*'YAR SHUGABA*👑
_page_ *26.*
_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾Bayan sun kaishi asibiti likita ya duba shi, ya tabbatar musu da damuwa ce ta haifar masa da suma
"amma yanzu ya farfad'o, nayi masa alluran barci domin kwakwalwansa ya huta, zuwa anjima inya farka, komai zaiyi dai-dai insha Allah"Bayanin da likita yayiwa su Yaya Ahmad kenan sai ya wuce, zama suka yi suna ta zancen zuci, Yaya Ahmad, Yaya Naufal, da kuma Yaya Jamal sune suka kawo shi asibiti.
A can gidan kuma sun k'ara shiga damuwa fiye da damuwar rashin Basma, Dady ya shiga tunanin ina ya san Aryan, lallai fuskansa tayi masa kama da wanda ya sani da dad'ewa, amma ya kasa tuna komai, matsantawan da yayi ma kansa da tunani ne ya haifar masa da ciwon kai, dole ya yakice abin a ransa dan gudun matsala.
Awa biyu Yaya Aryan ya farka, sai dai bai iya furta koda kalma d'aya ba, idanun sa sun masa nauyi da kyar yake iya bud'esu a hankali ya rufe, hawaye mai zafi ya gangaro masa a kefen idonsa, Yaya Ahmad ya matsa kusa da gadon cikin sanyin murya da tausasa zuciya yace,
"Aryan kayi hak'uri duk kan tsanani yana tare da sauk'i, dan Allah ka sanyawa zuciyanka salama, insha Allah komai zaiyi dai-dai, ka rik'a Addu'a a zuciyanka zaka samu sassauci, yawan damuwa baida amfani domin zai rik'a cutar da lafiyanka"
A hankali ya bud'e idonsa, ya fud'e baki zai yi magana amma ya kasa, Yaya Ahmad ne ya dakatar dashi ya d'aga masa hannu yace
"karka furta komai, ni dai kayi amfani da shawaran dana baka". Haka suka cigaba da zama a Asibiti sai yamma lis likita ya sallame su. Suka wuce dashi gida tare da magungunansa, suka gaisheda Umma, kana suka yi musu sallama.Umma ta kawo masa abinci faten Irish da naman kaza a ciki, da kyar yaci kad'an kana ta zauna kusa dashi ta dafa kafad'ansa tace
"Aryan ya kake abu kamar ma tsatson musulmai ba, banji dad'in yanda kake nuna rashin tawakkalin da kake yi, koda nasan zuciya ba tada k'ashi, daman dalilin dawowarka kenan kazo kaga abin bak'in ciki, amma haka Allah ya rubuta, ni dai ina k'ara jan kunnenka ka cire Basma a ranka, kayi tawakkali da lamarin Allah yanda yazo maka, Basma dai da auren wani akanta dan haka ka cireta a rayuwanka, in dai baso kake ka sanyawa kanka wani ciwon ba, a kullun ina maka Addu'a Allah ya baka mata tagari mai tsoron Allah"
Aryan rungume Umma yayi ya soma kuka wiwi, yace
"Umma ina k'ok'arin cireta a rayuwata, abinda naji ne ya d'aga min hankali, yanda Shureym ya azabtar min da Basma, yayi mata mugun rik'o, Umma ba zan samu natsuwa ba har sai Basma ta dawo cikin koshin lafiya ta cigaba da rayuwan farin ciki kamar kowa yake yi, dan Allah ki yafemin Umma na, son Basma a jini na yake, cireta a zuciyata abu ne mai wahala, sai dai na miki alkawarin kiyayewa akan haka".Umma ta kwantar da Kansa bisa cinyarta, ta shiga lallashinsa har saida yayi shuru yana ajiyar zuciya.
*Makkah*
Basma ta sauka lafiya ta kama d'aki a hotel dake kusa da harami, wanka tayi ta kwanta domin ta huta, tunanin rayuwarta takeyi, hakanan taji gabanta na fad'uwa, Aryan ne ya fad'o mata a rai, hoton fuskansa ke mata yawo a cikin kwayar idonta, hawaye ne ya soma zarya a idonta, bata hanasu zuba ba domin hakan ne zaisa taji sanyi a ranta. Takai kusan rabin awa a cikin wannan yanayin daga bisani ta mik'e tayi shirin fita ta wuce cikin masallaci.*Nigeria*
An samu bayanai akan Basma ta shiga jirgin k'asar Etopia, sakamakon binciken da akayi a airport, haka Abba ya tura wasu domin dubata a can k'asar na Etopia. Abba ya sanya an sakaye Shureym a cikin wani d'aki dake cikin gidansa, za'a bashi abinci da komai na buk'ata, fita ne kawai bazai yi ba dan har masu tsaronsa aka aje, har sai anga basma. Safeena duniya tayi mata k'unci, kuma gaba d'aya dangin su Shureym sunk'i amincewa da ita, dole yasa tayi d'amaran komawa gidansu Adamawa, da tsohon cikinta gunin tausayi.
YOU ARE READING
'YAR SHUGABA
Romance*'Yar Shugaban k'asa ce* Queen Basma, ta hakimce a seat d'in baya ita kad'ai, sai Meena 'yar Governor Kaduna ce ita ke driving, sai Leema 'yar Sarkin Kano wacce take gefen Meena. K'aran wak'ar Music na Larabawa ke tashi a motan, dukkan su suna bin w...