*'YAR SHUGABA*👑
_page_ *2.*
_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾Su Basma suna isa club, suka wuce cikin hol d'in, mutane ne sosai a ciki maza da mata, daka gansu kaga 'ya'yan manya, tsautsayi ne zai kai d'an talaka wurin, kid'a da sauti ke tashi kowa na zaune, kamar yanda suka saba zuwa suna da nasu wurin zama na musamman, duk suka zauna, aka cike musu wurin da kayan motsa baki, wani kyakkyawan Guy ne yazo kusa dasu suka gaisa Amma banda Basma domin bata shiga harkan Maza, Leema ce ta mik'e saurayin mai suna Jalal ya rik'ota ta kugunta suka wuce tare da hiransu na masoya, fita sukayi a wurin suka wuce cikin hotel da club d'in ke ciki. D'akinsa ya bud'e suka shiga, kamar suna jirace da juna suka fara kaiwa juna sak'onni, nan da nan suka rikice suka lula duniyar shashanci, Allah ya shirya Ameen, nan na fito na basu guri.
Ita kuma Meena ta mik'e ta wuce group d'insu na mashaya, wurin mata ne da maza a had'e, suna ganinta suka fara ihu, wuri suka bata ta zauna ta fara aikawa da syrup.
Queen itama Abokan rawanta suka matso kusa da ita nan suka d'unguma zuwa saman dandamali, nan fa kowa hankalinsa ya tashi ganin Basma ta hau, hayaniya ya k'aru suka fara ihu domin sunyi missing ganin rawan Basma, aka d'aura mata best wak'arta na music d'in labarawa, Queen Basma ta soma rawa mai ban mamaki tamkar ba jikinta take k'aryawa ba, sai wuri ya kuma hautsibewa da ihu, dama abinda Basma keso kenan, mutane suka fara mata yayyafin kud'i masu taya ta rawa suka k'ara dagewa farin ciki ne ya rufe su domin sunsan yau zasu kwashi kud'i. Dan in sun gama Basma cewa take a basu kud'in su raba.
Sai da taci rawa mai isarta kana ta sauka ta samu guri ta zauna tana maida numfashi, sauran 'yan rawar suma suka sauka, aka kwashe kud'in su tas aka basu, farin ciki ya gama rufesu domin yau sun samu kud'i sosai, suna alfahari da Queen data zama star d'insu.
Sai misalin k'arfe ukun dare suka dawo gida, ko wacce ta nufi d'aki ta kwanta, nima saina tayasu rufe k'ofa nace saida safe.
*Washe gari*
Da misalin k'arfe takwas na safe Aryan yayiwa Umma sallama ya wuce kasuwa kamar kullun, yana isa rumfansa hawaye ya ciko fal idonta, girgiza kai yayi saiya bud'e k'aton buhu da yake kasa kayan miya, haka ya karkasa tumatur, tarugu, sai tattasai, samun wuri yayi ya zauna daga inda rufin shagonsa ya kifa ya rab'e, sai ya rafka tagumi ya fara tuno rayuwansu.*ASALIN ARYAN? "*
Sunan mahaifinsu Aliyu, Asalinsu fulanin Gombe ne, mahaifinsa ya rasa Iyayensa tun yana k'arami, a wurin k'anin Baffansa ya tashi Malam Mu'azu, ya had'ashi da yaransa su biyu Aisha da Ibrahim ya rik'e. Matarsa Inna Amina suna kiranta da Inna Lami ta rik'e Aliyu Amana tamkar ita ta haifeshi, duk inda Aliyu yake Khalil na wurin, sun tsaku sosai makaranta tare suke zuwa, ga k'anwarsu Aisha suna ji da ita.
Wata rana Inna Lami ta aiki Khalil kasuwa shuru-shuru bai dawo ba har aka d'auki tsawon lokaci, abu kamar wasa Khalil ya b'ace anyi niman duniya amma ba amo ba labari, Malam Mu'azu da Inna Lami sun shiga tsananin damuwa, tun ana kwana d'aya da b'atan Khalil har ya d'auki tsawon wata ba'a ganshi ba balle aji labarinsa. Haka su Inna suka runguma Aliyu da Aisha suka barwa Allah lamarin sa da Addu'an Allah ya bayyana musu Khalil ko a mace ko a raye. Aliyu kuwa har rashin lafiya yayi saboda rashin d'an uwansa.
*Bayan shekaru*
Aliyu ya gama diploman sa a b'angaren kasuwanci, yana da shekaru 26. Aisha kuma tana da shekara sha takwas Malam Mu'az ya had'a Aliyu da Aisha auren zumunci, basu damu ba dama suna son junansu saboda akwai shakuwa mai k'arfi a tsakaninsu, Ana d'aura musu Aure sai suka tare a wani gefe daga cikin gidansu.
Bayan wata biyar da aurensu wani abokin Malam Mu'azu yazo Gombe mai suna Alhaji Sani, Malam yayi masa kyakkyawan tarba, d'aya tashi tafiya ya rok'i Malam akan ya bashi Aliyu ya tafi dashi Abuja tunda yayi karatu, ya d'auke shi aiki a companyn sa, da farko Malam bai yarda ba, amma daga baya saiya amince bisa sharad'in sai dai Aliyu ya tafi da matarsa, Alhaji Sani ya amince, cikin kwana biyu suka shirya sai garin Abuja.
YOU ARE READING
'YAR SHUGABA
Romance*'Yar Shugaban k'asa ce* Queen Basma, ta hakimce a seat d'in baya ita kad'ai, sai Meena 'yar Governor Kaduna ce ita ke driving, sai Leema 'yar Sarkin Kano wacce take gefen Meena. K'aran wak'ar Music na Larabawa ke tashi a motan, dukkan su suna bin w...