13

1.1K 71 0
                                    

*'YAR SHUGABA*👑

_page_ *13.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

Hankalin Yaya Ahmad yayi matuk'ar tashi, cikin kulawa yace
"haba Aryan ya, kake abu kamar k'aramin yaro, nace maka Basma tana barci inna farka zansa ta kiraka" ajiyan zuciya Aryan yayi yace cikin damuwa,
"to shikenan nagode" nan suka yi sallama ya kashe wayar.

Basma ta farka da misalin k'arfe biyu na rana, Kaka Ma'u ta sanyata tayi wanka ta sauya kaya marasa nauyi, sallan Azahar ta gabatar kana aka kawo mata abinci, Kaka Ma'u ce ta matsa mata taci, loma uku tayi da kyar kana ta sha ruwa tace ta k'oshi, mik'ewa tayi kamar an tsikareta tace wa Kaka Ma'u tana zuwa sai ta fice, tayi sa'a falon ba kowa haka ta sanya takalmi ta fito haraban gidan, motocin gidan sun ragu da alama sun tafi raka su mai Martaba ne airport, hanyar k'ofar fita tayi tana waige-waige kamar mara gaskiya, masu gadi suka hanata fita, saita fara musu masifa akan su bata hanya ta wuce, ganin ta cije ne yasa suka bata hanya tawuce, tana fita, taga Yaya Ahmad zaune bisa wani dakali daga gefe ashe duk yana jin hayaniyansu, tsayawa tayi cak ta kasa tafiya, Yaya Ahmad ne ya mik'e yazo gabanta ya tsaya cike da tuhuma yace
"Basma bakya jin magana, ina zaki bayan an hanaku fita, ya kike so ki zama mara biyayya ne" fashe masa da kuka tayi, girgiza kai yayi ya kama hannuta suka koma cikin gidan, part d'in su ya wuce da ita ya zaunar da ita a gefen sa ya kira sunanta a nutse

"Basma kin ga abinda rashin ji ya haifar miki, naso ace haka bai faru ba, dana tsaya miki tsayin daka akan baki auri Shureym ba a baki wanda kike so, Basma meyasa kika aje tarbiyanki kika nima lalacewa haka, bayan kinyi saukar Al'Qur'ani har sau biyu, kina da sani akan littafai Addini sosai, a takaice in aka baki aji zaki iya rik'ewa a matsayin Malama, ya a kayi kika shagala da duniya haka Basma?"

Jikinta ne yayi sanyi sosai ta kuma b'arkewa da kuka tace
"Yaya wlh mun riga munyi kuskure, kuma wannan rayuwar a England muka koyoshi, insha Allah bazamu sake ba mun tuba, ni dai ka taimakeni karka bari a aura min Yaya Shureym wlh bana sonsa, kafi kowa sanin waye Shureym bai cancanta ya zama mijina ba" ajiyan zuciya yayi yace
"na sani Basma amma Abba ya riga ya yanke hukunci, ni shawara a gareki shine ki masa biyayya sai Allah ya sauk'ak'a miki lamarin"

"To Yaya kamin Addu'a, amma da son Aryan zan mutu"

Tsaki yayi baice komai ba wayarta ya d'auka yayi dailing number Aryan, bugu d'aya ya d'aga, sai ya mik'a mata ta kara a kunne, a cikin damuwa Aryan yace
"My Basma kina lafiya kuwa?" kuka ta saki wanda hakan yayi dai-dai da k'ara rikicewansa, cikin damuwa yace
"meya faru gayamin mana ko so kike nima nayi kukan". Tuni Yaya Ahmad ya bata wurin domin ya gaji da jin kukan nata, Basma ta shiga bashi labarin komai bata b'oye ba, ai zubbur ya mik'e a tsorace yace
"Basma shikenan kinyi sanadin rabuwanmu, shikanan kin jawo mana damuwa mara yankewa" ya k'arasa maganar cikin rawar murya, Basma sai tai k'ara tsinkewa da sabon kuka, Aryan kashe wayar yayi gaba d'aya, Basma taita dialing number akashe, a firgice ta mik'e ta fita da gudu, Yaya Ahmad yana waje, ganin ta a guje yasa ya bita a guje, wurin gate ta nufa, masu gadi suka tare ta, kuka take da magiya akan su barta ta fita, amma suka k'i har Yaya Ahmad ya cimmu su.

Kama hannunta yayi gam yana janta, ihu sa saka tana tirjiya, ihun ta ne ya dawo da duk hankulan mutanan gidan duk suka fito a guje, da yake sun dawo daga rakiyan, kafin su k'arasa cikin gidan sosai Basma tayi wani ihu saita langwab'e, a razane Yaya Ahmad ya juyo yaga idanunta sun kafe ta suma, jikinsa na b'ari ya d'auketa tsak ya shiga cikin gida da gudu, a hanya yaci karo dasu momy, nan ya kewaye su ya wuce da ita part d'in president, a falon ya ajeta duk suka shigo ko wanne ya rufa a kanta, Ammi ne keta kiran sunanta amma shuru, da gudu Meena ta kawo ruwa aka yayyafa mata, lumshe ido tayi tare da sauke ajiyan zuciya mai k'arfi, President da kansa yazo ya d'auketa cak ya haye da ita sama, ya kuma yi gargad'in kar wanda ya biyoshi, a zata yayi akan gadonsa ya d'auki wayansa ya kira likitansu.

'YAR SHUGABAWhere stories live. Discover now