*PAGE* 5⃣8⃣
Koda yayi parking kallon yarima yayi yace ranka yadad'e mun fa iso.
'Daga kai kawai yarima yayi, nan Dr khalil yakalli zarah ta mirror yace gimbiya bismillah mun iso, murmushi zarah tayi cikin muryarta da tadashe saboda kuka tace toh.
Gabad'ayansu suka bud'e motar suka fito, yarima kallon zarah yayi da take taku dak'yar yace ko intaimaka miki?
Zarah batare da ta kallesaba tagirgiza kai, nan Dr mu'az da yarima sukayi gaba tana bayansu har suka shiga a main parlour suka tarar da matar gidan zaune ganinsu yasa tamik'e fuskarta d'auke da fara'a tace oyoyo ga manyan bak'i,
Dr mu'az ne yayi murmushi yace dear yau fa ga prince a gidan namu,
Murnushin jin dad'i tayi tace yau muntaki sa'a gaskiya,Saman kujerun da suke d'akin suka zauna nan matar dr mu'az tad'an russuna cikin girmamawa tagaishe da yarima.
Murmushi yarima yayi sannan ya amsa mata,
Wajen zarah tanufa tana murmushi tace gimbiya sannu da zuwa ina wuni?Murmushi itama zarah tayi sannan tace ina wuni.
Bayan sun gama gaisawa, Dr mu'az yace ranka yadad'e ga d'an akurkin gidan namu ina fata zaku iya rayuwa a cikinsa.
Harararsa yarima yayi yace kai fa tsiyata da kai ka iya tsokana.
Dariya Dr mu'az yayi yace ai gaskiya ce nafad'a,
Kallon matarsa yayi yace jamila gashinan prince yau wani irin farin ciki nakeji da naganni tare da shi, abokina ne tun daga primary har secondary tun lokacin banda komai muke tare da shi, shine silar yin karatuna dan a lokacin iyayena basuda komai mu talakkawane sosai da taimakonsa nayi karatu har nakai wannan matsayin da nake da shi kinga ko taya zan iya mance prince?Jinjina kai matarsa tayi tace tabbas hakane bazaka ta6a mancewa da halacci da yayi makaba, saisa a kullum yana cikin addu'anmu.
Kallonta yarima yayi yace madam kema kin biye ma wannan mijin naki sarkin tsokana.
Murmushi Dr mu'az yayi yace prince kenan kaima kasan gaskiya nafad'a saidai idan kanason 6oyetane.
Shuru yarima yayi baice komai ba.
Zarah dai tana zaune tana saurarensu ita dai burinta takwanta tahuta.
Matar mu'az mik'ewa tayi tace bari akawo muku ruwa kusha kafin agama abinci.
Bayan ta fita Dr mu'az kallon yarima yayi yace ranka yadad'e muje kuza6i part d'in da yayi muku a cikin gidan nan.
Girgiza kai yarima yayi yace no ba sai mun za6aba duk wanda aka bamu munaso yanzu magrib ta gabato muna buk'atar kimtsawa ga madam babu lafiya ina so asamo min drip zansa mata,,,yak'arashe maganar tare da kallon zarah.
Dr mu'az yace ayya Allah yasauk'e bari inje insa asamo daga nan ashigo muku da kayanku, yana fad'in haka yamik'e yafita yabar d'akin.
Yarima kallon zarah yayi da ta jingine kanta a kujerar da take yana shirin yin magana sai ga Matar mu'az ta shigo dan haka yafasa.
A gabansu ta aje k'aton tray d'in da yake d'auke da kayan marmari nan tatsiyaya musu drinks a cups ta aje ma kowa gabansa sannan tace kuyi hak'uri abincin ya kusan zama ready.
Murmushin k'arfin hali zarah tayi tace bakomai Aunty hakan ma mun gode, nan tad'auki cup d'in tafara shan drink d'in.
Nan Dr mu'az yashigo bayansa megadine janye da trollies d'in su yarima d'aya daga cikin rooms d'inne Dr mu'az yasa aka shigar da kayan sannan yakalli yarima yace ranka yadad'e kuduba kuga idan part d'in baiyi mukuba sai a canza.
Murmushi yarima yayi yace kar kadamu yayi mana, kallon zarah yayi yace muje kisamu kihuta.
Jamila cike da tausayi takalli zarah tace sannu gimbiya, Allah yabaki lfy.
![](https://img.wattpad.com/cover/185049970-288-k834826.jpg)