*'YAR SHUGABA👑*
_page_ *40.*
*_Final page_*
_Na_
*_Rahma Kabir✍🏾_**Bayan Kammala Wankan Jego*
Basma ta gama wanka, zaune take tasha kwaliya cikin d'inkin riga da sket na atamfa, Baby Hydar yana gefenta ta kwantar dashi, wayarta ce a hannunta tana latsawa da alama charting take yi, Sallaman Yaya Aryan shine ya katseta ta d'ago cikin murmushi tare da kallon so ta amsa masa, isa yayi kusa da ita ya zauna tare da rausayar da kai gefe yace
"Babyna kinga yanda ki kayi kyau kuwa, kamar Baby Hydar bai fita a jikinki ba, meye sirrin?"
Murmushi tayi wanda ya bayyana farin cikin ta tace
"Myn bafa komai, Ni ce dai yanda ka sanni sai dai fa na samu kyakkyawan kulawa wurin Ammi dan haka ita zaka tambaya sirrin"
Hararan wasa yayi mata yace
"Kinsan dai babu wannan tsakanina da Ammi, a bakinki ya kamata naji komai, yanzu dai mu bar wannan maganar yaushe zaki dawo gidanmu, ina missing d'inki Baby love, da kyar nake iya barci fa" ya k'arasa maganar cikin muryar tausayi.Kanne masa ido d'aya tayi tace
"Uhum Myn nifa sai nayi wata biyu zan dawo"Ido ya zaro waje yama kasa magana, da gudu ta mik'e ta bar wurin tana kwasan dariya, girgiza kai yayi ya d'auki Baby Hydar yabi bayanta, d'akinta ya sameta ya kwanar da Baby Hydar ya matsa wurin ta yace
"Babyna ko so kike in shiga wani hali?"
D'ago fuska tayi tana kallonshi cikin ido tace
"Baby nima na kosa na dawo gareka amma bansan ya zanyi ba, bazan iya sanar wa Ammi hakan ba, ka k'ara hak'uri suma sunsan ya kamata na koma karka damu"Ajiyar zuciya ya saki tare da busa iska mai zafi yace
"ki shirya zanzo gobe Insha Allah zamu fita"Ido ta zaro waje tace
"ina zamu kuma Myn? kunya nakeji"Murmushi yayi yace
"Hotel zamu domin ina da buk'atar Babyna in ba so take in fara biye-biye ba"Da sauri ta had'e bakinta da nashi domin bata son ya k'arasa maganar, sai da suka d'auki minti goma kana ta janye jikinta tare da sauke ajiyar zuciya, cikin kasalan murya tace
"Myn karka k'ara furta kalman da ya fito a bikinka domin kanada ni, Insha Allah zan kasance da kai a koda yau ba zan gaji da kai ba tunda nima inda buk'atarka, zan shirya mu fita amma gidanmu zamu ba Hotel ba, domin in samar maka farin ciki sweet babyna" saita manna masa kiss a goshinsa ta mik'e, tana mai cewa
"bari na kawo maka abinci dan nasan da wiya in kaci na rana".
Bud"e k'ofar da zata yi ne taci karo da Ammi, Ammi tace"Ina zaki kike sauri haka?" Sosa k'eya tayi tace
"Abinci zan kawowa Yaya Aryan"
"Ok ga wannan ki shanye shi zuwa anjima da yamma" ta amsa goran tana godiya.*Bayan Sallan La'asar*
Ammi ta sameta a d'aki tace
"Basma je kiyi wa Momynki Sallama yau zaki koma gida, da fatan kin gama shirya kayanki?""Eh Ammi na kammala bayan Yaya Aryan ya tafi"
"To madalla" saita fita.Tana isa part d'in Momy ta sameta zaune saman kushim tana karanta wani Jarida, sallaman da tayi ne yasa ta aje Jaridar a gefe ta amsa mata, Basma ta isa gefenta ta zauna tare da kama hannunta tace
"Momyna sannu da hutawa"
"Yauwa My Basma"
"Nazo muyi sallama ne Ammi tace yau zan koma gida" ta k'arasa maganar cike da shagwab'a.Hararan wasa ta mata tace
"Basma sai yaushe zaki girma da yin shagwab'a ne?"

VOUS LISEZ
'YAR SHUGABA
Roman d'amour*'Yar Shugaban k'asa ce* Queen Basma, ta hakimce a seat d'in baya ita kad'ai, sai Meena 'yar Governor Kaduna ce ita ke driving, sai Leema 'yar Sarkin Kano wacce take gefen Meena. K'aran wak'ar Music na Larabawa ke tashi a motan, dukkan su suna bin w...