.
yarima shuru yayi sai chan yace bazakijeba.
cikin sauri zarah tace saboda me? dan Allah kar kayimin haka.cike da rashin damuwa yace kinsan dai nan gidan sarautane baidace ace ana ganinki kina yawan fitaba.
zarah marairaicewa tayi tace kataimaka kabarni please
shuru yarima yayi sai chan yace kishirya zanyi magana akaiki.
cikin jin dad'i zarah tace toh nagode sosai Allah yasaka da alkhairi,yarima Ameen yace sannan yakashe wayarsa.
zarah mik'ewa tayi cikin jin dad'i tanufi part d'inta alkyabbarta tasaka sannan tasa aka d"aukar mata basket d'in da tazuba breakfast d'in ciki sannan suka fito.
suna cikin tafiya zasu fita daga 6angarensu daidai lokacin sumayya tadawo daga 6angaren iyayenta, kallon zarah tayi cike da mamaki dan yanayin shigarta ya burgeta sosai harara tashiga banka ma zarah,
zarah ko kallonta batayiba taratsa tagefenta zata wuce,
sumayya cikin tsawa tace ke dabbar inace da bazaki iya bari inwuceba, watau ke kin had'a shimfid'a da mijina kina ganin kamar daidai kike da ni ko? toh bari kiji wlh bazaki ta6a zuwa daidai da gimbiya sumayya ba matsiyaci kawai.zarah murmushi tayi cikin rashin damuwa tace naji nagode, zarah ra6awa tayi tawuce tabar sumayya tsaye tana ta surfa rashin mutuncinta a gaban idonta aka bud'ema zarah mota tashiga aka maida aka rufe.
tana gani motocin suka fita daga gidan,
wayarta tad'auko tayi dialing din wata number.ko da suka isa asibitin su mama suna zaune gefen gadon rauda suna fira sama-sama, zarah da sallamarta tashiga gefenta kuyangintane
biyu,
cikin sauri suka jawo ma zarah kujera tazauna sannan suka duk'a suka gaishe da su mama.