*'YAR SHUGABA👑*
_page_ *1.*
_Na_
*Rahma Kabir*✍🏾Mototaci ne guda uku suke tafe bisa hanya aguje, dukansu gilas d'in motocin masu duhu ne, mota ta farko dake gaba bodyguard ne a ciki.
Sai na tsakiya motar d'auke yake da tsadaddun 'yan mata su uku wanda ba zasu wuce shekaru Ashirin da biyu (22yrs) ba a duniya.
*'Yar Shugaban k'asa ce* Queen Basma, ta hakimce a seat d'in baya ita kad'ai, sai Meena 'yar Governor Kaduna ce ita ke driving, sai Leema 'yar Sarkin Kano wacce take gefen Meena.K'aran wak'ar Music na Larabawa ke tashi a motan, dukkan su suna bin wak'ar tamkar sune suka rerata, sunayi suna rawa da jinsu da kad'a kai, kana ganin su kaga 'ya'yan gata, cike suke da farin ciki fal da nishad'i, domin ba suda wata damuwa ko matsala a rayuwansu.
Motan baya itama na bodyguard ne, suke marawa motan Queen baya.
Wani Matashin Saurayi wanda bai wuce shekara Talatin ba (30yrs), yake tafiya cikin sauri domin ya amso wa Ummansa nik'an masara da k'anwarsa Khadija ta kai ta aje, saboda zata wuce tallan kwai, hankalinsa yayi nisa sosai cikin tunani, baisan yahau kan titi ba. Meena ce taja mugun burki, ji kake k'iiiii kad'an ya rage ta buge shi, Aryan tsayawa yayi cak ya runtse ido yana fad'in *Innalillahi wa inna ilaihir rajuun* jira yake motan ta bigeshi domin ya riga ya sadak'ar motan zata kad'eshi,
Cikin b'acin rai Queen Basma, Leema, Meena duk suka fito a motan, haka bodyguard suka yi parking akan hanya suka fito rik'e da bindigogi, cikin k'ank'anin lokaci suka had'a gosilo, mutane suka fara taruwa, ganin bindiga ne yasa kowa ya kama kansa, Queen Basma ta k'arasa kusa da Aryan bodyguard suka take mata baya, tsadadden k'amshin turarenta ne ya dawo da hankalin Aryan jikinsa, domin ji yayi wani k'amshi na ratsashi, bud'e ido yayi a hankali yayi tozali da kyakkyawar fuskan Queen wanda saida gabansa ya fad'i, nan take tsoro ya ziyarce shi, kallon k'asa da sama Queen Basma ta bisa dashi cike da jin haushinsa, kyamansa taji saboda wani irin warin zufa dake tashi a jikinsa, tattaro miyon bakinta tayi ta tofa masa a jikinsa tare da toshe hancinta da hankacif, juyawa tayi ta kalli d'aya daga cikin bodyguard d'inta, cikin sauri ya k'araso, Aryan baiyi aune ba bodyguard d'in ya kifa masa kyakkyawan mari guda biyu, Leema ce ta k'araso cikin isa tace"Hee, Marin ma kad'ai ya ishe shi" sai ta juya tana kallonsu Meena tana murmushi, ta kuma cewa
"babies mu wuce kar mu b'atawa kanmu lokaci akan wannan mahaukacin, kunsan duk muna da abinyi a gabanmu".
Dakyar Aryan yaja k'afansa zuwa gefen hanya, zuciyansa cike da k'unci, su kuma su Meena suka shiga mota suka wuce.Tsananin damuwa ne Aryan ya tsinci kansa a ciki, sai ya fara zancen zuci yace,
"shi dai talaka kullun shi wulak'antacce ne a idon jama'a, Allah kai ka haliccemu kayimu ma banbantan jinsi, kaine mai girma, ka saka mini da kyakkyawan sakayya" wani guntun hawayen ya sauka a kuncin sa, ba abinda yake k'ara masa bak'in ciki sai irin yanda Queen Basma ta tofa masa miyau, murmushi yayi na k'arfin hali ya girgiza kai a fili ya furta "Rayuwa ce" sai ya wuce inda zashi.Sai gabda Magrib ya kaiwa Umma nik'an masaran, ya sameta ta rafka tagumi, sallaman da yayi shine ya dawo da ita daga duniyar tunani data fad'a, nisawa tayi ta amsa tace
"Aryan ya akayi ka dad'e ga ruwan sanwan ya tausa harya fara k'onewa" zama yayi a tabarma dake tsakar gidan yace
"Umma kiyi hakuri naje basu nik'a ba saida na jira suka nik'a shiyasa na dad'e" Umma tace
"Allah sarki, ba damuwa tunda mun samu nik'an yanzu zan gama insha Allah"
Nan ya zauna yana mata hira tana aikinta har aka kira sallan Magrib ya wuce masallaci.Ta b'angaren su Queen Basma kuwa gidan hutawanta suka wuce, musamma tasa aka gina mata shi dan hutuwa. K'aton gida ne babban flat wanda ya k'unci kayan alatu a ciki, ginin zamani aka yi shi a tsakiyar babban fili, filin gidan za a iya pakin mota goma, sai daga can gefe ruffa ne mai d'auke da kujeru da table a tsakiya, an tanaji wannan wurin dan hutuwa, wurin zagaye yake da shukokin furenni masu fidda k'amshi mai dad'i, sai kuma daga bayan gidan katon swimming pool ne wanda aka sanya masa ruwa mai kyau da tsafta, in ka kalli ruwan har kashe ido yake dan haske, lokaci-lokaci ake jenye ruwan ana sauya wani. Daga gaban swimming pool d'in akwai wata yar k'aramar k'ofa wanda sai sadaka da cikin garden(lanbu), ya k'unci bishiyoyi na kayan marmari (fruits) da kuma kujeru na hutu dan shawakatawa, wurin ya had'u matuk'a.

YOU ARE READING
'YAR SHUGABA
Romance*'Yar Shugaban k'asa ce* Queen Basma, ta hakimce a seat d'in baya ita kad'ai, sai Meena 'yar Governor Kaduna ce ita ke driving, sai Leema 'yar Sarkin Kano wacce take gefen Meena. K'aran wak'ar Music na Larabawa ke tashi a motan, dukkan su suna bin w...