38

1K 57 0
                                    

*'YAR SHUGABA👑*

_page_ *38.*

_Na_
*_Rahma Kabir✍🏾_*

Koda suka isa Asibiti direct d'akin Likita suka nufa, nan take aka fara mata tests da sauran gwaje-gwaje, Likita ya tabbatar musu tana d'auke da juna biyu harna tsawon wata biyu, Yaya Aryan farin ciki sosai ya kama shi, hatta ita kanta Basma farin ciki ya rufeta, nan take Likita ya rubuta musu Magani suka siya a pharmacy na Asibiti suka kamo hanyar Gida. Suna tafi bisa hanya Aryan tuk'i yake a hankali kwance cikin natsuwa, wani irin nishad'i suke ji mara misaltuwa, hannunsa ya d'aura kan cikinta, da sauri ta kalleshi sai ya kashe mata ido d'aya cikin wani salo na murya yace

"Ki kula min da kanki da Unborn Baby d'inmu plss"

Murmushi tayi ta gyara zama tace cikin shagwab'a
"Uhum Ni fa nayi k'arama da Haihuwa dan bazan iya ba Haihuwa ba ance da wahala, tsoro nake ji"

Waro ido waje yayi yace
"To me kike nufi"
"Ni dai tsoro nake ji amma ina son cikin sosai"

Dariya yayi yana buga sitiyarin mota yace
"wow My Basma rikici, bafa wani wahala da kinyi nishi shikenan fa"

Hararan wasa tayi masa tace
"ai su Meena sun bani labarin wahalan da suka sha wajen Haihuwa, ni dai ka tayani da Addu'a kar ya bani wuya Myn" ta k'arasa maganar cikin shagwab'a. Shafa gefen kumatunta yayi yace

"Babyna kullun cikin Addu'a nake miki karki damu, insha Allah zaki Haihu lafiya dashi" murmushi tayi ta amsa da "Ameen". a haka suka isa gida cike da farin ciki.

*Bayan Kwana Biyu*
Suna kwance Basma tayi pillow da hannunsa tace

"Baby ina so karka gayawa kowa ina da ciki, nafi so su ganshi in ya fito"
"Saboda me" ya jefa mata tambaya.

"Kunya na keji"
"Uhum su kunya ko, in ya fito zanga yanda za kiyi"

Mirginawa tayi ta kwanji samansa, ido cikin ido suke kallon juna sai ya sakar mata Murmushi, murgud'a masa baki tayi saiya sanya hannu ya kama bakin, kukan shagwab'a ta fara sai ya saki yana dariya, tace

"Baby ina son shan agwaluma"
"What, ya fad'a da k'arfi, Na manta shi ma"

kuka ta shiga rerawa ita lallai fa zata sha agwaluma, marairaice fuska yayi yace
"Baby ina zan sameshi bama lokacinsa bane fa"

Tashi tayi ta zauna ta fara tsotsan bayan hannunta, a dole tayi fushi, tashi yayi ya zauna shima ya jawota jikinshi, hab'arta ya d'ago yace
"Babyna ki fad'i wani abun wanda kika san bazan sha wuyan nima ba pls" murgud'a masa baki tayi tace
"Farar k'asa da yalo"

Ajiyar zuciya ya saki ya mata kiss a goshi sannan ya sauka bisa gadon yace
"zan fita yanzu na nimo miki, inna siya zan bama driver ya kawo miki domin yau ina da aiki sosai a office"

Bata ce masa kala ba ya shige toilet dan ya watsa ruwa, itama mik'ewa tayi tabi bayanshi, ta iske shi a bawo yana wanka zuwa tayi itama ta shige ciki, dole ya aje nashi wankan yayi mata sannan ya d'aura mata towel ta fito, Murmushi yayi yace
'Wannan unborn Baby ya sa Basma rikici, in da banyi mata wankan ba ta fara kuka' duk a zuciya yake wannan maganar.

Bayan ya idar da nashi wankan ya fito ya taddata ta sanya atamfa d'inkin riga da sket, tayi makeup kamar ba ita ba tayi kyau sosai, tsayawa yayi yana kallonta ta juyo fuska tana dariya tace
"Ya aka yi ne ka zuba min ido ko na sauya maka ne?" girgiza kai kawai yayi ya soma shiryawa, dama ta ciro masa kayan da zai sanya, k'ananun kaya ne da suit, zama yayi ta shirya shi, ta sanya masa riga da wando ta d'aure masa belt ta kuma yi sitokin d'insa, ya d'aura neck tie ta santa masa suit, turarukan sa ta shiga fesa masa har saida ya amshe yana fad'an

"Ya isa haka ko so kike ki k'arar mini Madam rikici"

Murgud'a baki tayi ta matsa ta d'auko gyalenta da hand bag, ta sanya takalmi mai tudu ta d'aura igiyan ta d'auke key motan Yaya Aryan tace
"Muje aikin ko"
Sakin baki yayi yana kallonta, murmushi ta sakar masa ta kanne masa ido d'aya tare da kama hannunsa tana jaaa, suka fito falo masu aikinta ta basu oder duk abinda take so suyi mata, kana ta cigaba da Jan hannunsa suka fice. Bud'e motan tayi ta zauna mazaunin driver bai iya furta komai ba ya shiga gefenta ya zauna ta sanya key ta tada mota ta fice abinta.

'YAR SHUGABAWhere stories live. Discover now