👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑_*Written By~Sis Nerja'art*_
*PAGE* 4⃣6⃣
Kallonsu yayi d'aya bayan d'aya sannan yace jiya bayan na fita zarah ta shigo part d'ina?
Gaba d'aya shuru sukayi suna tunani sai chan d'aya daga cikinsu yace gaskiya bata shigoba,
Yarima ido yazuba mai sannan chan yace toh ko akwai wanda yashigo?
Nan ma shuru sukayi, Yarima yace kuyi tunani dai.Chan sai suka kalli juna sai suka eh toh ranka yadad'e gimbiya sumayya ta shigo bayan magrib, gaskiya inba itaba babu wanda yashigo.
Yarima jinjina kai yayi yace kun tabbata? Gabad'ayansu sukace eh ranka yadad'e.
Yarima baice komai ba yawuce yashige,
Koda yashiga parlour saman kujera yazauna tare da dafe kansa mamakin sumayya duk yacikasa ahankali yace idan na fahimta toh duk wani abu da yake faruwa toh dasa hannun sumayya a ciki, toh meyasa sumayya take yin haka? Meyasa takeso taga ta yi silar mutuwar auren zarah? Anya ba da sa hannunta aka zuba poison a abincinba? Wani huci yafitar mai zafi sannan yace koma me kenan da sannu gaskiya zatayi halinta ba zan zargetaba, yana nan zaune a wajen wayarsa tafara ringing ganin mai kiransa yasa yai picking tare da cewa Doctor kin iso?
Daga chan 6angaren tace eh ranka yadad'e gani a waje dogarawa sun hanani shigowa.
Yarima yace ohk, ba d'aya daga cikinsu wayar.
Toh ranka yadad'e, cewar doctor feedoh, nan tamik'a ma dogari d'aya waya, yana d'auka Yarima yace kubarta tashigo.
Jin muryar Yarima yasa yarissina kamar yana gabansa sannan cikin girmamawa yace toh ranka yadad'e angama.
Yarima kashe wayarsa yayi tare da mik'ewa yashiga bedroom d'in tsaye yayi bakin gadon yana k'are ma zarah kallo da gabad'aya ta galabaita, ahankali yazauna gefenta tare da dafa kanta yace ya jikin?
Gyad'amai kai kawai tayi,Mik'ewa yayi yafito waje yasa d'aya daga cikin guards d'insa yaje yazo mai da doctor feedoh, cikin sauri yatafi.
Nan Yarima yadawo parlour yazauna yana jiransu, bayan minti biyar sai ga guard d'in tare da doctor feedoh sun shigo, duk'awa guards d'in yayi yace gata ranka yadad'e,
'Daga masa hannu yarima yayi,
Fuskarsa d'auke da murmushi yace u ar wlcm Dr.
Dr feedoh saida tazauna sannan tace thanks Dr, ya mai jikin.
Alhmdllh yace tare da mik'ewa yace bismillah mushiga daga ciki kidubata,
Ohk sir, cewar dr feedoh nan yarima yawuce gaba tana biye da shi har cikin bedroom d'insa, daga gefen da zarah take kwance yazauna, kallonta yayi da tazuba ma Dr feedoh ido, ahankali yace ga doctor nan zata dubaki.
Fuskar Dr feedoh d'auke da murmushi tace sannu gimbiya, ya k'arfin jikin naki?
Zarah ma d'an guntun murmushi tayi cikin k'arfin hali tace Alhmdllh.
Dr matsowa tayi tana fiddo kayan aikinta daga cikin jakka tace ranki yadad'e ko zaki iya fad'amin abinda yake damunki?
Zarah kallon yarima tayi da shima yatsareta da ido, shafa kanta yayi sannan yace kidaure kiyi mata bayani kinji? d'aga mai kai tayi alamun toh, yana fad'in haka yamik'e yace doctor bari inbaku waje.
Doctor feedoh murmushi tayi cikin girmamawa tace a'a ranka yadad'e kayi zamanka ka ga inda na6ace sai kataimaka min.
Murmushi yayi yace kar kidamu ai nasan aikinki, bakida matsala, yana fad'in haka yafita yakoma parlourYana fita doctor feedoh gefen gadon tazauna, fuskarta d'auke da murmushi tace ranki yadad'e kamar da me dame kike ji?
Ahankali zarah tabud'e baki tace zazza6i da ciwon kai.
Dr rubutawa tayi tace bayansu babu abinda kuma kikeji?
Zarah shuru tayi kamar tana tunani sai chan tace sai kuma yawan kasala da bacci, jinjina kai Dr tayi tace bayansu bakya tashin zuciya?
Girgiza kai zarah tayi.
Nan Dr tarubuta sannan tace toh kina cin abinci?
Ba sosai ba, cewar zarah.
Dr idon zarah d'aya taduba sannan tad'auko wata roba tamik'a mata tace ko zaki taimaka kiyo fitsari nan ciki, saboda akwai awon da nakeso inje yanzu inyo.