49

3.4K 93 2
                                    

*PAGE* 4⃣9⃣

Haka sultana sadiya ta isa 6angarensu farin ciki fal a zuciyanta, cikin sa'a ko da ta isa tatarar angama dafa zogalen, nan tasa wata baiwarta tak'wad'a mata, sannan tawuce cikin bedroom d'inta inda tad'auko k'ullin maganin da tasa aka samo mata.

Bayan an gama kwad'on a parlour aka kawo mata cike da jin dad'i tabud'e taduba saida tad'ibi nata sannan tazuba ma sauran maganin tamotse yadda ba za'a ganeba sannan tajuye a cikin wata kula mai kyau, murmushin mugunta tayi tace zarah kinyi babban kuskure da kikayi saurin yarda da ni dan bakisan wacece ni ba,

Sallamar da akayine daga wajen d'akin yasa ta amsa saida tagama abinda take sannan tabada izinin ashigo, jakadiya ce tashigo cikin sauri taduk'a tagaishe da sultana sadiya cike da girmamawa.

Sultana sadiya kallonta tayi a wulak'ance saida tayamutsa fuska sannan ta amsa.

Jakadiya k'ara duk'ar da kanta tayi k'asa tace ranki yadad'e daman dada ce ta aikoni wajenki.

Shuru sultana sadiya tayi na d'an lokaci sannan tace ina saurarenki.

Jakadiya ledar da take hannunta ta mik'a mata tace gashi tace akawo miki.

Kar6a sultana tayi tabud'e batasan lokacin da Murmushi yakubce mataba ganin wata had'ad'ar sark'a da dada ta aiko mata da shi, cikin sakin fuska sultana sadiya tace kice mata nagode.

K'ara duk'awa jakadiya tayi tace Allah yaja da ranki nabarki lafiya,

Gyad'a mata kai kawai sultana sadiya tayi,
Har jakadiya ta wuce zata fita sultana sadiya takirata.

Cikin sauri jakadiya tadawo taduk'a tace ranki yadad'e na amsa kiranki.

Sultana mik'a mata kular tayi tace gashi kikai ma gimbiya zarah.
Cikin sauri jakadiya takar6a cike da mamaki tace ranki yadad'e gimbiya zarah ko gimbiya sumayya?

Harara sultana tawurga mata cikin fad'a tace zarah nace miki ko sumayya?

Jikin jakadiya yana rawa tace kigafarce ranki yadad'e gimbiya zarah zan kaimawa Allah yahuci zuciyanki.

K'ofa sultana sadiya tanuna mata, cikin sauri jakadiya tad'auki kulan tafito.


A chan 6angaren zarah bayan sultana sadiya ta tafi komawa tayi saman cushin tazauna tare da dafe kanta mamakin sultana sadiya duk ya kamata dan yau ne karo nafarko da tafara ganin fara'arta, tunowa tayi da duk wulak'ancin da take yi mata a baya, murmushi zarah tayi wanda ita kad'ai tasan ma'anarsa.

Jakadiya tafiya take ammah mamakine yacikata ahankali take furta miye had'in sultana sadiya da gimbiya zarah? Miyasa batace inkai ma gimbiya sumayya ba sai zarah? Anya ba wata k'ullalliya da matarnan take shiryawa?
Bari dai inje sai inji daga bakin gimbiya.

Lokacin da ta isa a parlour tasamu zarah zaune tana shan fruit salad, cike da girmamawa taduk'a tagaishe da zarah, cikin sakin fuska zarah ma tagaisheta tare da tambayarta su dada.

Murmushi Jakadiya tayi tace suna lafiya sannan tamik'a mata kular tace ranki yadad'e gashi daga sultana sadiya tace inkawo miki.

Murmushi zarah tayi batare da ta kar6a ba tace bud'e mugani.

Cikin sauri Jakadiya tabud'e, zarah lek'awa tayi tace ba laifi kwad'on ya min kyau saidai ba zan iya ciba.

Murmushi Jakadiya tayi tace ranki yadad'e wai miye tsakaninku dan nayi mamakin ganin ta bada kwad'o akawo miki.

Itama zarah murmushi tayi sannan takwashe komai tafad'a ma Jakadiya.

Jinjina kai Jakadiya tayi tace duk tak'are cikinki ne da taji ance kina da shi takeso taga bayansa.

Yarima SuhailWhere stories live. Discover now