*'YAR SHUGABA👑*
_page_ *36.*
_Na_
*_Rahma Kabir✍🏾_**Bayan Mako D'aya*
Aryan da Basma sun murmure sunyi kyau sun fara kumari, kwance suke bisa gado Aryan yace
"My Queen nan da Mako guda Insha Allah zamu je Makkah muyi Umara tare da Honey Moon, amma fa na yin Ibada, sannan Gobe Insha Allah zamuje Asibitoci domin in cika miki alkwarinki"
Kallonsa take cike da So da K'auna tace
"Myn Godiya nake Allah ya k'ara maka Bud'i na Alkhairi yasa kafi haka""Ameen My Pretty" sai ya rungumeta tare tayi mata sumba a goshinta. Daga nan kuma suka yi Addu'an barci, cikin minti goma Basma barci ya d'auketa. Shima ba dad'ewa barci ya kwashe shi.
Saura kwana Uku su tafi Makkah, suka zagaye dangi tare da yi musu Sallama, har Kano sunje sun kwana d'aya, suka je Kaduna ma suka kwana washe gari suka dawo Abuja, a gidan Abba suka yini kowa na farin ciki da sauyawan su, sunyi kyau da k'iba gwanin sha'awa, sai dare suka koma Gida.
Ranar da zasu tafi, harda su Momy suka yi musu rakiya, Basma har kuka tayi saboda kewar 'Yan uwanta. A cikin Jirgi Aryan ya rungumeta a jikinsa yana lalla shinta har barci ya d'auketa.
*MAKKAH*
Sun samu masauki a hotel d'in kusa da Harami, suka yi wanka a tare sannan suka ci Abinci, Basma ta shirya cikin jallabiya Brown mai ratsin fari a jiki babu kwalliya fuskarta amma tayi kyau, sannan ta shirya Aryan cikin doguwar jallabiya fara da farar hula, ta sanya masa turare, tana murmushi tace"My Aryan ina kishi ka fita domin gaskiya Mata karsu kallen min kai, dan ba k'aramin kyau kayi ba"
Murmushi ya sakar mata yace
"ai kema kinyi kyau sosai, ji yadda Jallabiyar ta amshi jikinki, nima gaskiya ina kishi dan haka Nik'af zaki sanya"Dariya ta sanya tace
"Nik'af? bazan iya numfashi a ciki ba Allah kuwa, ban tab'a d'aurawa ba, Ni koda nayi Islamiyya bana sayawa sai dai ina sanya Hijab har k'asa da safa, amma bana iya sanya Nik'af, kuma ai fuskata ba kwalliya"Dariya shima yayi yace
"Ai fuskarki ko ba kwalliya kyanki na nan, amma naji baza ki saka ba, sai dai zaki rik'a d'aure fuska kina bonewa"Dariya ta kyalkyale da shi ta fad'a jikinsa, rungumeta yayi kamar bazai sake ta ba sai da suka yi minti biyu a haka kana suka saki ajiyar zuciya a tare yace
"kin ga tashi mu wuce masallaci" Ba musu ta mik'e suka wuce masallaci.
Sun duk'ufa wajen yin Ibada da yiwa Allah Godiya bisa Ni'imomin da ya basu, sannan kuma da Addu'an Allah ya k'ara musu zaman lafiya acikin zamansu ya barsu tare har a Aljanna, ya saka wa iyayensu da gidansu Aljanna. Sun rokawa dukka nin Al'umma Musulmi da kuma samuwar zaman lafiya a K'asar mu Nigeria da dukkan Duniya gaba d'aya. Nima dai na taya su da "Ameen Ya Rabbi"
*Bayan Mako Guda*
Suka wuce *MADINAH* dan ziyaran Masallaci Monzon Allah S.A.W. Basma ta kira Hajiya Kaltum ta sanar mata da zuwansu, cikin farin ciki tace su tawo gidan ta. Anan suka samu masauki da kyakkyawan tarba.
Bayan sun natsa, Basma ta kwashe labatinta tas ta bata Hajiya Kaltum, ba k'aramin mamaki tayi ba da labarinta, tace
"Ashe Basma ke *YAR SHUGABA* Ce, lallai rauyuwa kenan, da ace da farko na rik'e ki da wulakanci da baza ki Ni meni ba, Naji dad'i sosai kuma Nagode" Nan dai suka cigaba da hira.
A masallaci suke kwana danyin Ibada. Satin su biyu a Madinah suka shirya dawowa Makkah, Basma Check d'in kud'i ta rubutawa Hajiya Kaltum masu yawa wanda ni kaina ban san yawansu ba, ta bata ta ciresu a bank, dan cigaba da kasuwancin ta, Hajiya Kaltum tayi mata Godiya harda kuka, kaya ta had'a ma Basma na gyaran jiki, ta kuma had'a mata da guzirin wasu kayan. Cikin farin ciki da kewar juna suka baro Madinah, shima Aryan ya yaba sosai da Mutuncin Hajiya Kaltum.
YOU ARE READING
'YAR SHUGABA
Romance*'Yar Shugaban k'asa ce* Queen Basma, ta hakimce a seat d'in baya ita kad'ai, sai Meena 'yar Governor Kaduna ce ita ke driving, sai Leema 'yar Sarkin Kano wacce take gefen Meena. K'aran wak'ar Music na Larabawa ke tashi a motan, dukkan su suna bin w...