*'YAR SHUGABA👑*
_page_ *39.*
_Na_
*_Rahma Kabir✍🏾_**Cikin Basma Wata Tara Da Sati Biyu*
Basma ce a cikin kitchen tana zuba Peppe Meat a plet, fitowa tayi tana jan k'afa da alama cikinta yayi mata nauyi sosai, zama tayi akan kushim ta fara ci tare da cuna baki alamar yaji ya dame ta, haka tayi ta ci tana gumi tare da shan Gwaba juice, haka ta cinye tas tare da lashe hannu, da alama bai isheta ba sai ta kwalawa d'aya daga cikin masu aikinta kira
"Uwale, Uwale" da sassarfa ta fito ta risina tace
"Hajiya gani"
"Yauwa k'aromin peppe Meat d'in nan, ki zuba min da yawa sannan ki d'auko min goran ruwa da cup ki kawo min"Jiki na rawa Uwale ta wuce kitchen ta kawo mata gaba d'aya duk abinda take so, zama ta gyara ta cigaba da cin kayanta tanaci tana shan ruwa saboda bala'in yaji data zuba a ciki.
Sallaman su Meena da Deeja ne ya katse ta, ta amsa musu, zama duk suka yi suna yi mata tsiya
"kullun in muka shigo sai mun ganki da wani abun kina ci, acici mala'kan tauna" Meena ce take fad'an haka.Dariya kawai tayi musu ta cigaba da cin abin ta, hira suke sosai suna tattaunawa akan taron daya gudana a garin Katsina wanda Basma bata samu zuwa ba, hak'ik'a taron ya k'ayatar kuma sun tattauna akan Matsalolin masu yima Yara k'anana fyad'e, Basma tace
Wallahi nayi missing taron kuma ba haka naso ba"Deeja ta lura da yanda Basma take yatsine fuska cikin kulawa tace
"K'alli yadai naga tun d'azu kina ta yamutse fuska kodai abin yazo ne?"Murmushi kawai tayi tace
"inda yazo kya ganni ina d'irkan abinci"
Dariya suka yi mata, Meena ta mik'e tace"Kinga bari naje na shirya Yaya Naufal ya kusa shigowa kunsan da an sakko Sallan Juma'a suke dawowa"
Deeja ma mik'ewa tayi tace
"Hakane 'Yar Uwa, nima bari naje na shirya kinsan yau akwai yini a gidan Abba bayan Sallan La'asar" Nan suka yiwa Basma Sallama, sai tace"Uhum masu Maza to sai ku tafi kan k'uda ya riga ku" Dariya suka kwashe dashi suka fita.
Basma ji tayi cikin ta yayi mata hak'e-hak'e da kar take numfashi, gyara zama tayi ta jingina jikin kushim, a fili tace
"Ya Rabb ka rabani lafiya da abinda ke cikin nan, kayi masa albarka da kyakkyawan Albarkanka, Ameen, yau dai cikin nan ya d'aure min sosai to Allah gani gareka"Bata rufe baki ba cikin ya fara tsingulinta, da sauri ta mik'e tana jan k'afa ta shiga d'aki ta d'auko key na Motanta, fitowa tayi ta bama masu aikinta order akan abinda take so suyi mata, sai ta fita tana nishi, gaba d'aya ciwon mara ya soma damunta, driver ta kira yazo ta mik'a masa key Motarta tace
"Kaini Asibiti" ba musu ya amsa cikin girmamawa.Kafin sukai Asibiti ciwo ya tsananta salati kawai take yi, da sauri Driver ya kira Nurses suka zo suka shiga da Basma cikin Asibiti d'akin Haihuwa suka wuce da ita, Nurse Sa'a ta dubata tana 8cm, da alama ta jima tana nakud'ar a tsaitsaye inji Nurse d'in, Basma nak'uda ta taso sosai Aryan take kira tare da Abbanta, hawaye ya na zuba, Addu'a take da niman sassauci a wurin Allah.
Yaya Aryan yana gun Aiki ji yayi Kansa ya sara masa, gabansa ne ya fad'i, a lifi ya furta Basma, da sauri ya mik'e yabar abinda ya keyi ya soma had'a kayansa, jaka ya d'auka ya sanya hularsa ya fito, Massinger ne yace
"Yallab'ai akwai masu jiranka suna wurin Alhaji Naufal"
Yana tafiya yace
"kace su dawo ranar Monday wani uziri ya taso min".Mota ya shige ya kamo hanyar gida, wayar Basma yaketa kira amma bata d'auka ba, Basma a gida ta bar wayan, hankinsa ne ya kuma tashi, wayar Deeja ya kira ya tambayeta Basma tace
"Ban jima da fitowa daga part d'inku ba ina ganin tayi barci ne" Cikin damuwa yace "ok" ya kashe wayar.
Basma ta cika 10cm haihuwa ta taso amai ta fara yi, haihuwarta mai fayar baki ne, amai take sosai tana yunk'uri, bayan ta gama aman sai nak'udar ta lafa a hankali barci ya fara fizgarta, hutun minti biyar tayi nak'udar ya dawo, cikin ikwan Allah bata k'ara minti goma ba ta haifo d'anta Namiji mai kama da Aryan sak. Yaron kato sai ihu yake Hamdala Basma ta shiga jerowa da yiwa Allah Tasbihi.

YOU ARE READING
'YAR SHUGABA
Romance*'Yar Shugaban k'asa ce* Queen Basma, ta hakimce a seat d'in baya ita kad'ai, sai Meena 'yar Governor Kaduna ce ita ke driving, sai Leema 'yar Sarkin Kano wacce take gefen Meena. K'aran wak'ar Music na Larabawa ke tashi a motan, dukkan su suna bin w...