19

999 67 0
                                    

*'YAR SHUGABA*👑

_page_ *19.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

*Nigeria*

Abba sun sauka lafiya cikin dare, ya shaida ma su Momy Basma na gaishesu ba wata Matsala. Yaya Naufal ya labaratawa Yaya Ahmad duk abinda ya faru, damuwa ne ya ziyarceshi yace
"anya kuwa Shureym na kula da Basma?" Yaya Naufal yace
"yana kula da ita a yanda muka gani, kuma ai in da da matsala zata gayawa Abba" murmushi kawai Yaya Ahmad yayi a ransa yace
"ban yarda ba dole zanyi bincike akai, dan Basma tana da zurfin ciki, ni kad'ai take gayawa damuwanta ko Momy" a fili kuma yace
"hakane, to Allah ya bata lafiya ya k'ara musu zaman lafiya"
"Ameen" Yaya Naufal yace, kana ya wuce part d'inshi.

*Kasar Monaco*

Aryan yayi nisa cikin karatunsa, a yanzu hankalinsa ya kwanta, sai dai har yanzu bai maida jikinsa ba, yana waya dasu Umma da Khadija sai Yaya Ahmad, yanzu ya daina kashe wayansa kullun tana kunne, har yanzu bai dawo cikin walwala ba, baya dariya sai dai yak'e kuma shima saiya d'auro, murmushi ne kawai ya kanyi time to time.

Wata rana yana makaranta ya fito daga aji yana tafiya, karo yaci da wata ta tawo a guje bata lura dashi ba, d'agowa tayi cike da tsoro, cikin harshen turanci tace
"yi hak'uri wlh ban kula bane" gyad'a mata kai kawai yayi sai ya rab'eta ya wuce, binsa tayi da kallo cike da tunani barkatai,

"iya had'uwa wannan guy d'in ya had'u, ko dan wani kasa ne oho? Gaskiya bazan bari ya kub'ucemin ba, dan na kamu da sonsa, kuma shine dai-dai tsarina"

Abinda take fad'a a ranta kenan, da gudu ta bi bayanshi, bata san sunanshi ba gashi ya tsere mata, duk da haka bata hak'uri ba, ta cigaba da bin bayansa da gudu ta cimmasa, gabansa ta sha, sai ta tsaya cike da yin nishi tace

"Yi hak'uri na tsaidaka, sunana Jidda Bukar, ni 'yar Nigeria ce katsina state, muna zama a Abuja, nazo nan karatu ne, in ba zaka damu ba ko zan san daga ina kake? dan kayi min zubin d'an k'asar India"

Murmushi yayi a takaice yace cikin harshen turanci
"sunana Aryan Aliyu, Dan k'asar Nigeria" ido ta zaro tace
"wow ashe k'asarmu d'aya, wlh gani nayi ba kayi kama da 'yan Nigeria ba, amma nayi murna sosai, cewa nayi bari na biyo ka saboda naga Kana da sauk'in kai, in ba damuwa ko zamu kulla abota" ransa ne ya b'aci, amma saiya dake cikin rashin sakin fuska yace
"nagode, amma ba zai yuwu ba kawai, in dai mun had'u sai mu rik'a gaisawa" yana gama fad'an haka ya wuce, binsa ta cigaba da yi tare da yi masa magayi akan suyi exchangen number, tsayawa yayi zuciyansa na tafasa cikin masifa yace
"ya isa dan Allah, kiyi hak'uri ina da mata, pls ki fita a harkata, sai wani bina kike kamar naci miki bashi" jikinta ne yayi sanyi bata k'ara furta komai ba sai ta juya ta fara tafiya, tausayi ta bashi sai ya dakatar da ita yace
"Jidda kiyi hak'uri ban cika son ana takura min ba" juyowa tayi idonta ya cika da kwalla tace
"ba komai na fahimceka" Numbern shi ya karanta mata, kana suka yi sallama.

Ta wuce cike da murna shi kuma ya tafi cike da tunanin Basma, ji yake kamar yaci amananta, wani b'angare na zuciyansa yace
"bakaci amana ba, itama ai tanacan tare da mijinta" runtse idonsa yayi hawaye mai zafi ya fito masa, ji yayi komai ya dawo mishi sabo, zazzab'i ne ya rufeshi, sai ya tafi gida cike da matsananciyar damuwa.

Tun daga wannan ranar Jidda ta mak'alewa Aryan, Sam baya son abinda take masa, yana k'ok'arin janye mata amma sai k'ara shige masa take, ita burinta bai wuce ta samu zuciyar Aryan, ko bazai aureta ba tunda yace yana da mata, zata amince masa su tab'a rayuwa ko kad'an ne, domin tana fama da sha'awansa.

Aryan yana gida a kwance da yamma, sai yaji anyi masa knocking, tashi yayi ya tafi ya bud'e, mamaki me ya rufe shi ganin Jidda ce, murmushi tayi masa sai tabi gefensa ta shige d'akin, binta yayi da kallon yana mamakin yanda akayi tasan gidansa, cikin nuna ko rashin damuwa Jidda ta cire mayafinta ta zauna a kan kujera mai mazaunin mutum d'aya, komawa yayi ya zauna kujeran dayake fuskantarta tace

'YAR SHUGABAWhere stories live. Discover now