*'YAR SHUGABA*👑
_page_ *16.*
_Na_
_*Rahma Kabir*_Yana isa d'akin ya shiga bugawa, kwance take bisa gadonta tana kallon tv, koda taji bugun k'ofan, ta d'auki kusan minti uku kafin ta mik'e ta nufi k'ofar ta bud'e, tsaye ta ganshi yana k'are mata kallo, miyau ya had'iye da k'arfi, gaba d'aya hankalinsa ya tashi da ganin Basma cikin k'ananun kaya, hararansa tayi cikin tsiwa tace
"Malam lafiya ko da matsala ne"
guntun murmushi yayi bai ce komai ba, sai yabi gefenta ya kutsa kai cikin d'akin, zama yayi kan kujeran zaman Mutum d'aya, ya shiga k'arewa d'akin kallo yana shakar kamshin d'akin, wanda ya saukar masa da kasala had'e da tsananin sha'awar Basma, ita kuma tura k'ofan tayi ta koma cikin d'akin ta zauna gefen gadonta ta cigaba da kallon tv, sun kai minti biyar a haka ba tare da wani yace wani abu ba, Yaya Shureym ne ya katse shurun yace
"Basma meyasa bakya fitowa falo ki zauna?"
Cikin nuna ko in kula tayi banza dashi, yace
"magana nake kinyi banza dani" Cikin yatsina fuska tace"naga cewa wannan ba matsalan ka bane, ka je ka cigaba da zama da karuwanka, don ni ban yarda aure ku kai ba, kyamarka nake ma, da zaka taimaka ka tashi ka fita da ka kyauta min"
"Iya b'acin rai ransa ya baci, mik'ewa yayi da sauri zai isa inda ta zauna, ai da sauri itama ta mik'e tana ja da baya harta isa jikin bango, kankame jikinta tayi ta runtse ido domin yanda taga ransa ya b'aci ta sadakar zai duketa, gabda ita ya tsaya wanda hartana jin hucinsa, hannunta ya shiga b'amb'arewa a jikinta, a razane ta bud'e ido tana kallonsa, ba tayi aune ba ya rungumeta da k'arfi ya matseta a jikinshi, tirjiya ta shiga yi tana k'ok'arin kwatar kanta, ganin ya rik'eta gam yak'i sakinta, saita gantsara masa cizo a damtsan hannusa, da sauri ya saketa yana yarfe hannu, saita maza ta matsa a gun, yana jiyowa ya nima k'ara kamota, da sauri ta ruga, guje-guje suka fara a cikin d'akin, yana k'ok'arin kamata tana kaucewa.
Safeena shiganta d'aki da tayi, tana tsammanin Shureym zai biyo bayan ta, sai taji shuru, ganin haka yasa ta lek'a falo sai taga wayam baya gun data barshi, cike da masifa ta fito ta nufi d'akin Basma, tana bud'e k'ofa sai ta cimmusu suna wannan wasan guje-guje, ai sakin baki tayi tana kallonsu, shiga ciki tayi rai b'ace, Shureym yana ganinta yayi sauri ya tsaya yana sosa k'eya, mugun kallo Safeena tabi shi dashi bata ce masa uffan ba, sai nuna masa hanyar waje tayi alaman ya fita, sum-sum ya fita yana murmushi k'asa-k'asa, yana fita ta gyara tsayuwa tana kallon Basma tace
"A hir d'inki da Mijina domin ba sa'anki bane, in kuma ke mayya ce to Mijina yafin k'arfinki, ki shiga taitayinki domin wlh inna kuma ganin haka zan d'auki tsastsauran mataki mafi muni a gareki" tsaki Basma tayi tace cikin fad'a
"ai ko wlh da kinga yanda zanyi k'asa-k'asa dake, ke d'in banza ke wacece da zaki zo ki nima shiga tsakanina da Mijina kuma d'an Uwana, kefa ba kowa bace face karuwa mara lasisi mara mutunci, ki gaugauta fita sabgata domin had'uwata dake bazai yi kyauta, kibar ganin ina miki shuru-shuru, jaka kawai"
Ai tuni Safeena ta cika ta b'atse, magananun Basma sun tunzurata, bata san lokacin da tayi kukan kura ba ta nufi Basma gadan-dagan, Basma na ganin tayo kanta sai ta shige bayi da gudu tare da sanya key, tana maida numfashi, iya tsoro ta tsorata da Safeena, dan ta girmeta kuma ta fita girman jiki, tace a fili
"ko banza nasha dakyar muguwa kawai" Safeena tana ganin ta shige bayi sai tayi kwafa, ta fita da sauri.
Ta tada Shureym a d'akinsa, ta shiga surfa masa masifa shi dai uffan bai ce ba, da ya gaji da jin haya niyarta sai ya shige baya danyin wanka ya barta tsaye baki na kumfa, a ransa yace
"Safeena akwai masifa, ta dage ta hakikance akan abin da yake halal d'ina, gaskiya bazan d'auki wannan sakarcin ba, domin ko ban son Basma ai ina feeling d'inta, balle ma ina sonta kawai kauda kai nake ina miki biyayya, saboda ina tsananin sonki, amma nasan hukuncin da zan d"auka"

YOU ARE READING
'YAR SHUGABA
Romance*'Yar Shugaban k'asa ce* Queen Basma, ta hakimce a seat d'in baya ita kad'ai, sai Meena 'yar Governor Kaduna ce ita ke driving, sai Leema 'yar Sarkin Kano wacce take gefen Meena. K'aran wak'ar Music na Larabawa ke tashi a motan, dukkan su suna bin w...