*PAGE* 6⃣2⃣
*BAYAN WATA DAYA*
Zarah cikinta ya girma sosai dan a lokacin watansa takwas da ta zauna k'afafuwanta har kumbura suke, lalla6ata kawai yarima yake dan indai yana gida baya bari tana komai saidai shi yayi mata.
Yau ma kwance take saman cinyarsa suna kallon wani series film, d'ago kai tayi takallesa tace my dan Allah kataimaka kakira min su mama mugaisa kaga har yanzu bamuyi waya da su ba.
Kallonta yarima yayi batare da yayi magana ba, ganin haka yasa zarah tace ammah Indai kaga da matsala toh kabarsa kawai.
janyo wayarsa yayi yace ai dolema inkirasu dan nasan hali yanzu kin fara min kuka.
Murmushi zarah tayi tace karufa min asiri kai ai d'an alalla6ane ranka yadad'e inba hakaba yanzu mutum ya amsa query.
Hmm haka dai kikace, yanzu dai bari inkirata mugaisa, nan yarima yakira mama cikin girmamawa yagaisheta, bayan sun gaisa nan yamik'a ma zarah.
Cike da jin dad'i zarah tace hello mamana,
Daga chan 6angaren mama tace zarahta.
Murmushi zarah tayi tace ina wuni mama?
Lfy lou zarah, ya gidan,,cewar mama.
Lafiya lou mama nayi missing d'inku kwana biyu.
Daga chan 6angaren mama tace aikam dai zarah kun 6oye, ai muna neman wayanki bata shiga.
Zarah d'ago kai tayi takalli yarima da hankalinsa yana wajen T.V sannan tace eh wayarce tasamu matsala saisa, ina fata duk kuna lafiya ina abbanmu da su yaya rauda?
Mama tace babanku baya nan saidai su rauda, ai muna ta kiranki mufad'a miki munkoma sabon gida.Wata irin k'ara zarah tayi cike da murna tace Alhmdllh gaskiya naji dad'i Allah yasa alkhairi, Allah yatsare sai munzo ganin gida.
Dariya mama tayi tace Ameen y rabb, toh Allah yakawoku lafiya.
Ameen mama, aba su yaya rauda mugaisa.
Nan mama tabasu sukasha hira har suna cewa zasuzo dan sun fitar da anko d'in bikkin Aysha, nan zarah tace a'a kar suzo dan sun d'anyi tafiya ammah idan sun dawo zata nemesu, sun dad'e suna hira sannan sukayi bankwana suka kashe wayar cikin jin dad'i.
Mik'ama yarima wayarsa tayi tace ka gama min komai nagode sosai my soulmate,
Murmushi yarima yayi yace toh yanzu hankali ya kwanta ko?Girgiza kai zarah tayi tace har yanzu da saura, hankalina bai ida kwanciyaba.
Kallonta yarima yayi yace toh menene yayi saura?
Marairaicewa tayi tace dan Allah kakira ummi mugaisa da ita ko tasamu sauk'i a ranta dan nasan duk inda ummi take yanzu bata cikin kwanciyar hankali.
Nan da nan fara'ar da take fuskar yarima tagushe gabad'aya damuwa tabayyana, shuru yayi baice ma zarah komai ba.
Ganin haka yasa zarah tace dan Allah kataimaka koda minti biyune mugaisa da ummi.
Da mamakinta sai gani tayi ya janye mata kai daga saman jikinsa nan yamik'e yashige bedroom.
Da kallo zarah tabisa cike da tausayinsa, nan tamik'e tabi bayansa, saman gado ta tarar da shi kwance yayi pillow da hannuwansa, takawa zarah tayi taje tahau gadon takwanta daga gefensa tare da rungumesa cikin kwantar da murya tace kayi hak'uri mijina idan na 6ata maka rai, nima ba ason raina hakan yakasanceba kawai dai gani nayi yakamata ace koda sau d'ayane ka kira ummi dan nasan a yanzu duk inda ummi takasance toh hankalinta a tashe yake, ammah da taji kana cikin k'oshin lafiya na tabbata hankalinta zai kwanta,
Yarima maida idanunsa yayi yalumshe yana jin wani iri a ransa.Zarah cigaba tayi da cewa kafini sanin yadda ummi takeji a game da kai, kana tunani ko da sau d'aya hankalinta zai kwanta alhali batajin ko muryarka?
![](https://img.wattpad.com/cover/185049970-288-k834826.jpg)