👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑_*Written By~Sis Nerja'art*_
*PAGE* 4⃣5⃣
Ahankali yake warwarewa har yagama sannan yabud'e yafara karantawa gabansane yafad'i ganin sunansa aka rubuta da larabci, sai wasu rubutu da shi kansa baisan menene aka rubutaba saboda mitsi-mitsine daga chan k'asa kuma sunan zarah yaga anrubuta sannan daga gefe akasa d'aya ansa _ni zarah zan mallaki yarima_ gabansane yacigaba da fad'uwa cike da mamaki yace zarah ce tasamin laya dan tamallakeni? Me take nufi da hakan? cikin sauri yaje yad'auko na toilet d'in yawarware sunansa da na zarah kawai ne jikin takardar, tsaye yayi cike da mamaki yana k'ara bin takardun da kallo,
Zarah kwance take d'akinta duk kasala ta rufeta tanaso taje part d'in yarima ammah ta kasa saboda batajin dad'in jikinta, daga k'arshe dai daurewa tayi tamik'e tad'auko alkyabbarta tasaka sannan tafito tanufi part d'insa.
Ahankali tabud'e bedroom d'insa tashiga tsaye tagansa rik'e da layar, juyowa yayi yaimata wani irin kallo, cak zarah taja tatsaya cikin ranta tace shikuma wannan mutumin me yake nufi da hakan?
Muryarsa taji ya ce abinda kikayi shirin yi toh bai yuwuba dan haka sai kicanza sabon shiri ammah ni nafi k'arfin duk wani sihiri.Zarah zuba masa ido tayi tana kallonsa cikin rashin fahimtar abinda yake magana a kai, ahankali tace ban fahimci akan abinda kake nufiba.
Yarima wurga mata harara yayi yace kar kimaidani wanda baisan abinda yakeba ko kin d'auka banga layun da kika ajeminba cikin toilet da k'arshin pillow na ba, zarah zaro ido tayi tace ni kuma?
Mik'amata yarima yayi yace toh ai sai kiduba kigani idan k'arya akayi miki, cikin sauri takar6a tashiga dubawa, tsoro da fargaba duk suka cikata, cikin sauri tad'ago kai takalli yarima da shima yake kallonta, muryarta tana rawa tace wlh ban aikataba bansan wanene yake neman jamin sharri ba, innalillahi wa'inna ilaihiraji'un, dasauri taje wajen yarima tarik'o hannunsa k'wallah duk ta cika mata ido tace kayarda dani wlh bani bace nakawo maka laya,
Fizge hannunsa yayi cikin d'aga murya yace idan bake bace toh wanene? Kuma sunan wanene a jiki?
Zarah kallonsa take cike da mamaki tace yanzu ka yarda zan iya yi maka asiri? Cike da rashin damuwa yace toh idan ban yardaba me kikeso inyi?
Murmushi Zarah tayi wanda yafi kuka ciwo sannan tace da ace ni mushrikace da ba akanka zan faraba kuma ba zan ta6a amincewa in aurekaba da tun farko zan san yadda zanyi inga ban aurekaba saboda nima inada wanda nake so, kuma da ace ina asiri da tun farko zanyi maka ba sai munkai wannan lokacinba, wlh nagaji da wannan sharrin da ake ja min komawane yaje dan kansa, tak'arashe maganar cikin kuka,Yarima kallonta yake har takai aya sannan yace idan kin gama zaki iya tafiya dan magangununki bazasu ta6a tasiriba agareni, Zarah d'ago kai tayi takallesa tace bakomai insha Allahu gaskiya zatayi halinta komawanene asirinsa zai tonu, tana fad'in haka tawuce tafita tabar d'akin.
Tafiya take zata koma part d'inta hawaye suna zuba daga idanunta ita kanta batasan inda take jefa k'afartaba, hawaye d'aya na bin d'aya, ahankali take furta ya ubangiji kakawo min mafita a cikin wannan al'amari, ya ubangiji katona asirin duk wani mai nufin sharri agareni, me nayi musu? Meyasa sukeson ganin sun 6atamin rayuwa, wanene yake nufina da sharri haka?
Tuntu6e ne tayi batasaniba nan tatafi zata fad'i, cikin sauri taji an rik'ota tafad'a jikin mutum, d'ago kai tayi cike da mamaki dan ganin kowanene? Ido tazuba ma jakadiya da itama take kallonta, ahankali jakadiya tace ranki yadad'e meyake faruwa dake ne haka?
Zarah runtse idanunta tayi nan wasu sabbin hawayen suka shiga gangarowa, jakadiya cikin sauri tawaiga gaba da bayanta ganin bakowa yasa tarik'e Zarah suka ida isa part d'in Zarah.Jakadiya kallon kuyangin Zarah tayi tace kubamu waje, cikin sauri duk suka ficce sukabar d'akin.
Zaunar da Zarah tayi saman d'aya daga cikin cushin sannan tazauna k'asa gaban Zarah, kallon Zarah tayi da tajingine kanta a jikin cushin d'in hawaye suna zarra daga idanunta, tace ranki yadad'e meyake faruwa da ke ne?
Zarah ahankali tabud'e idonta takalli jakadiya, nan tayi murmushi wanda yayi kuka ciwo sannan tadafe kanta.