12

1K 69 0
                                    

*'YAR SHUGABA*👑

_page_ *12.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

*Da Dare*
Bayan sallan Isha'i, Yaya Ahmad ya nufi d'akin Momy ya tambaya ko su Basma sun dawo, Momy ta shaida masa masu dawo ba, da mamakin hakan yabar part d'in Momy, ya kira Yaya Naufal a waya yace masa ya fito ya raka shi wani guri, cikin sauri ya fito suka kama hanya.

Ta b'angaren Basma kuwa sun gama shiri tsaf sunyi hotunan da suka saba, sai suka fito haraban gidan suka shiga mota, mai gadi ya bud'e musu gate, d'aya bayan d'aya suka fice, wanda yayi dai-dai da shigowan Yaya Ahmad layin, ganin motocin su ne, sai Yaya Naufal yace
"to ai gasu nan sun fito ina ga gida zasu" Yaya Ahmad yace
"ai kuwa, amma bari mubi bayansu mu tabbatar da gidan zasu" da sauri ya juya akalan motansa yabi bayansu, tafiya suke da gudu kamar zasu bar gari, sun zo dai-dai kan kwanar da zai sadasu da gida, sai Yaya Ahmad yaga sun mik'e, da mamaki ya juya ya kalli Naufal yace
"ka gani ko, ba gida zasu ba, duk yanda akayi akwai inda suke zuwa yaran nan, Amma dai bari muje" sun cigaba da bin bayansu har su Meena suka isa hotel d'in.

Sun shiga ciki sunyi parking motocin, Yaya Ahmad yayi parking motonshi a waje, da sauri ya fito Naufal na biye dashi a baya, da shigansu sai suka hango su Basma cikin wani shegen shigan tamkar zasu gasar kyawawa, tafiya suke tamkar ba zasu taka ba, har suka shiga cikin club d'in, mamaki da tsoro ne ya lullub'e su Yaya Ahmad, binsu su kai a baya, escot na ganin su Naufal duk suka fara b'arin jiki, d'aya daga ciki bakinsa ya d'auki rawa yace,
"sir sannu da zuwa" Yaya Ahmad ya masa wani mugun kallo ya wuce su, har cikin hol d'in suka bi su Basma, suna hangen inda suke zauna, Yaya Ahmad yace
"Naufal ga key je gida da sauri ka d'auko Momy da Ammi, kace kawai suzo, dan bai kamata ace mu kad'ai muka gansu ba" cikin sauri Yaya Naufal ya amsa ya wuce, Yaya Ahmad ya samu wani kujera ya zauna daga baya duk yana hango su, bayan kamar minti ashirin saiga Jalal yazo ya kama hannun Leema suka bi ta wata k'araman k'ofa ta gefe suka fita, da sauri Yaya Ahmad ya bi bayansu, a hankali yake binsu tambayar b'arawo, har suka isa d'akin hotel d'in da Jalal ya kama, suna shiga ya dawo, jikinsa ne ya d'auki rawa saboda tsabar b'acin rai, yana dawowa hol d'in ya hangi Meena cikin wani group maza da mata suna d'aga kwalaben syrup, bai tsinke da lamarin ba saida ya hango Basma kan step tana kwasan rawa iya k'arfinta, da karairaya jiki, ai tuni wasu zafafan hawaye suka cika masa ido bai taba tsammanin haka ba, lamarin ya girgiza shi, wayansa ne ya soma ringing da sauri ya fita hol d'in, ya duba ashe Yaya Naufal ne sai ya d'aga, ya sanar masa sun zo, da sauri ya isa wurin motocin harda escot d'in su Momy, Ahmad ya kasa magana hannun Momy ya kama suka wuce cikin hotel d'in, haka su Ammi suketa binshi har suka isa d'akin da Leema ke ciki, kwankwa k'ofan yayi, daga ciki Jalal ya bud'e daga shi sai best da gajeran wando, Yaya Ahmad ya runtse ido ya bud'e, Jalal ya na musu kallon mamaki yace
"lafiya wa kuke nima?" daga ciki ne Leema ke cewa cikin d'aga murya
"baby waye ne? kazo mana wlh ina cike da buk'atarka fa" ai da k'arfin Yaya Ahmad ya bangaje Jalal ya kusa kai ciki, su Ammi ma suka rufa masa baya, a razane Leema ta mik'e tana ja da baya harta kai jikin bango, Allah yasa bata cire kayan jikinta ba, idonta ne kamar zasu yo waje saboda tsananin furgici, su Momy da Ammi sai suka hau salati, abin ya girgiza su, Yaya Naufal saboda fushi baisan sanda ya zaro bel d'insa ba ya shiga jibgar Leema, ai Jalal na ganin haka ya fice a sittin, Leema ta kasa ihu domin tashin hankalin da take ciki ya wuce na jin azabar dukan da Yaya Naufal ke mata, da kyar Ammi ta kwaceta tace su fita, haka suka fito cikin tashin hankali.

Momy tace
"ina su Basma suke" Yaya Ahmad yace
"muje in kaiku" ya musu jagora har cikin hol d'in, saboda dan dazon mutane da kyar suka samu hanyar shiga, Yaya Ahmad ne yace
"Momy ga Basma can" yayi mata nuni da inda take kwasan rawa, Ammi ne tace
"innalillahi wa inna ilai hir rajiun, mun shiga uku ni Faitima" idon Momy ne ya kawo kwalla, sai tayi saurin shanyewa tace
"ita kuma Meena tana ina?" cikin mutane Yaya Ahmad ya kusa dasu, ya kaisu hargun da take, suka tsaya ta bayanta, Momy ta dafata, Meena ta juya da niyyar kwararo ashar domin ta riga tayi tatil, ganin Momy a bayanta ne yasa ta mik'e zunbur tace cikin maye
"Ke ya kike min kama da Momy ce" wani wawan mari Yaya Naufal ya sakar mata saida taga taurari, a gigice ta kalle shi, ai tuni hanjin cikinta suka hautsine sai taji cikin ta ya murda, nan da nan jikinta ya d'auki b'ari, ta kasa magana sai rufe baki tayi, idonta tamkar zasu fad'o k'asa saboda tsoro, Momy ce ta kama hannunta suka fita waje, a cikin mota suka sanya ta kusa da Leema, sannan suka k'ara komawa cikin hol d'in.

'YAR SHUGABAWhere stories live. Discover now