09

1.2K 76 0
                                    

*'YAR SHUGABA*👑

_page_ *9.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

*Washe gari*

Da misalin k'arfe hud'u na yamma, ya Aryan yayi wanka, sai ya d'auki d'aya daga cikin kanyan da Basma ta siya masa ya sanya, yayi kyau sosai da yake k'ananun kaya ne, sai ya d'auki hulan sanyi ya sanya a kansa saboda gashin kansa. Ya fito yace wa Umma sai ya dawo, Deeja tace
"Yaya Aryan kayan nan ya maka kyau, amma meyasa ka sanya hulan nan, ai daka cire zaka fi kyau" murmushi yayi yace
"Deeja banyi aski bane, kinga sumana ya taru shiyasa na sanya" murmushi tayi tace
"hakane, to sai ka dawo" kana yasa kai ya fita.

Tafiya yake bai san ina zashi ba, ya mik'e hanya sanb'al saida ya kai k'arshen layin su kana ya karya kwana, tafe yanke yana tunanin Basma da irin hiran da suka yi jiya, bai ankara ba wata mota ta taho a guje, gadan-dagan tawo kansa, ai ba shiri yayi tsalle ya koma jikin bangon wani gini saura kiris ya fad'a kwata, ya razana sosai, Basma dake cikin motan me zata yi inba dariya ba, da yake motan mai bak'in glass ne, Aryan ya kafa wa motan ido yana jiran wanda yake ciki ya fito, saida ta gama cin dariya sosai, kana ta bud'e ta fito, ido Hud'u suka yi sai ta kwashe da dariya, iya kuluwa yayi sai ya tamke fuska, cikin fushi yace
"dama kece kika son bigeni da gan-gan ko? anya Basma ba kida Matsala a kwakwalwa ba kuwa" yana fad'an haka saita tsaida dariyanta tace cikin tsiwa
"haba Yaya Aryan ya zaka kamanta ni da hauka, nifa da wasa nayi maka, tun daga nesa na hango ka nace bari na dan tsokane ka, ashe Yaya Aryan haka kake da tsoro" saita k'ara kwashewa da dariya, a yanzu shima dariyan yayi domin Basma ta kai mak'ura wurin shak'iyanci, tace
"Yaya Aryan dama fa wurinka zani, ka rakani wani wuri" kallonta yayi tare da tsare gira yace
"ni sa'anki ne, kije ki samu Deeja tana gida ita saita raka ki, amma ba dai ni ba" ai nan da nan Basma tayi fuskan tausayi tace
"Yaya Aryan ni kai nake so ka rakani" yayi murmushi yace
"to bazani ba" b'ata rai tayi kamar zatayi kuka tace
"haba Yaya Aryan kayi hak'uri muje ba zamu dad'e ba" ganin zata fara masa kuka yace
"to muje".

Nan suka shiga mota suka fara tafiya, ta sanya wak'ar larabawa yana yi a hankali, ta juyo tace
"Yaya Aryan kayi kyau amma abu d'aya ya b'ata wankanka" murmushi yayi bai tanka mata ba, ai bai aune ba sai yaje ta janye hulan kansa ta b'oye a dayan gefenta, da sauri ya juyo yace
"wai ina wasa dake ne?" tuni Basma ta shagaltu da kallon sumansa saura kad'an ta buga motan dake gabansu, da sauri ta gyara tuk'in ta mai da hankali kan hanya, Yaya Aryan ya kwashe da dariya yace
"Yarinya taga suma ba irin nata ba ta rikice" dariya kawai tayi bata ce komai ba har suka isa wurin shak'atawa.

Parking suka yi duk suka fito, suka jera ba tare da sunce ma juna komai ba, shi dai binta kawai yakeyi, sun isa wani wurin da aka zagayeshi da furanni masu k'amshi, wuri sanyi ga iska mai dad'i, kujerune a ciki da table a tsakiya duk suka zaune, weta ne ya zo da sauri ya tambayesu abinda za a kawo musu, Basma tace
"ice cream da shawarma da kuma drink" ta kalli Yaya Aryan tace
"Yaya me za'a kawo maka" yace
"duk abinda zaki ci shi zanci" murmushi tayi ta gaya ma weta ya tafi kawo musu.

Suna fuskantan juna Yaya Aryan yace
"dama nan wurin zaki kawoni" dariya tayi tace
"eh, saboda in dan saka ka waye, dan naga kamar baka waye ba" hararanta yayi yace
"kece dai baki waye ba da kike sanya k'ananun kaya ki fito ko ajikinki wai irin kin had'u" da sauri ta kalli jikinta tace
"Yaya kana nufin banyi kyau ba ne?"
"eh baki kyau ba saboda shigan bata dace dake ba" tace
"Yaya Aryan, na sanya ne saboda naga a mota nake" riga da wando ta sanya sun kamata sai dai rigan ya sakko har gwiwanta amma duk shape d'in jikinta ya fito sai ta yi rolling da gale a kanta ta rufe gashinta" yace
"eh, ai ba shiga bane na musulunci mace tayi ta fita" jikinta ne yayi sanyi tace
"To insha Allah bazan sake yin shigan na fito ba, amma zan rik'a sanyawa a gida" murmushi yayi yace
"da dai yafi miki" tace
"Yaya Aryan sumanka tayi maka kyau, meyasa kake rufewa?" ya kalleta suka had'a ido sai da suka kalli juna na tsayin minti uku, kana ya sauke ajiyan zuciya yace
"Basmaaa" sai duk jikinta ya mutu ta sunkuyar da kai k'asa, sai taji ta cigaba da magana,
"bana son barin suman, kuma yawan askewa yana k'ara yawansa, shiyasa nake yawo da hula, saboda in mutane suka gani suna yawan min magana akai" murmushi tayi tace
"Yaya Aryan dan Allah karka aske, zan siyo maka mayuka na maza, da zaka rik'a gyarawa, wlh har sheki zai rik'ayi, ba kaga yanda mazan India suke yi bane" murmushi yayi yace
"ni Basma bana son sumar dan a takure nake" marairaice fuska tayi tace
"to ko zaka aske, karka aske duka ni ina son ganinka dashi" hararenta yayi, kan yayi magana an kawo musu shawarman.

'YAR SHUGABAWhere stories live. Discover now