30

3K 120 2
                                    

*PAGE* 3⃣0⃣

da asuba zarah ko da tafarka saida tajawo wayarta taduba tana tunanin zaiyi mata reply ammah batada reply d'in yarima ba, wani irin haushi taji ya kamata ahaka tatashi taje tashiga toilet dan tad'auro alwallah.


  _*WASHE GARI*_

Yarima ne zaune gaban memartaba a fada gefensa  shaheed ne bayan sun gaishesa me marimba gyaran murya yayi yace toh Alhmdllh bakomai yasa nakira kuba saidai inshaida muku waziri yafad'a min sak'onka kai shaheed kuma na amince zan tattauna da iyayenta.

yarima kallon shaheed yayi fuskarsa d'auke da tambaya dan bai fahimci abinda ake nufiba, shaheed janye kallonsa yayi daga yarima tare da k'ara duk'ar da kansa yace godia nake ranka yadad'e, yarima kamar zai yi magana sai kuma yafasa dan bayason shiga abinda bai shafesaba, memartaba ne yakula da shurun da yarima yayi yace suhail kai bakace komai ba.

yarima k'ara duk'ar da kansa yayi fuskarsa d'auke da murmushi yace ranka yadad'e kagafarceni ni ai bansan akan abinda kuke tattaunawaba.

memartaba salati yayi yace kuna tare ammah kace baka saniba?

yarima kallon shaheed yayi yace ko kafad'a min,
shaheed susa k'eya yayi yace kai yarima akan fa soyayyarmu da Rahma.

da mamaki yarima yake kallonsa yace daman soyayya kuke ban saniba?
shaheed kame-kame yafara yace am daman cewa nayi sai daga baya sai infad'a maka.

harararsa yarima yayi sannan yamaida kallonsa ga memartaba yace ranka yadad'e nidai gaskiya ban aminceba sai nayi nazari a kai dan yanzu neman aure sai an fad'ad'a bincike.

yarima kallon shaheed yayi da yasaki baki yana kallonsa, murmushin mugunta yayi yace dan haka sai nabincika kafin inbaka k'anwata.

shaheed marairaicewa yayi kamar zaiyi kuka yace haba yarima kar kayi min haka wlh su daddy, abbah da su ummi bawanda baisan muna tareba kaine kawai baka saniba.

yarima harararsa yayi yace yayi maka kyau dan haka sai kacanza shek'a ammah ba akan k'anwata ba.

shaheed rik'o hannunsa yayi yace dan Allah kayi hak'uri kataimaka min kaifa matanka biyu nima insamu inyi 'yar guda kafasan halina kuma kasan zan kular maka da ita.

d'auke fuskarsa yarima yayi daga kallonsa yace sai kabari sai na tambayeta.

shaheed dasauri yad'auko wayarsa yakira Rahma tana d'auka ko sallama bai bari tayiba yace please Rahma kifad'a ma yayanki kina sona.

yarima faujewa yayi ko da shaheed yamik'o masa wayar yak'i kar6a duk yadda shsheed yaso yarima yayi magana ammah ya k'i daga k'arshe yakashe wayar tare da rik'o hannuwan yarima yace dan girman Allah kataimaka min wlh idan narasa Rahma bansan ya rayuwata zata kasanceba.

Yarima kallonsa yayi nad'an lokaci sannan yayi murmushi yace toh shikenan yanzu nasan zaka iya rik'emin k'anwa, Allah yasa alkhairi Allah yakaimu lokacin.

shaheed cike da jin dad'i yace Ameen babban yaya.

memartaba da yake zaune yana sauraren duk dramar da sukeyi da alamu sun mance da gabansa suke, gyaran murya yayi nan duk suka duk'ar da kansu cikin jin kunya dan sunma mance a fada suke.

murmushi yayi yace Allah yayi muku albarka kuje zan nemeku.

gaba d'ayansu suka sake duk'awa suka kwashi gaisuwa sannan suka mik'e suka fita cikin jin dad'i,

ko da suka fita harararsa yarima yayi yace kai dan bakada kunya kana soyayya da k'anwata ammah baka fad'amin ba,
murmushi shaheed yayi yace ranka yadad'e ai wajenka nakoya kaima fa haka kake aurenka duk bana sani sai daga baya.

Yarima SuhailWhere stories live. Discover now