04

1.4K 104 0
                                    

*'YAR SHUGABA*👑

_page_ *4.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

An shirya gagarumin gasa na rawa a k'asar England, Basma na d'aya daga cikin masu fafatawa. In ta dawo daga school babu abinda take yi sai gwajin rawa, su Leema suke k'ara mata k'arfin gwiwa.

Ranar taro, k'aton hol cike yake mak'il da mutane maza da mata, ko wanne yana mazauninsa, ga kuma masu tantance rawar daga gefe, zaune suke akan kujeru na alfarma, ga dogon table a gabansu an d'aura kayan motsa baki da kuma abin sha, masu fafata gasar su Hamsin ne, a ciki ake son a finda zakara guda d'aya wanda aka tanada mak'udan kud'i da key na mota sai kuma hular Queen na rawa ga wanda taci, sai na biyu dana uku kyautar kud'i. Gasar maza da mata ne, Ganin yawansu da Basma tayi sai zuciyarta ya tsinke ta karaya, gani take ba zata ci ba, jere suke akan layi wannan na bin wannan, sun sanya riga top mai dogon hannu sai kuma wando dogo pencil ya matse jikinsu, rigan ta kama su daga sama zuwa ciki, k'asan kuma ya bud'e, tsayinta ya kawo rabin cinya. Wasu sun sanya hula a kai wasu kuma sun baje gashin su a baya, shigar Basma tayi mata kyau, ta dunk'ule gashinta ta sanya hula, ba wani makeup a fuskanta amma tayi kyau sosai. Basma itace ta goma sha shida a cikin jerin layin.

D'aya bayan d'aya suke fitowa suna gwada rawan su, alkalai suna dubawa tare da rubuta makin, 'yan kallo kuma suna ihu in rawar tayi musu kyau ga masu gwajin.

A haka layi yazo kan Basma, cikin salo da kwarewa ta fara rawa mai ban sha'awa, a hankali take komai cikin nutsuwa, lauye duk sassan jikinta take yi tamkar roba, ta d'auki tsayin minti ashirin tana rawa, nan fa hol ya kaure da ihu da alama rawarta ya birge su. Alkalai suka dakatar da ita suka ce ta tafi, na gaba yazo ya nuna nashi.

Da haka har aka gama tantance rawar su Hamsin. Daga cikin alkalai wani ya mik'e yace cikin harshen turanci, zasu cire mutane goma daga cikin su, domin fafatawa na k'arshe, washe gari zasu yi rawa a cikinsu za'a tantance Mutum na farko dana biyu har zuwa na uku da sauran numbers. Nan fa hol yayi tsit ana son aji su waye zasu shiga gasa ta k'arshe.

An fara kiran Mutum na farko da haka har aka je kan Mutum na tara, Basma bata ji sunanta ba sai ta sadak'ar da ta rasa gasar, wanda basuji sunan su ba sai kuka wasu kuma damuwa ya bayyana a fuskokinsu, Basma bata an k'araba taji an kira sunanta Basima MB a ta goma, da yake da haka tayi regista da sunan ta basima MB, saboda basaja, kuma ita ba 'yar k'asan ba ce. Ai hol saiya kaure da ihun su Leema da Meena sauran Mutane ma suka tayasu ihun. Da haka aka tashi taro Maza hud'u mata shida sune zasu fafata a washe gari.

*Washe gari*
Hol ya cika mak'il da Mutane fiye dana jiya ma, nan kowa ya samu guri ya zauna, yau shigan dasu Basma sukayi kusan irin na jiya ne sai dai an sauya launin kalan kayan da suka sanya jiya. Alk'alai suka baza ido, na farko ya fito ya fara fafatawa, har aka kai na biyar, daga nan sai aka tafi hutun tak'aitaccen lokaci.

Bayan an dawo aka d'aura har zuwa na k"arshe ta fito wato Basma, nan ta soma kafa tarihi domin rawar ta na yau yasha ban-ban dana jiya, Basma ta dage iya iyawanta, sai baza rawa take tamkar ba ita ba, inba ka mata kallon caf ba bazaka shaida Basma ce ba, domin tayi shiga na b'adda kama. Saida tayi rawa sosai sannan aka dakatar da ita, alk'alai sun fita a hol sunje had'a marking, sai da suka b'ata kimanin rabin awa kana suka dawo kan high table suka zauna, sun fara fad'an sakamako daga na goma ne, har suka zo kan na shida ya rage saura mutum Hud'u, Basma na ciki, a haka har suka fad'i na Hud'u dana uku, saura Basma dawata 'yar k'asar England d'in, sai aka tafi hutun rabin sa'a, nan fa kawayen su Basma suka rufe ta da Murna Addu'a suke Allah yasa itace mai nasara. Burin Basma ko na biyu tazo zatayi farin ciki tunda ta kafa Tarihi a fagen rawa.

Koda aka dawo daga hutun takaitaccen lokaci, hol d'in yayi shuru ana jiran aji wacce tayi winning, mai fad'an sakamako saida yayi shurun minti biyar kafin ya furta first position Basima MB kece ki kai nasara, d'ayan kuma ta zama na biyu, hol d'in ya kaure da kuwwa, nan take aka d'aurawa Basma Hular Queen, wannan dalilin ne yasa Basma take amsa sunan Queen Basma. Sunyi hotuna kala-kala hatta gidan TV na k'asar sun nuna gasar a TV.

'YAR SHUGABAWhere stories live. Discover now