*'YAR SHUGABA*👑
_page_ *10.*
_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾Wani wajen shak'atawa ta kaisu ba wancen na farko ba, sun samu k'asan wata bishiya suka zauna kan kujeru, ga table a tsakiya, an kawo musu drinks ne da ruwa, Basma ko kallon Yaya Aryan batayi ba kuma tak'i magana, jikin Yaya Aryan yayi sanyi sai ya kwantar da murya yace
"Basma fushi kike dani?" kallo d'aya ta mishi a fak'aice sai ta kauda kai gefe, murmushi yayi yace
"haba k'anwata ki daina fushi dani mana, bana son ganin b'acin ranki, burina in saki farin ciki har k'arshen rayuwana" d'agowa tayi suka had'a id, idonunta fal da hawaye suna gabda zubowa, da sauri Yaya Aryan ya tara hannunsa a fuskanta domin hawayen ya sauka bisa tafin hannunsa, cikin wani irin murya wanda shi kanshi baisan yanada ita ba, mai dad'i da zak'i yace
"Basma karki min asaran hawayenki ya kai ga zuba a k'asa, ba tare da na sharesu ba, ki yafe ma Yayanki, ba zai zake b'ata miki raiba" murmushi tayi na jin dad'i, saita runtse idonta hawayen suka sauka bisa hannunsa, Yaya Aryan ya koma ya zauna, suna kallon juna ya d'aga hannunsa zuwa bakinsa ya lashe digon hawayen ya shanye, Basma saita tafa masa rap rap rap, cike da farin ciki tace
"wow, Yaya Aryan yau kawai na tabbatar da cewa ka d'aunke ni jinin jikinka kuma 'yar uwanka" murmushi yayi yace
"ke ce baki sani ba amma tun ranar da kika bani hak'uri na d'auke ki a haka, kawai dai na d'an nuna miki ni din Namiji ne" hararansa tayi na wasa tace
"ohoo dama shiyasa ka ke basar dani domin kaga rauni na ko, amma ba komai tunda ka fahimci yanda na d'auke ka" dariya yayi yace
"sosai na sani, Basma kin zama haske a rayuwana da Ahalina, sanadinki Umma da Deeja da Ni kaina muna farin ciki, kin mana abinda ban san dame zan biya ki ba face Allah ya baki miji nagari, ya kuma baki Aljannah" murmushi tayi najin dad'in abinda yace har cikin taranta, Abu d'aya ne taji ya mata wani iri lokacin da ta tuno da Yaya Shureym, tambayar kanta ta shiga yi,
"yanzu inna yi aure shikenan Yaya Shureym ya rabani da Yaya Aryan kenan?" Nan danan taji zuciyarta ya mata wani iri, ganin ta lula duniyar tunani, sai Yaya Aryan ya matso da fuskansa ya hura mata iskan bakinsa, nan take ta dawo hayyacinta, sai duk suka zubawa juna ido, suna baiwa junansu wasu sak'onnin cikin kwayar idonsu, suna karantar wa juna sirrin zuciyansu, sun d'auki tsawon minti biyar kana Yaya Aryan ya kashe mata ido d'aya, da sauri ta sunne kai k'asa alaman jin kunya, a gaskiya duk wanda ya gansu a wannan yanayin, babu abinda mutum zaice illa Aryan da Basma masoya ne.Yaya Aryan ya d'auko kujeransa ya dawo kusa da ita, da muryansa mai dad'i yace
"k'anwata meyasa ba kya jin kunyar kallon kwayar ido na? ke ce mace ta farko da take iya kallon ido na harta karanta wasu sirri dake ciki, domin ido naya d'aya daga cikin abinda kewa mutane kwarjini" murmushi tayi kawai ba tace komai ba, ya cigaba da cewa
"Amma na fahimci idanunmu sun fara sanin sirrin dake cikin juna, kema haka idonki yake kamar nawa" Basma sunkuyar da kai tayi k'asa, bata tab'a jin nauyi ko kunyar wani namiji ba sai akan Yaya Aryan, wasa take da yatsun hannunta, ta kasa motsi mai k'arfi, gaba d'aya tanajin ta a cikin sabon yanayi da bata tab'a jiba game da wani d'a namiji sai akan Yaya Aryan, a yanzu kunya da kwarjininsa ke tasiri a jikinta, Yaya Aryan ya kira sunansa yace
"Basma kinyi shuru ko yau ba kya jin tsokana ne, magana da kuma fad'a?" murmushi tayi tace
"ai Kaine kake magana, tun d'azu kake wasu bayanai da ban fahimcesu ba" murmushi yayi yace
"kina so ki sansu?" tace
"eh ina so" yace
"to d'ago fuskanki ki kalleni, zaki fahimci abinda nake nufi acikin ido na" ta d'auki minti d'aya kafin ta d'ago fuskanta, suka had'a ido ko wanne fuskansa da murmushi, sakonni suke zubawa zuciyoyinsu, ko wanne idonsa yayi tamkar mangyada aciki, bugun zuciyarsu yana buguwa a hankali, zan iya ce muku suna bugawa kusan a tare, idonun su yana k'eftawa a hankali tamkar ba zasu rufe ba, numfashinsu yana fita a hankali kamar basa cikin duniyarmu, sun d'auki tsawon minti bakwai, kana Basma ta yi ajiyar zuciya ta sun kuyar da kai, shima Yaya Aryan ajiyan zuciya yayi, cikin wani irin murya kamar yana rad'a yace, Basma kin fatimci abinda nake nufi yanzu?" murmushi tayi kawai ba tace komai ba.
DU LIEST GERADE
'YAR SHUGABA
Romantik*'Yar Shugaban k'asa ce* Queen Basma, ta hakimce a seat d'in baya ita kad'ai, sai Meena 'yar Governor Kaduna ce ita ke driving, sai Leema 'yar Sarkin Kano wacce take gefen Meena. K'aran wak'ar Music na Larabawa ke tashi a motan, dukkan su suna bin w...