*'YAR SHUGABA*👑
_page_ *7.*
_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾Basma da Deeja suna tafe a hankali a cikin mota, Basma ta kalli Deeja tace
"Deeja dan Allah ina son ki bani tarihinku a tak'aice in ba damuwa" murmushi Deeja tayi tace
"ba damuwa Anty Basma" nan ta fara bata labarinsu tas a takaice, har suka isa Asibiti zancen suke yi, Basma tana girgiza kai alaman tausayawa sosai.Bayan sun isa Asibiti, suka tadda Yaya Ahmad a office d'insa, ya duba Deeja ya k'ara bata wasu maganin kana ya sallamsu yace
"an gama ba zata k'ara dawowa ba" Basma ce tace
"ok Yaya godiya muke" murmushi yayi mata yace a cikin harshen yaran barebari,
"Basma, Khadija tana da kyau, ko kin lura da haka kuwa?" da murmushi a fuskanta ta mayar masa cikin yare,
"sosai ma kuwa, haka Yayanta yake kuma yama fita kyau, ita tafi kama da Ummansu" murmushi yayi yace cikin sigar wasa
"to kina ganin inna zab'eta tayi?" zaro ido tayi waje tace
"Yaya talakawa ne fa, amma kana ganin su Ammi zasu yarda?" dariya yayi sosai yace
"mai zai hana suk'i yarda, damu dasu duk d'aya muke a gurin Allah, face wanda yafi wani imani, kawai ke zaki wayar da ita sosai ta zama kamar yanda kika waye, sannan zan sata a makaranta tayi karatu, kinga ai shikenan ba mai hanani aurenta" murmushi tayi tace
"hakane Yaya Ahmad, ni ai wallahi ka sani farin ciki sosai, dama kuwa kasan abin da nake shiri kenan na maidata makaranta" dariya yayi yace
"to na rigaki buk'atar samun Ladan" itama dariya tayi tace
"yauwa Yaya Ahmad, ya za ayi ka samar ma Yayanta aiki a company Abbanmu, yana da diploma a computer science, kaga in an d'aukeshi sai ya koma karatunsa, yayi digree da masters, kuma yana aiki ana biyansa salary mai kyau" murmushi yayi yace
"shawara mai kyau, kinga mun taimaka su, tunda suna cikin buk'atan haka, kuma dama amfanin Arzikin kenan, in ka samu ka bama na k'asa da kai, zansa ma a k'ara yiwa unguwarsu titi, zamu d'auki matasan unguwan marasa k'arfi mu sanya su a makaranta, dan naga unguwar akwai mabuk'ata sosai" tace
"da kyau Yaya Ahmad, wannan shawaran yayi, Allah ya bamu ikon yi" yace "Ameen" duk wannan hiran cikin yaransu na barebari suke yi, Deeja tayi shuru tana saurarensu amma bata fahimtar me suke cewa, computer science d'in da Basma tace, shine ya bata damar fahimtar k'ila hiran da sukayi da ita ne, take gaya masa.Mik'ewa Basma tayi tace
"Yaya bari mu tafi" murmushi yayi yace a cikin harshen labaraci
"ki kulamin da Matata, karki sake ki gaya mata ba yanzu ba tukun, kuma ina so ki b'oye musu asalinmu, saboda su samu damar sake jiki damu" murmushi tayi tace itma cikin larabci,
"ai Yaya bazan fad'a ba, zance musu Mom d'nmu da Dad basa k'asarnan suna Canada, muke Nigeria da sauran family d'inmu, kuma gidan hutuna shine gidan iyayenmu, kaga bazasu gane ba" Cikin harshen turanci yace
"good girl" tana dariya suka fita, Deeja dai jinsu takeyi, tad'an so ta fahimci hiran amma bata gane ba saboda batajin labarci sai kalmomi kad'an take iya tsinta.Suna tafe a hanya suna hira a yanzu Deeja ta saki jiki sosai da Basma, koda suna kusan sa'a amma akwai girmamawa na musamman da Deeja kewa Basma, Basma tace
"Deeja samu shiga kasuwa siyayya" tace
"to Anty Allah ya kaimu lafiya".Sunje Babban shago na saida kayan kanti, side d'in maza suka fara shiga, riga da wando ta siya kala biyar k'ananun kaya, sai manyan kaya shadda da material na maza kala biyar d'inkakku, sai su singilet da gajeran wando guda biyar-biyar, sai takalmi kala hud'u, huda kala biyu, da kuma turare masu k'amshi har kala Hud'u, sai a gogo kala biyu. Aka sanya kowanne a jaka, ta bada kud'i aka sanya musu a mota.
Suka shiga side d'in mata nanma kaya ta sanya Deeja ta zaba kananu da kuma lesshi da atamfa, hatta gyale, takalma da d'an kunne duk ta siya mata, sannan ta siyawa Umma nata kayan kala uku da mayafi, takalmi da d'an kunne da sarka, harda turare, Siyayya suka yi sosai kana suka wuce gida.
Suna isa suka fara shiga da kaya, Umma ai bud'e baki tayi tana kallon kayan cike da mamaki, saida suka shigo dashi tas, Basma ta ware na Yaya Aryan tace
"Deeja ina d'akin Yaya Aryan yake?" Deeja tace
"shine can da yake kallonki" tace
"d'akin abude yake?"
"Eh a bud'e yake kullun" Umma kallonta take kawai ta kasa magana, Basma ta nufi d'akin ta bud'e, ba laifi d'akin ba wari yana k'amshin turaren wuta na tsinke, sai dai d'akin akwai datti da tarkacen kaya, aiko shiga tayi ta bud'e k'ofar, ta fara kauda kaya kana ta samu tsintsiya ta share d'akin, har wani gumi ta had'a abinda ba'a saba yiba, Deeja tazo zata tayata tace ta barshi itama zata iya, tana gama sharan ta kakkab'e zanin katifar ta gyara kana tazo ta kwashi kayan data siya masa ta aje gefe guda, ta fito tana sharce zufa, Umma ne tace

YOU ARE READING
'YAR SHUGABA
Romance*'Yar Shugaban k'asa ce* Queen Basma, ta hakimce a seat d'in baya ita kad'ai, sai Meena 'yar Governor Kaduna ce ita ke driving, sai Leema 'yar Sarkin Kano wacce take gefen Meena. K'aran wak'ar Music na Larabawa ke tashi a motan, dukkan su suna bin w...