05

1.3K 88 0
                                    

*'YAR SHUGABA*👑

_page_ *5.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

*washe gari*

Basma ta tafi aiken Momy da misalin ƙarfe sha biyu na rana, gidan hajiya Aisha ta tafi ta kaimata saƙon Momy. A hanyarta na dawowa ne saita wuce gidan hutu ta ɗauko wasu kayanta kana ta kama hanyar gida, escot na biye da ita a baya, ta hau kan babban hanya bata ankara ba ta bige wata Yarinya, cike da tashin hankali ta koma bakin hanya tayi parking, bodyguard suka fito a motansu suka nufa wacce ta bige, saboda tsoro Basma ta kasa fitowa, sun ganta kwance cikin jini a sume, cikin sauri ɗaya daga cikin ascot ɗin ya isa gun basma yace
"Hajiya Yarinya ta suma fa" cikin sarƙewan murya tace
"ku sata a motanku a seat na baya, sai kuzo ku biyu ku shiga tawa motan tunda ku huɗu ne" cikin sauri ya amsa
"yes Madam" ya tafi tare da cika umarnin data basu.

General hospital direct suka wuce, aka wuce da ita emergency room, cikin sauri Basma ta ɗauki wayarta ta kira Yaya Ahmad ta shaida masa suna cikin asibity ta bige wata yazo da sauri, baifi minti biyar da kiranshi ba saiga shi yazo yace
"ina take?" cikin damuwa tace
"tana emergency room" bata kaiga ƙarasawa ba ya wuce ciki.

Zarya ta shiga yi hankali ta a tashe ganin ma ashe ba ƙaramar Yarinya ta bige ba budurwa ce, an ɗauki kusan minti talatin kafin duka likitocin suka fito, da sauri Basma ta tari Yaya Ahmad tace
"Yaya ta farfaɗo kuwa?" ciki da tausayawa ƙanwar tashi ganin yanda ta burkice yace
"ta farfaɗo yanzu dai ta samu barci kuma anyi mata dressing inda taji ciwo, nan da awa guda zata farka insha Allah". Da ƙarfi Basma tayi ajiyan zuciya tace "Alhamdulillah" sai Yaya ya jefo mata tambaya yace
"in kika je ne har kika bigeta?" gefe ta koma ta samu wuri ta zauna, shima binta yayi ya zauna, nan ta bashi labarin yanda ya faru. Ya girgaza kai yace
"Allah ya kyauta gaba, amma meyasa kikayi driving da kanki" murmushi tayi tace
"Yaya Ahmad wlh kawai hakanan naji ina sha'awar tuka kaina" Dariya yayi yace
"hmm su Basma rikici, kije gida kawai saiki turo Shugaban mai kula da sashin Ammi Baba kulu tazo ta zauna da ita, tunda ke yau nasan kinada baƙo ya kusa sauka ma", murmushi tayi tace
"tom Yaya Ahmad bari naje anjima zan dawo insha Allah"
"ok sai kin dawo, ki kula da kankifa"
"insha Allah Yaya zan kula" suka rabu cikin farin ciki.

Tana isa gida taje ta samu Baba Kulu ta sanar da ita saƙon Yaya Ahmad, driver zai kaita, cikin sauri Baba kulu ta tafi.

Basma tasa masu aikin Kicin na ɓangaran Ammi ta sanar musu abincin da za suyi mata na tarban baƙonta. Sai ta nufi sashin Momy ta samesu zaune da Ammi suna magana ta gaishesu kana tace
"Momy na kai mata saƙon tace za kuyi waya" Momy tace
"ok, amma naga kin daɗe ko kin biya gidan hutun naki da kika saba?" murmushi tayi tace
"a'a Momy wallahi a kan hanyar dawowa na gida, na bige wata, yanzu haka tana asibity, na tura Baba Kulu ta zauna da ita zuwa anjima zan koma" cikin tashin hankali Ammi da Momy suka hada baki
"subhanallah da fatan dai abin da sauki" murmushi tayi tace
"da sauki kamar yanda Yaya Ahmad ya sanar dani shiyasa na taho ma" Ammi tace
"to Allah ya bata lafiya ya kuma tsare na gaba" duk suka amsa da "Amin". Saita shiga ɗakinta dake sashin Momy.

Tana Shiga ta  faɗa makeken gadonta wayarta ta jawo ta duba taga miss call ɗin su Meena, kiranta tayi bugu buyu ta ɗauka, Meena bata jira Basma ta yi magana tace
"wlh Basma ba kida kirki, jiya ko ki kiramu kiji ya muka sauka" cikin natsuwa tace
"Afwan ya habibty, nima Momy saida tamin faɗa, haushin haka yasa ban kiraku ba" Nan dai suka shirya, Basma ta bata labarin accident ɗin da tayi, Meena ta mata Allah ya kyauta na gaba kana suka kashe wayar.

Basma ta kuma kiran Leema itama mita tayi mata ƙorafi kamar yanda Meena tayi nan ta bata haƙuri suka yi hira kana suka yi sallama.

Bayan sallan asri Basma tayi wani wanka ta sanya baƙar jallabiya mai ɗauke da kwalliya pink color, tayi rolin da gyalen abayan, saita fito, abinci ta ɗauka a baske kamar yanda Momy tasa aka dafawa mara lafiyan, saita shiga mota driver ya jata zuwa asibity.

'YAR SHUGABAWhere stories live. Discover now