*'YAR SHUGABA*👑
_page_ *15.*
_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾*Da dare*
An shirya kayataccen Dinner a katon hol mai d'aukan mutane dubu, manyan mutane sun halarci wannan Dinner, harda wasu yan k'asashen waje sun halarta, Amare da Angwaye sunsha kyau, ko wanne zaune yake da Amaryansa, Safeena na zaune cikin mutane ranta ya gama b'aci, zuciyarta yana mata zafi dan tsananin kishi, tunani ta shiga yi, ita fa Auren sirri aka mata sam ba'ayi irin wannan shagalin ba, haushi ya k'ara cikata, amma tasan matakin da zata d'auka akan Shureym, dan taga yana ta rawan jiki akan Basma.
Kowa ka ganshi a wannan lokacin yana cikin farin ciki, amma banda Basma da take cikin damuwa na rashin ganin Aryan agun, dan batasan yayi tafiya ba, sai kuma Safeena da take jin haushi akan mijinta. Anyi taro lafiya an watse lafiya, cikin farin ciki da kwanciyar hankali.
*Washe gari*
An kai ko wace Amarya gidan Mijinta da misalin larfe hud'u na yamma, Deeja an kawota gidan president a side d'in mijinta, haka Meena ma an ajeta acikin gidan president, part d'insu na gefen nasu Yaya Ahmad, Leema kuma an wuce da ita Kaduna zuwa gidan Jamal da Dady ya siya masa, sai Yaya Adam an wuce da matarsa Munayah, an kaita part d'inta dake cikin gidan Sarki, Basma ita ce tayi saura a gida, itama part d'inta yana gidan Sarki kusa dana Yaya Adam, kasantuwar Yaya Shureym bai gama aikin da suka d'aukeshi ba na shekara biyu, yasa zasu wuce America, su cikasa sauran shekara d'ayan daya rage. Sauran baki kuma suna nan basu soma tafiya ba.Sai Washe gari ko wani Ango ya shiga d'akin matansa, suka fud'e faifan sabon rayuwa cike da So da K'auna.
Da safe su Basma suka wuce airport, da kyar aka raba Basma da jikin Ammi, tasha kuka kaman ranta zai fita, Shureym kuwa sai wani kamata yake yana lallashi, sun shiga jirgi Basma na d'agawa iyayenta hannu, ji take kamar in ta tafi bazata dawo ba, haka suka zauna wuri guda, sannan aka rufe k'ofar jirgi, ana rufewa Shureym ya tashi kusa da ita ya kowa gefen hagunsa, kusa da Safeena ya zauna, ta cika ta batse dan haushi, Basma ta bishi da kallo ganin ya zauna kusa da wata mace cike da mamaki, bata iya cewa komai ba, Safeena ce da taga Basma na kallonsu, sai tayi saurin sakin fusha ta juyo fuskanta tana kallon Shureym, sai ta had'a bakinsu guri guda, ai da sauri Basma ta kauda kai, zuciyarta na dukan uku-uku, bakinta na fad'an
"Inalillahi wa inna ilaihir raji'un" kwantar da bayanta tayi jikin kujera, ta runtse ido, tsananin radad'i zuciyarta yake mata, bawai kishin Yaya Shureym taji ba, tsabar bak'in ciki da irin tsanar hayayyansa take, a tunaninta k'aruwansa ce, Safeena tana ganin Basma ta kauda kai, sai ta janye jikinta ta fara magana k'asa-k'asa tace"Baby wlh ka b'ata min rai cikin kwanakin nan, naga sai wani rawar jiki kake akan wancen yar iskan Yarinya, to wlh ka sani bazan tab'a raba kwana da ita ba, alkwari ka d'aukan min cewa kai mijin mace d'aya ce, dan haka kai nawa ne ni kad'ai, tunda kace had'in zumunci ne shiyasa na yarda da auren, dan haka da kanta zata gaji da zaman gidanka, harta nima saki tayi gaba"
Gaban Shureym ne ya fad'i, hankalinsa ya tashi, amma sai ya dake ya wayince yace
"Love ke kad'ai ce a guna, me zanyi da Basma, had'in zumunci akai mana dan bana sonta"
Cike da murmushi tace
"yauwa Babyna, kamin alkwara ba raba kwana da ita" murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo yace"na miki alkawari, ai bana son b'acin ran ki, ko me kike so zan miki domin in saki farin ciki" Safeena farin ciki ya rufeta, take nan ta manta da b'acin rai data shiga.
Basma kuwa kuka ta shiga yi mara sauti, a haka har barci ya kwasheta.
*America*
Bayan sun kai, mota biyu ke jiransu, d'aya wanda zai d'auki kayan su, d'aya kuma wanda zasu shiga, Basma jikinta a mace ta bud'e k'ofan bayan mota zata shiga, sai Yaya Shureym ya daka mata tsawa yace
"Karki kuskura ki shiga nan, ki shiga gaba ki zauna da driver, ko baki ga ina tare da matata bace?" cikin tsoro Basma ta bar jikin mota cike da tsiwa tace
"Matarka ko Karuwa?" Ai bata rufe baki ba ya tawo da sauri ya wanketa da mari, a razane ta dafe kuncinta tace
"Ni ka mara akan wannan yar iskan, to Allah ya isa mugu fasik'i kawai" tana gama fad'an haka tabar wurin da gudu, ta shige gaban motan daya d'auki kayansu ta zauna, driver ya tukasu suka wuce. Cike da k'unar rai Yaya Shureym ya girgiza kai yayi kwafa, iya ka k'uluwa Safeena tayi, amma ta share suka shiga mota tana sake-saken irin matakin da zata d'auka akan Basma, Lallai dole saita fahimtar da ita cewa ita matar Shureym ce.

YOU ARE READING
'YAR SHUGABA
Romance*'Yar Shugaban k'asa ce* Queen Basma, ta hakimce a seat d'in baya ita kad'ai, sai Meena 'yar Governor Kaduna ce ita ke driving, sai Leema 'yar Sarkin Kano wacce take gefen Meena. K'aran wak'ar Music na Larabawa ke tashi a motan, dukkan su suna bin w...