*'YAR SHUGABA👑*
_page_ *31.*
_Na_
*_Rahma Kabir✍🏾_*Mai Martaba ya had'a duk kan iyalinsa ya gabatar musu da Amaryansa Umma, sai kuma ya gabatar da Matar Shureym Safeena, Hajiya Sa'a k'iri-k'iri ta nuna kishi sosai akan Umma, Mai Martaba ya ja mata kunne sosai da gargad'i, dole ta shiga taitayinta dan tasan halinsa sarai.
Shureym ya zauna a cikin gidansu na sarauta kusa da part d'in Yaya Adam, d'akin Safeena yana kallon d'akin Basma wanda ya dad'e a kulle bata tab'a zama a ciki ba, Shureym kullun yana sanyawa a gyara d'akin Basma tamkar tana zama a ciki tsaf yake.
*Bayan sati biyu*
Komai yana tafiya yanda ya kamata, Umma ta soma sabawa da zaman gidan sarauta, suna shiri sosai da Hajiya Murja, Mami ganin ba Sarki sai Allah dole ta sauko suka had'a kai suna zaman lafiya. Mai martaba yaji dad'i yanda suka had'a kai, mulki kuma yana tafiya yanda ya kamata.
*Da dare*
Mai Martaba ya kira Yaya Shureym domin suyi magana, Mai Martaba yace
"na kira ka ne akan maganar Basma, wai shin kun dai-daita kuwa? dan yanzu ana niman wata guda kenan dana ce na baku sati d'aya"Sunkuyar da kai yayi k'asa ya soma sosa k'eya, yace cikin inda-inda
"am am Baffa muna kan dai-dai tawa dan ina waya da ita" cikin nuna ko in kula Baffa yace
"Kira ta yanzu a wayanka inji, ka kuma sanya min a hands free"Gaban Shureym ya buga damm, cikin tsoro yace
"Baffa a k'ara bani lokaci yanda zamu samu damar fahimtar juna" wani kallo Baffa yayi masa sai da cikinsa ya kad'a, cikin d'aure fuska yace
"Nace ka kira min ita" jikinsa ya d'auki rawa ya ciro wayar ya danna number ta, Kiran farko taki d'auka harya katse, acan kuwa Basma tana kallon kiransa tak'i d'auka, ya sake kira cike da Masifa ta d'aga ko sallama babu tace"Wai Yaya Shureym meye damuwanka da nine? dan Allah ka rabu dani ka fita rayuwata, baza ka tab'a samun yanda kake so ba dan kasan bana Sonka, Abu d'aya zai za na koma d'akin ka, shine in su Abba sun nuna suna son haka, dan bazan tab'a bijirewa buk'atansu ba" saita fara kuka, jikin Yaya Shureym yayi matuk'ar sanyi, bai iya furta mata komai ba ya kashe wayar.
Mai martaba yayi ajiyan zuciya yace
"Shureym ka b'ata rawanka da tsalle, da ka rik'eta tun farko da Amana da tuni ta manta da k'iyayyar bata son ka, dan haka yanzu ga wannan farar takardan da bairo, in har na isa da kai kuma ni d'in Uba ne a gareka to ka rubuta mata saki d'aya a ciki, idan da rabon zaku zauna kafin ta fita Idda in ta sauko sai ka maidata".A razane Shureym ya kalli Mahaifinshi cikin kid'ima yace
"Dan Allah Baffa karka min haka, wallahi ina son ta, zan shiga mawuyacin halin inna rasata, plss Baffa ka tausayamin" sai ya soma zubda hawaye.Baffa ya tausaya masa amma sai ya danne damuwansa yace cikin Natsuwa
"Shureym na riga na gama magana, yana da kyau itama Basma tayi rayuwar farin ciki, kamar yanda da farko kaje ka auri wanda kake so ba bada sani na ba, dan haka itama a bata dama ta auri wanda take So"Shureym yana kuka ya d'auki paper da bairo ya rubuta kamar haka
"Basma na sake ki saki d'aya, ba dan bana sonki ba sai dan ki auri cikar burinki, in dai hakan zaisa ki farin ciki, ina son ki Basma Son da babu adadi, da kuma shi zan mutu a raina".
Yana gama rubutawa ya mik'e ya fita daga falon yana kuka, Baffa yana kiran shi amma ina yayi gaba cike da tashin hankali.
Part d'insa ya wuce, ya shiga a birkice, Safeena na ganinsa haka, ta isa inda ya zauna ta shiga tambayansa, kuka yake wiwi yana dafe da Kansa, cikin kuka yace
"Baffa yasa na saki Basma saki d'aya" salati ta saki a fili, a zuciyarta kuma tad'an ji dad'i, wani b'angare kuma ba taji dad'in haka ba, lallashinsa ta shiga yi, da kyar ta samu yayi shuru.
KAMU SEDANG MEMBACA
'YAR SHUGABA
Romansa*'Yar Shugaban k'asa ce* Queen Basma, ta hakimce a seat d'in baya ita kad'ai, sai Meena 'yar Governor Kaduna ce ita ke driving, sai Leema 'yar Sarkin Kano wacce take gefen Meena. K'aran wak'ar Music na Larabawa ke tashi a motan, dukkan su suna bin w...