*'YAR SHUGABA*👑
_page_ *20.*
_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾Safeena cike da damuwa tace
"amma Shureym anya baka jawo tonuwar asirinmu ba, domin in dai Basma taji cewa ka kai karanta ne, tofa zata gaya duk abinda ya faruwa, da kuma dukanta da kake yi"Runtse idonsa yayi ya bud'e, cike da damuwa yace
"wlh Safeena raina ne ya b'aci, idona ya rufe sam ban kawo haka ba, sai yanzu da kika tunatar da ni, yanzu ya kike ganin za'ayi" cikin damuwa ta rafka tagumi tace
"ina ganin karka gaya mata, kace kawai ana nimanku ne, inya so inta je can taji komai, kuma na fison dama kowa yasan dani a family d'inku dan nagaji da b'oye-b'oye" cike da damuwa Shureym yace
"haba safeena bai kamata ace abinnan ya fasu yanzu ba, kawai ki tayani da Addu'a kar asirinmu ya tonu" yana gama fad'an haka sai ya mik'e ya shige d'aki, Safeena ta bi bayansa da kallo, ta yatsine baki tace
"ba Addu'an da zanyi, in maganar ta fito karshe dai ace an raba aurenka da Basma, kuma abinda nake so kenan".Shureym yana shiga d'aki ya kira Maminsa ya sanar mata duk abinda ke faruwa, hankalinta ya tsahi ta shiga yi masa fad'a, tace
"yanzu kazo kaja asirina zai tonu, a gaskiya ba yanzu naso ace maganar nan ya fito ba, domin hakan zai iyi barazana ga aure na, kuma kaima za ka fuskanci fushin Mahaifinka, gaskiya zan San abinyi" tana gama fad'a ta kashe wayar.Kai komo ta shiga yi a d'akinta tana tunanin hanyar da zata bullowa lamarin, zama tayi tayi dogon nazari, murmushi naga tayi sai ta ce
"Allah ya kaimu goben, na samo mafita".Da dare Shureym ya kira Basma a waya, yasan in yaje d'akinta ba zata bud'e ba, yace
"ki shirya gobe in Allah ya kaimu zamu tafi Nigeria, Dady ya kirani yace muje akwai Family miteeng, dan haka ki shirya da wuri da sassafe mamu tafi" cike da murna tace
"Allah ya kaimu" saita kashe wayar.Mikewa tayi, tayi rawa da tsalle, tana murnan zata ga family d'inta, kaya ta shiga had'awa kamar wacce zata bar garin duka ba dawowa. Zan iyace cewa barci b'arawo shine ya saceta, amma sam ta kasa sukuni, kosawa tayi gari ya waye.
*Washe gari*
Yau Basma harda yiwa Safeena sallama sai fara'a take mata, Safeena tace
"hoo su Basma za'a tafi min da miji sai dariya kike, to Allah yasa in kin tafi karki dawo" harara Yaya Shureym ya galla mata, saita gimtse sauran maganarta tana dariya k'asa-k'asa, Basma kuwa cike da dariya tace
"Ameen ya rabb, nima bana fata na dawo, kuma mijinki gaki ga shi, babu abinda zan miki dashi, ni dai na barki lafiya" saita fice tare da jan trolley kayanta.Safeena ta bisu har mota tare da musu Addu'a, haka suka wuce airport, Shureym yana cike da damuwa, Basma kuma cike take da murmushi.
*Nigeria*
Gidan President ya cika da dangi, sunzo sunata zumunci, da yake ya kama yau rana ce ta Juma'a, mazan gidan duka suka taru suka tafi babban masallacin Juma'a na Abuja.
Bayan sun dawo gida, iyayen maza da mata suka had'u a babban falon bak'i na shugaban k'asa, anan aka shirya musu abinci a tsakiyar falon kan babban dadduma daya mamaye falon, yara kuma suka baje nasu liyafar a part d'in Ammi, can suke hidimarsu.
Bayan sun gama cin abinci suka shiga hiran zumunci, Abba (President) ya kalli Dady (Gobno Ibrahim) yace
"Ibrahim yanzu gamu duk mun had'u gaba d'ayanmu, ina so ka sanar mana musabbabin had'uwarmu anan daka buk'aci muyi"Dady ya nisa ya d'ago ya kalli Abba yace
"naso ace Shureym da Basma sun zo tukunna sai kuji bayani a bakinsu, dan dama mun had'u anan ne domin su, na tabbatar suna gab da shigowa" Mai martaba yace
"A'a Ibrahim ka fara sanar mana da komai kafin zuwansu" Mami (Hajiya sa'a) tace
"kwarai kuwa, ya kamata mu ji komai, domin ni hankali na ya ya shi" Hajiya Fatima (Ammi) tace
"gwara ka fad'a kawai domin mu fara tattaunawa akai" ita dai Momyn Basma bata iya furta komai ba saboda nuna kawaici, Hajiya Murja Mahaifiyar Leema ita ma bata furta komai ba, Ummin Meena kuwa shuru tayi cike da damuwa a fuskanta.

YOU ARE READING
'YAR SHUGABA
Romance*'Yar Shugaban k'asa ce* Queen Basma, ta hakimce a seat d'in baya ita kad'ai, sai Meena 'yar Governor Kaduna ce ita ke driving, sai Leema 'yar Sarkin Kano wacce take gefen Meena. K'aran wak'ar Music na Larabawa ke tashi a motan, dukkan su suna bin w...