*'YAR SHUGABA*👑
_page_ *18.*
_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾Bayi ta shiga ta gasa jikinta da ruwan zafi, domin duk jikin yayi mata tsami, bayan ta fito ta samu ta sanya kaya ta fice zuwa studio, photo ta d'auka aka wanke mata, fuskanta ta fito da kyau bakinta a kubbure, ta dawo gida. Rubutawa tayi a diary d'inta kamar yanda ta saba, kana ta koma ta ajiye shi a mazau ninsa, ta had'a tea tasha kana ta d'aura da pain relief tasha, saita bi lafiyan gado.
*Nigeria*
Gudu take tana ihu, Abba kawai take kira tana cewa
"wayyo Abba zai kasheni kazo ka taimake Ni, Momy na wai bakwa sona ne kuka bari zai kashe ni" a razane Abba ya farka daga barcin tare dayin Addu'a
*"A'uzu bi kalimatil lahit taammat min sharri ma kalak'a"* gumi ne ke tsatsowa a jikinsa, gaba d'aya hankalinsa ya tashi, jingina yayi jikin gado, Momy ta farka a barci saita ganshi zaune, tashi ta yi ta zauna, cikin muryan barci tace
"yallab'ai lafiya ka zauna cikin wannan Daren?" agogan dake manne a d'akin ta kalla, k'arfe biyu da rabi na dare, sharce zufa yayi ya dafe kansa cikin damuwa yace
"Hajiya Maryam wlh mugun mafarki nayi da Basma, hakan ya nuna kamar tana cikin Matsala" Momy ta gyara zamanta tace cikin natsuwa
"Abba wannan aikin shaid'an ne kawai, amma Basma bata cikin matsala, saboda munsan wa muka bama 'yar mu fa, kawai dai kila ka sanya ta a ranka ne saboda rashinta na tsayin lokaci da bata tare damu" ajiyar zuciya yayi yace
"a gaskiya jiki na ya bani Basma tana cikin damuwa, insha Allah gobe in Allah ya kaimu da sassafe zanje America dan ganin lafiyar ta" ajiyar zuciya Momy tayi tace
"Allah ya kaimu goben nima saina maka rakiya" murmushi kawai yayi ya tashi ya shiga bayi, alwala ya d'auro ya shiga jero sallan Nafila, itama Momy bata kwanta ba, tashi tayi itama tayi alwala tare da gabatar da nata Nafilan.*Washe gari*
Da misalin k'arfe Bakwai na safe su Abba sun gama shirin tafiya, Abba ya hana Momy tafiya yace tayi zamansa ba zai kwana ba shima, Yaya Naufal tare da muk'arrbansa suka wuce airport ba tare da b'ata lokaci ba, dama jirgin President na jiran zuwansu, shiga suka yi suka kama hanya sai America.
*America*
Basma na kwance a d'aki sai nishi take fitarwa da k'arfi, numfashinta na fita da kyar, ta rufa da bargo amma duk da haka bai hanata jin sanyi ba, sai kerma jikinta yake yi, zufa ne ya lullb'eta hawaye na fita a idonta, a wannan lokacin tana buk'atar tai mako.
President suna isa, aka turo motoci daga gidan shugaban k'asar America ya kwashe su, sun gaisa dashi kana suka ci abincin, shi Abba ya kasa cin komai drink kawai yasha, burinsa bai wuce yaga Basma ba, wayarsa ya ciro ya kira Shureym, bugu biyu ya d'auka cikin ladabi yace
"Abba ina kwana?" Abba ya amsa fuska sake yace"Shureym gani nazo k'asarku, ina gidan shugaban k'asa, kana ina kazo ka kaini gidanka, domin mu gaisa da Basma"
Ai bai k'arasa maganan ba jikinsa ya d'auki rawa, muryansa har tana sirk'ewa dan fargaba yace
"Abba naje wurin aiki gani bisa hanya zanzo""OK saika zo karka b'ata lokaci fa domin yau zan koma"
"to Abba, insha Allah gani bisa hanya". Sai suka kashe wayar.Ai jikin Shureym na rawa ya tafi gidanshi, ya kira Safeena ya shaida mata zuwan President, itama hankalinta ya tashi, yana isa ya shiga gidan a sukwane, ya samu Safeena a falo tana kai kawo, da sauri ya kama hannunta yace
"kije gidan k'awarki, anjima in sun tafi zan kiraki ki dawo" jiki na rawa ta fice a gidan, d'akin Basma ya nufa ya bubbuga k'ofar amma shuru, hankalinsa a tashe yace"Basma dan Allah ki bud'e, Abba ne ya zo zani na d'auko shi, dan Allah ki rufa min asiri zan gyara mistake d'in dana miki pls Basma, bari naje da sauri kinga ma kirana yakeyi" bai jira amsarta ba ya fice da sauri.

YOU ARE READING
'YAR SHUGABA
Romance*'Yar Shugaban k'asa ce* Queen Basma, ta hakimce a seat d'in baya ita kad'ai, sai Meena 'yar Governor Kaduna ce ita ke driving, sai Leema 'yar Sarkin Kano wacce take gefen Meena. K'aran wak'ar Music na Larabawa ke tashi a motan, dukkan su suna bin w...