25

1.2K 73 0
                                    

*'YAR SHUGABA*👑

_page_ *25.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

*K'asar Monaco*

Yaya Aryan tunda gari ya waye yaji gaba d'aya hankalinsa ya koma Nigeria, tunani barkatai ya shiga yi, cikin sauri ya mik'e ya shiga had'a kayansa, yana kammalawa yayi wanka ya shirya cikin Manyan kaya, Shadda ganila ash color ya sanya hula bak'i da takalmi, tare da sanya bak'in tabarau, yayi matuk'ar kyau, hakanan ya tsinci kansa cikin nishad'i, burinsa bai wuce ya ga Ummansa, ya wuce airport sai Nigeria.

*America*

Su Abba sun kamo hanyan Nigeria, Shureym ya tafi office d'insa ya aje musu komai nasu, ya sallame su, sunyi-sunyi ya k'arasa aikinsa amma yak'i dole suka hak'ura, gida ya koma ya kwashi kayansa, Safeena na biye dashi ba um ba um-um a tsakaninsu, sun shiga mota da duk kayansu, shureym ya sallami duk ma'aikatan gidan ya bama wani abokin aikinsa Key d'in gidan, dama gidan na ma'aikatansu ne, airport suka wuce baifi minti talatin da zuwansu ba jirginsu ya d'aga sai Nigeria.

*Nigeria*

Yaya Aryan ya sauka lafiya, taxi ya shiga ya sauke shi a gida, yana shiga suka gaisa da mai gadi, ciki ya shiga ya wuce d'akinsa, wanka yayi ya sanya k'ananun kaya, kana ya nufi sashin Umma, bata san da dawowansa ba, domin yana so yayi surprising d'inta, yana shiga falo yaga Iya mai aikinta suka gaisa Iya tace
"aiko Hajiya bata nan" zama yayi ya kira number Umma ringing biyu ta d'auka yace
"Umma kina ina na dawo ina son in baki mamaki kuma bakya gida, da safen nan ina kika je haka?" murmushi tayi tace
"Aryan wani irin ka dawo, ba munyi da kai sai nan da wata uku zaka dawo ba, meya dawo da kai yanzu?" dariya yayi yace
"Umma hankalina ya dawo gida ne wlh, kewarku ya cikani sosai, shiyasa na dawo, yanzu kina ina ne?" tace
"ina gidan shugaban k'asa wurin Khadija" yace
"Da fatan dai lafiya ko?"

"lafiya lau, ka k'ara so ka gaishesu mana"
"To Umma gani nan zuwa" haka ya mik'e ransa bai masa dad'i, yana ji kamar karya je.

Khadija ta kira Umma ta sanar mata da abinda ke faruwa, dalilin zuwan Umma kenan da safen domin tayi musu Allah ya kyauta.

Yaya Aryan ya isa gidan president, ya same su Umma a part d'in Momy, zama yayi a k'asan kafet, Kansa a sunkuye ya gaishe dasu Ammi, ganin falon cike da mutane ya sashi jin wani iri, sai ya fito Deeja ta biyo shi a baya.

Sun zauna a barandan shan iska dake cikin farfajiyan gidan, nan suka k'ara gaisawa suka shiga hiran zumunci, Deeja bata yi gigin gaya masa abinda ke faruwa ba, Umma ce ta fito ta samesu suna zaune cikin barandan, murmushi Umma tayi, farin ciki ne ya mamayeta Aryan ya dawo da walwalansa, Addu'a tayi Allah ya bashi mata ta gari. K'arasawa tayi wurin tace
"Deeja ni zan tafi in Ahmad ya dawo ki gaishe shi" Deeja ta kwab'e fuska kamar za tayi kuka tace
"kai Umma baki dad'e ba fa, kuma da kin jira sun kusa k'ara sowa ma" murmushi tayi tace
"haba Deeja baki ganin Yayanki ya dawo ne, so nake inje in had'a masa abinci dan nasan da wuya inya karya ma" Murmushin jin dad'i Yaya Aryan yayi yace
"kinsan kuwa Umma nayi missing d'in Abinci ki, kuma akwai yunwa a tare dani, ki tafi kawai nima ina bisa hanya" dariya tayi tace
"yauwa Aryan saika tawo" nan tayi sallama da Deeja ta wuce ta shiga mota driver ya jata sai gida.

Aryan suna zaune a wurin Yace
"Deeja lafiya naga gidan naku da taron mutane?" murmushi yak'e tayi tace
"lafiya lau, president ne yayi umarni da duk a taru anan, mutanen kano da Kaduna duk sunzo, yanzu jiran isowarsu muke daga America" yace
"to Allah yasa lafiya, Nima ina ganin bari na gudu ba zan iya jiran su dawo ba, zuwa gobe in Allah ya kaimu zanzo na gaishesu" bai rufe baki ba, motoci suka fara shigowa cikin haraban gidan, Deeja tace

"laaa gaka sun dawo ma muna zancen su" murmushi kawai yayi baice komai ba, yana kallon mototcin da suke shigowa, da sauri ya mik'e lokacin yaga su Yaya Ahmad sun fito ya isa wurin yana dariya, suka kama hannun juna cike da farin ciki a fuskokinsu Yaya Ahmad yace
"Aryan saukan yaushe?" cike da dariya yace
"yau na sauka"
"to kai da mu kayi waya kace sai nan da wata uku zaka dawo" murmushi yayi yace
"wlh naji hankali na yayo gida burina in ganin a Nigeria" gaban yaya Ahmad ne ya fad'i amma saiya dake, ya mayar masa da murmushi yace
'lallai fa kace kana kewarmu"
"kwarai kuwa nayi"

'YAR SHUGABAWhere stories live. Discover now