*'YAR SHUGABA*👑
_page_ *22.*
_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾Da misalin k'arfe uku na dare, Basma ta tashi ta gabatar da sallan Nafila, Addu'a tayi da niman yardan Allah akan abinda take shirin yi, haka ta zauna tayi ta tasbihi, har gabanin sallan Asubahi, kana ta k'ara yin alwala tayi raka'atanil fijri, sannan ta gabatar da sallan Asubahi, azkar ta karanta, sai ta tashi ta nad'e sallaya, idonta a rufe ta fad'a gado, murmushi ta saki, a ranta tace
"ashe ma Yaya Shureym mugun wawa ne, da nasan haka yake da saukin kai da tuni nasan abinyi, wai su sun d'auka da gaske period nake, hmm kana tunanin cin zarafin da kayi min da sharrin da kamin kasha ni masilla ne, wlh saina d'auki fansa mafi muni a gareka, azzalumi kawai" tsaki taja saita gyara kwanciya, cikin k'ank'anin lokaci barci mai nauyi yayi gaba da ita.
Sai k'arfe goma na safe ta farka, wanka tayi ta shirya cikin riga da sket English wears, ba wani makeup da tayi, fitowa tayi taga su Yaya Shureym suna Karin kumallo, murmushi ta sakar musu saita k'arasa wurin taja kujera ta zauna, gaishe su tayi suka amsa cikin kulawa, tace
"kuyi hak'uri na makara ban tashi da wuri na had'a mana breakfast ba" murmushi Safeena tayi tace
"Basma kenan, karki damu ai nice da girki, nasa kuku ya had'a mana tunda ni gaskiya bana girki" Basma harta kai hannunta zata jawo food wormer sai ta janye hannunta jin Safeena na fad'in kuku yayi musu breakfast, da sauri tace
"gwara da ban zuba ba, dan bazan iya cin girkinsu ba" mik'ewa tayi ta wuce d'aki, shi dai Shureym saurarensu yake yi yana kai loman abinci, a ransa yana yabawa Basma"yanda take k'ok'arin yin abinci da kanta duk irin matsayinta da take dashi na 'YAR SHUGABAN K'asa, amma ita Safeena ba 'yar kowa ba sai iyayin tsiya, k'ilama bata iya bane, dan Ni ban tab'a cin girkinta ba"
Maganar Basma shine ya dawo dashi daga zancen zuci da yake, tace
"Yaya Shureym bari naje naci abinci" kallonta yayi sama da k'asa yace
"amma kinsan yanzu ba zan yarda da wannan fitan naki ba ko" marairaice fuska tayi tace
"yaya takeway kawai zanyi na dawo" d'aure fuska yayi yace
"ni bawai fitan bane damuwa na, kawai bana so ki had'u da d'an iskan saurayinki d'in nan ne" idon Basma ya ciko da kwalla bata ce komai ba, saita juya zata koma d'aki, dakatar da ita yayi yace
"kije amma na baki minti talatin, in kika bari ya wuce, to kinfi kowa sanin hukunci na, bawai na bari bane sanyi kawai nayi" bata tanka mishi ba, ta wuce abinta tana kissima abinda zata aikata mishi.Tana fita studio ta wuce, wayarta ta basu ta nuna masu hotunan da take so a wanke mata, tana gama musu bayani ta wuce siyan abinci. Cikin sauri ta dawo ta basu kud'insu ta karb'i hotunan da wayarta, ta adana su a jaka, kana ta fita cikin sauri, taxi ta tara ya sauketa a gida ta shiga da sauri.
Ta taddasu a falo,
"sannunku da hutawa" tace, kana ta nufi d'akinta, Yaya Shureym ya dakatar da ita, damm taji gabanta ya fad'i, amma saita dake ta juyo, kallonta yayi yace
"amma kinsan kin d'auki kusan minti arba'in ko, daga siyan abinci shine zaki d'auki wannan lokacin" marairaice fuska tayi tace"haba Yaya Shureym, kasan k'asar nan bafa Nigeria bane, duk yanda na tadda layi sai an sallami wanda suka rigani kafin a bani, su ba ruwansu da cuwa-cuwa, kuma bada motan gida na fita ba, da taxi ne"
Kallonta yayi a takaice kana ya d'auki telephone ya kira masu gadin gidan, tare da duk ma'aikatan gidan, bayan sunzo yace tare da nuna Basma
"karku sake ku bar wancen ta fita a gidan nan sai in na baku izini" duk wannan bayani a cikin harshen turenci yake musu, cikin girmama suka amsa masa kana ya sallamesu suka fita, mik'ewa yayi ya zo inda ta tsaya kana ya amshi ledan take away d'in, yace
"muje na taya ki ci" gabanta ne ya shigo dukan uku-uku, burin ta karya buk'aci ganin abinda ke cikin jakarta, haka suka jera suka shiga cikin d'akin, Safeena wani bak'in kishi ne ya tirnik'eta, tsaki taja tace

YOU ARE READING
'YAR SHUGABA
Romance*'Yar Shugaban k'asa ce* Queen Basma, ta hakimce a seat d'in baya ita kad'ai, sai Meena 'yar Governor Kaduna ce ita ke driving, sai Leema 'yar Sarkin Kano wacce take gefen Meena. K'aran wak'ar Music na Larabawa ke tashi a motan, dukkan su suna bin w...