24

1.1K 67 0
                                    

*'YAR SHUGABA*👑

_page_ *24.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

*Etopia*

Basma ta sauka a jirgi, sai rarraba ido take ko za ta ga wanda zata iya tambaya, jikinta yayi sanyi ganin tazo garin da bata tab'a zuwa ba, tsoro da fargaba ne ya cika ta, runtse ido tayi ta bud'e tace a fili
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil, laa ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazza zalumin, astagfirullah wa'a tubu ilai" abinda tayi ta maimaitawa kenan a zuciyarta, a hankali ta soma jin k'arfin gwiwa da natsuwa, fitowa tayi bakin hanya ta tari taxi, cikin harshen turanci tace
"Hotel mai kyau nake so ka kai ni" cikin harshen turanci ya mai da mata da
"to shigo mu tafi". Ya kai ta babban hotel mai kyau, ta biyashi kana ta wuce ciki, kud'in d'aki ta biya, saita ja trolley d'inta, wata daga cikin ma'aikatan Hotel d'in suka yi mata jagora har d'akin data kama.

Wanka tayi ta gabatar da duk Sallolin da ake binta, bata jin zata iya cin abu mai nauyi, telephone ta d'auka ta kira cikin holel d'in da a kawo mata coffee da kuma Burger, haka suka kawo mata, ta soma cin Burger taji sam teste d'insa ba dad'i, ajiyewa tayi tasha coffee d'in kawai. Tunanin ya za tayi rayuwa anan take yi, can ta tuno da rayuwarta da Yaya Aryan ta tabbatar da shi ta aura duk haka bazai faru ba, kuma ba zata sha wannan wahalar ba, hawaye ya sauka a kuncinta, tace

"ya Yaya Aryan zaiji in yaji labarin na gudu" tunani barkatai tayi kamar zata kunna d'ayan wayarta saita fasa, dan tasan za'a iya nimanta ta layin, cire sim d'in tayi a wayan sai ta adana a cikin wallet d'in ta. Lafiyan gado tabi ta kwanta tana tunanin rayuwa, da haka barci ya d'auke ta.

*America*

Yaya Shureym sun dawo daga Asibiti, baifi minti 20 da wucewar Basma ba suka dawo, hon yayi amma yaji shuru ba'a bud'e masa ba, ba gate man a wurin, saukowa yayi ya bud'e da kansa ya koma mota ya shigo da ita, bai damu daya rufe gate d'in ba, waige-waige yayi amma bai ga ma'aikatan gidan ba, tsaki yaja sai suka shiga falo.

Suna shiga suka fara jin ihu da hayaniya daga cikin falon, bin inda ihun ke fita suka dinga bi har suka isa k'ofar d'akin Basma, kallon-kallo Shureym da Safeena suka yi suna tunanin su waye a ciki, Shureym ne yayi k'arfin hali ya bud'e k'ofar, arba yayi da mai gadi da sauran ma'aikatan gidan sunyi gwimi sai zaro ido suke yi, cike da mamaki ya shiga tambaya su, nan suka bashi amsa, murmushi mugunta Yaya Shureym yayi ya kalli Safeena yace

"kinga aikin shaid'aniyar yarinyar nan ko, wato kwana biyu tayi lamb'o ta natsu kamar ba ita ba, amma yau tasa kai ta fita duk dokar dana sa mata, baisa ta fasa k'etare wa ba, ta musu dubara ta fice, wlh yau inta dawo Ni da ita ne, sai nayi mata dukan da tunda aka haifeta ba ayi mata shi ba, kuma yau saina amshi hakk'ina da k'arfin tsiya"

Yana gama fad'an haka ya wuce ya bama Safeena wuri, Safeena jikinta yayi sanyi, domin ta fara tsorata da lamarin Shureym akan yanda ya damu da budurcin Basma, kishi ne ya rufeta saita bi bayansa a fusace.

Masu gadi haka suka fita sum-sum, dan ba suji duk abin da suke cewaba, a cikin Hausa su kayi magana, sun koma bakin aikinsu.
Safeena ta cimmasa a cikin falon, ya zauna sai gumi yake yana kwafa yace
"Yarinyar nan ni zata rainama wayo, ni bata bani hakk'ina ba taje bama wancan d'an iskan, wai ta yaya zan yarda ba bin maza Basma take yi ba" Safeena ce tace

"Wai kai Shureym meyasa ka damu da Basma ne haka? yarinyar da bata sonka batasan kana yi ba, plss karabu da ita mana ka huta" cikin tsawa yace

"ya isa, ya isa Safeena, wlh kika kuma furta kalman in saki Basma sai na miki abin da baki tunani, banda albarka cin cikin dake jikinki da saina huce haushi na akan ki, kuma in baki sani ba ki sani ina matuk'ar son Basma, son da ban tab'a yiwa wata Mace ba, ban yiwa kaina ba, na gaji da danne zuciyana akan Son da nake mata dan kawai in saki farin ciki, tom daga yau na daina b'oyewa ina son Matata sosai"

'YAR SHUGABAWhere stories live. Discover now