*PAGE* 4⃣8⃣
Sultana sadiya dak'yar tasamu tad'an tsaida nutsuwarta sannan tad'an yi d'an murmushi mai kama da yak'e tace ranki yadad'e ya akayi kikasan cikine da ita kuma an tabbata shi d'inne?
Murmushi dada tayi sannan tace tabbas cikine da ita dan rannan k'arnin kifi kawai taji ammah saida tayi amai ke ko yanayinta zaki kallah sai kin gane hakan kuma ko jiya da yarima yazo gaisheni saida namatsa mai da tambaya sannan yafad'amin ashe cikin har ya kai tsawon wata hud'u, kinsan halin yarima ba komai yake fad'aba.
Sultana sadiya saida gabanta yayi wani irin fad'uwa, cikin zuciyanta tace wata hud'u??? batasan lokacin da tace hmm ai yarima ya iya munafunci.
Ganin yadda sultana bilkisu da dada suka zuba mata ido yasa tayi murmushi tace ya za'ayi ni a matsayina na mahaifiyarsa yak'i fad'amin, ai ya kamata tasamu kulawa sosai a wajenmu tunda mune matsayin dangi yanzu a wajenta saboda da mu take zaune.Dada murmushi tayi tace tabbas maganarki gaskiya ce koda munso ace sumayya ce tafara haihuwa ammah bakomai tunda haka Allah yak'addara kuma dukkansu d'ayane tunda duk matansane,
Sultana sadiya cikin rashin nuna damuwa tace ai d'a nakowane da zarah da sumayya duk d'ayane a wajena.
Murmushi sultana bilkisu tayi tace nima haka ina sa rai nan ba da dad'ewaba my dota nima tahaifo mana baby.
Dariya sultana sadiya tayi sannan tace saidai daga baya dan mu nan ba da dad'ewaba zamu amshi jika.
Eh munji babu komai muma namu insha Allahu yana nan zuwa.
Dada ido tazuba musu cikin jin dad'i sannan tace Allah yakawo masu albarka.
Gabad'ayansu suka amsa da Ameen.
Mik'ewa sultana sadiya tayi tana murmushi tace ranki yadad'e zan wuce akwai bak'uwa da zanyi yanzu hakama ina sa ran ta iso, insha Allahu zan je induba jikin my daughter.
Cikin jin dad'i dada tace toh bakomai.
Sultana bilkisu tace sai anjima sultana.'Dan rissinawa sultana sadiya tayi sannan tace na barku lafiya, tana fad'in haka tajuya tafita.
Nan sultana bilkisu da dada suka cigaba da hirarsu, saida maraice yayi sannan sultana bilkisu tayi ma dada sallama takoma part d'insu cike da farin ciki akan cikin zarah.
A 6angaren sultana sadiya ko da tafita bak'in cikine yatokare mata mak'ogwaro, takaici duk yacikata ita kanta ta yi mamakin yadda akayi ta iya danne bak'in cikinta a gaban su dada.
Ko da ta isa part d'inta a parlour tayada zango nan tashiga kaiwa da kawowa ahankali take furta na shiga ukku ya akayi wata daga zuwanta tariga d'iyata samun ciki, kai da sake dole ne inbi ta kowace hanya wajen ganin na zubar da shi, taya wata d'iyar talakka zata fara aje jika a masarautar nan? Ba dai hakan yana nufin plan d'in da nashirya ya rugujeba? Inaaaa hakan ba zai ta6a yuwuwaba wlh, Tsanar zarah sa yarima ne taji ya k'aru a cikin zuciyanta.
Cike da 6acin rai tajanyo wayarta takira sumayya, sumayya na yin picking sultana sadiya cikin d'aga murya tace ke kina ina?
Daga chan 6angaren gimbiya sumayya tace ummah lafiya naji ki haka? Ina gida.
dan ubanki kizo yanzu kisameni ina jiranki.
Sumayya cike da mamakin mahaifiyartata tace toh ummah,
Sultana sadiya bata k'ara magana ba ta kashe wayar tare da wulli da ita saman cushin.Daga chan 6angaren sumayya da mamaki tabi wayar da kallo ahankali ta furta lafiya? Kiran me ummah take min haka cikin gaugawa? Ba abinda yafi d'aure mata kai sai jin yadda ummah tayi mata magana cikin tsawa.
Ahankali tafurta Allah dai yasa lafiya, tana fad'in haka tamik'e tasaka alkyabbarta sannan tafito tanufi part d'in mahaifiyartata.Ko da ta isa a tsaye tatarar da sultana sadiya tana zagaye d'akin tana cize le6e, cike da rud'ewa sumayya ta isa wajenta tace ummana lafiya me yake faruwa?
Ajiyar zuciya sultana sadiya tayi tace sumayya komai ma ya faru.
Cike da mamaki sumayya tace ummana ban fahimcekiba.
Taya zaki fahimceni sumayya bayan kinyi wasa da damarki? Toh gashinan abinda nake guje miki ya faru..."sultana sadiya tafad'i hakan cikin d'aga murya"
Sumayya tsaye tayi tana kallon ummanta cikin rashin fahimtar inda tadosa.
Sultana sadiya ajiyar zuciya tayi tace sumayya kishiyarki tana d'auke da cikin yarima na tsawon wata hud'u.
![](https://img.wattpad.com/cover/185049970-288-k834826.jpg)