*PAGE* 5⃣1⃣
Zarah tana fitowa nan kuyanginta suka take mata baya har cikin gidansu, Zarah dagudu ta isa wajensu mama da suke zaune suna 'yan soye-soye, jikinmama tafad'a tace cikin murna tace oyoyoo mamana.
Mama ma rungumeta tayi cikin jin dad'i tace oyoyoo Zarah na.
Yaya rauda kallon Zarah tayi tace ikon Allah kedai har yanzu baki girmaba.
Zarah turo baki tayi cikin shagwa6a tace yaya rauda na fa kwana biyu banga mamanaba, mama janye Zarah tayi daga jikinta tace rabu da ita zarahna,
Daidai lokacin kuyangin zarah suka iso suka duk'a cikin girmamawa suka gaishe da su mama
Cikin sakin fuska su mama suka amsa musu tare da tambayarsu gida sukace Alhmdllh, kallonsu zarah tayi tace zaku iya tafiya amaidaku gida, duk'awa sukayi sukace to ranki yadad'e angama, mama leda tasamu tak'ulla musu su donut tabasu, nan sukayi sallama da su mama sannan suka mike suka tafi.Zarah kallon mama tayi da tazuba mata ido, murmushi Zarah tayi tare da duk'awa tagaishe da ita.
Mama amsa mata tayi cikin sakin fuska tare da tambayarta mijinta da mutanen gida
Zarah cikin jin kunya tace duk suna lafiya mama.Juyowa tayi tana dariya tace yaya rauda ina kwana? Harararta yaya rauda tayi tace yanzu k'arfe sha biyu zaki kira mana kwana.
Afuwan yaya rauda ina wuni?
Murmushi yaya rauda tayi tace lfy lou ya gidan?
Zarah tace Alhmdllh komai daidai.Sai a lokacin zarah taji k'amshin soyen ya daki hancinta, yamitsa fuska tayi jin zuciyanta yana shirin tashi tace wai banga amaryaba,
Mama tace tana nan d'aki tana k'ullah kunun aya, cikin jin dad'i zarah tace wow bari inje insha har na ji ina son sha, cikin sauri tawuce tanufi d'akin.
Mama da yaya rauda binta sukayi da kallo cike da sha'awa dan ko ba'a fad'a musuba sunsan zarah cikine da ita.
Tana shiga d'akin taja tatsaya, Aysha da take zaune tana k'ullin kunun aya ganinta yasa tataso dagudu tarungumeta tana oyoyoo Aunty zarah, zarah ma dariya tayi tace ke zaki karyani ni sakanni,
Aysha janye jikinta tayi tana dariya tare da zuba ma zarah ido tace Auntyna kinga yadda kika koma kamar ba keba
Murmushi zarah tayi tace ke banson tsokana, amaryarmu ya shirye-shiryen bikki? Allah yasa kar asa mana bikkin nesa.
Dariya Aysha tayi tace wlh Aunty zarah nima addu'an da nake kenan.
Da mamaki zarah takalleta tace lallai Aysha ashe bakida kunya toh Allah yakyauta,,,,tana fad'in haka tawuce tanufi wajen kunun ayan tabar Aysha tana ta dariya.
Zarah zubawa tayi sosai tasha har saida taji ta k'oshi sannan tabarshi.
Duk yadda taso tataya su mama girki kasawa tayi saboda k'amshin tayarmata da zuciya yake, dole tahak'ura tayi zamanta.
Abbah ma koda yadawo ya yi murna sosai da ganin 'yar tasa.
Wajen k'arfe ukku 'yan neman aure sukazo anmusu tarbar mutunci, inda aka tsaida maganar akan nan da watanni hud'u masu zuwa.
Sun kawo su biscuits su alewa bakin gwalgwado sun bada sai kud'in nagani inaso da na neman aure.
ko da abbah yazo musu da labarin su mama sunyi murna sosai nan sukaita fatan alkhairi.
Nan aka zauna aka k'ullah kayan aka d'ibi na dangi sannan aka aika mak'ota nasu.
Mama duk yadda taso zarah taci abinci k'iyawa tayi daga k'arshe saidai tabada aka siyo mata awara nan tazauna taci.
![](https://img.wattpad.com/cover/185049970-288-k834826.jpg)