23

1.1K 76 0
                                    

*'YAR SHUGABA*👑

_page_ *23.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

Jirgin su Basma ya sauka lafiya, drop ta d'auka taxi, ya kaita asibitin da Yaya Ahamd yake aiki, nan ta bufa, ta ciro trolley d'inta guda biyu da kuma wannan bak'ar jakar da diary ke ciki, ta jasu zuwa cikin asibitin, gefe ta tsaya ta samu d'aya daga cikin masu gadi yana ganinta ya washe baki dan ya ganeta suka gaisa tace
"aam Baba Dr Ahmad yana ciki kuwa? cikin ladabi yace
"yana ciki, motansa yana cikin wancen barandan yayi parking d'inta"

Murmushin jin dad'i tayi sai ta ciro wata farar takarda mai d'auke da wasik'a a ciki tace
"Baba Dan Allah ka taimaka ka kai masa wannan kayan, sauri nake jirgi na jirana, ka gane ni ai?" cikin dariya yace
"kwarai Hajiya na gane ki" murmushi tayi ta k'irga dubu Ashirin ta bashi tace
"Baba ga wannan saika ci goro ko" jiki na rawa ya amsa yayita shi mata da albarka, kiran wani matashin saurayi yayi d'aya ne daga cikin drivern asibiti, yayi masa umarni daya d'auki d'aya daga cikin trolley, shi kuma Baba yayi mata sallama ya sanya wasik'ar a aljiunsa, kana ya d'auki d'ayan trolley da kuma bak'ar jakar suka shiga cikin asibiti.

Basma binsu tayi a baya har saida taga sun isa k'ofar office d'in Yaya Ahmad, kana tadan tsaya, tana ganin sun Shiga sai ta juya cikin sauri ta isa bakin gate, taxi ta koma ta shiga, da gudu suka bar unguwar.

Mai gadi suna Shiga, Yaya Ahmad ya kalle su cike da mamaki yace
"Malam wannan kayan fa daga ina?" da dariya a fuskansa yace
"Uwar d'akinta tace na kawo maka" cikin mamaki yace
"wace uwar d'akin naka?" yace
"Basma mana, ita tace na kawo maka domin tace tana sauri ne ana jiranta, tace in baka wannan wasikar ma" saiya mik'a masa, cike da tsoro da mamaki Yaya Ahmad ya mik'e yace
"Basma kuma?" da sauri ya fita a office d'in, Baba mai gadi da d'ayan saurayin suka rufa masa baya, gate ya nufa yana hangen ko zai ga Motan da tazo a ciki, babu kowa bamu alaman wata mota, Baba mai gadi yace
"kaga ikwan Allah sun riga sun tafi, acan fa na hangi mota taxi wanda ya kawo ta, nima nayi mamaki dana ganta a cikin taxi" ajiyar zuciya Yaya Ahmad yayi ya shiga wasi-wasi da damuwa, komawa office yayi ya Shiga bud'e jakukunan, tabbas kayan Basma ne a ciki, bak'ar jakar ne ya nima bud'ewa amma arufe take babu key a jiki, zama yayi kamar wanda yayi aikin gajiya, dan jikinsa duk a mace yake, da kuma tsananin fargaba da zuciyansa yake ciki, bud'e wasik'ar ya yi, ya soma karantawa kamar haka...

*ASSALAMU ALAIKUM*

*Yaya Ahmad da fatan duk kuna lafiya, nasan zaka yi mamaki da ganin kayana ba tare da na bari mun had'u ba, Yaya Ahmad ina cikin damuwa na tsani rayuwar dana ke ciki, dan haka zanyi nesa da kowa ko zanji saukin abinda ke damuna, Yaya Ahmad kafi kowa sanin bana son auren da a kayi min, amma na hak'ura nayi biyayya gasu Abba, na d'auki alk'awarin yiwa Yaya Shureym biyayya in zauna dashi, amma kash sai dai shi a gunsa akwai mugun nufi a zuciyansa game dani, a ranar da muka shiga jirgi zuwa garin America lokacin aurenmu, anan cikin jirgi Yaya Shureym ya fara shayar dani ruwan bak'in ciki, wanda har yau ina cikin shansa, Yaya Ahmad na so gaya maka komai a wancen lokacin, saina ce bari nayi hak'uri bai kamata in fara kai k'ara ba, kuma ma duk abinda zan fad'a ba mai yarda dani akai, sai kai kawai nasan zaka yarda tunda kai kasan halinsa, d'aurewa nayi tun daga ranar dana tafi na bar gida har zuwa yanzu, Yaya Ahmad bari na tak'aice maka bayani, duk kan k'arin bayani da kuma labarin zamana a America yana cikin wannan diaryna na rubuta shi, da kuma wasu hotuna a ciki wanda zasu zame min shaida, duk a cikin wannan bak'ar jakan, akwai kuma wayata a ciki wanda akwai wasu hotuna a ciki, ga system d'ina ka aje min shi, key d'in dana baka rannan ka aje min shine mabud'in wannan jakar, ina so ka kai gida ka bayyana wa su Abba komai dake cikin jakar nan, tare da karanta musu wannan wasik'ar da kuma abinda ke cikin diary na, Yayana nagode da kulawanka, nasan kaida Momy ne zaku fi kowa shiga damuwa, dan Allah ka bama Momyna hak'uri, kuma nayi muku alk'awari duk inda nake zan kula da kaina zan kare mana martaban gidanmu da mutunci na, insha Allah zan kiyaye duk kan hakk'ok'in Allah wanda ya rayata akaina, kuma zan kare igiyar Aure na.*

'YAR SHUGABAWhere stories live. Discover now