*'YAR SHUGABA*👑
_page_ *6.*
_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾Ya Ahmad saida ya bari sun kusa gida sai ya samu guri yayi parking, ya kalli Basma yace
"Basma ki gaya min me ya faru? dan bazani gida dake a haka ba" share hawayenta tayi ta fara bashi labarin duk abinda ya faru, bata ɓoya masa komai ba tun farkon haɗuwanta da Aryan, saida ta gama tsaf kana ya gyara zamansa ya fuskanceta da kyau yace"Basma gaskiya baki kyauta ba, domin ke kika ja komai ya faru, meyasa idonki zai rufe saboda samun duniya ki wulakanta Mutum, Allah da kanshi ya karrama ɗan Adam ya fifitamu akan Aljanu, Basma yanzu halittan Allah ya cancanci wulakanci? haba Basma ban san yaushe kika sauya halinki ba, kina taƙama da mulki da kuɗi ko, to wallahi Allah zai iya amshesu daga hannun mu ya bama wasu, ki sani wannan duniyar ba matabbata bace munzo cin kasuwa ne, duk kuma abinda muka shuka shi zamu girba a makomarmu, Basma na lura tunda kuka tafi England ke dasu Meena duk kuka sauya hali"
Jikin Basma ne yayi sanyi sosai, tabbas maganganun sa sun ratsata, cikin mutuwar jiki tace
"Yaya Ahmad wallahi yanzu hankalina ya dawo jikina tabbas ban kyauta masa ba, nagode daka tunatar dani da kayi, lallai na shagala da ruɗin duniya, Yaya Ahmad bansan me ya shiga kaina ba" saita ƙarasa maganar tana kuka, murmushi yayi yace
"Ai shi Allah mai gafara ne, inaso duk lokacin da kika ƙara haɗuwa dashi, to ki bashi haƙuri" tace
"to Yaya Ahmad insha Allah zanyi yanda kace" wannan karan dariya yayi har haƙoransa na fitowa yace
"yauwa ƙanwata farin cikina, yanzu bani labarin yanda kika ƙarasa a gidansu Khadija" murmushi tayi ta soma bashi labari, masha Allah yace, kana ya tada motan suka wuce gida suna hira cikin nishaɗi tamkar Basma batayi kuka ba.Yaya Aryan yana isa gida ya tadda Umma riƙe da kuɗi tana juyasu a hannunta, da sauri ya ƙarasa yace
"Umma wannan kuɗin fa? Khadija ta dawo kuwa? dan na zaga sosai ban ga mai kamarta ba, na tambaya ba wanda ya ganta" murmushi Umma tayi tace
"Khadija ta dawo yanzu ta shiga bayi, ashe wai wata Yarinya ce ta bigeta a mota suka kaita asibity" nan dai Umma ta labarta masa abinda ta sani, Yaya Aryan ya jinjina lamarin yace
"to Allah ya kyauta nagaba, yanzu duk wannan kuɗin su suka bada?"
"eh su suka bayar, harda siyayya ma suka yi mata na kayan ciye-ciye" kafin yayi magana Khadija ce ta fito daga wanka tace
"sannu da zuwa Yaya Aryan"
"yauwa Khadija" nan suka gaisa itama ta ƙara bashi labari, Umma ce ta miƙa masa kuɗin tace
"ga kuɗin saika gyara runfarka daga nan ka biya kuɗin haya, sauran kuɗin ka siya mana kayan abinci" Amsa yayi cikin natsuwa yace
"Allah ya saka da alkhairi, bari na fita in duba Muntari kafinta sai mu fara maganar gyaran"
"to Aryan saika dawo, Allah ya muku albarka" duk suka amsa da "Ameen" kana ya fice.Bayan sallan Magrib jirginsu Prince Shureym ya iso, yana sauka a jirgi motoci na jiransa, ya ƙarasa su tafi gidan president.
Bayan sun kai ya wuce falon shugaban ƙasa ya gaisheshi, kana ya wuce part ɗin Ammi ya gaisheta, ya shiga wurin Momy itama ya gaisheta, saiya wuce part ɗinsu Yaya Ahmad can ne masaukinsa, yana shiga falon sai ya faɗa wani ɗaki, wanka yayi ya kimtsa saiya gabatar da sallan Magrib, yana idarwa aka kira sallan isha'i, ya tashi ya gabatar, sai da ya kammala gaba ɗaya, kana ya tashi ya fita falon ya zauna, TV ya kunna sannan ya ɗauki wayarsa ya kira Safeena hira suka shiga yi na kewar junansu.
Ɓangaren Basma kuwa, ta sanya aka kawo masa abinci aka jera a kan kafet dake tsakiyar falon, wanka tayi ta sanya doguwar riga na leshi, tayi ɗaurin Maryam Babangida, tayi kyau matuƙa sai ƙamshi takeyi.
Basma doguwa ce kaɗan tanada ƙiba shima kaɗan, sai fatarta akwai ɗan duhu mai haɗe da haske, ita ba baka ba ita ba fara ba, tsaka tsaki, sai kuma tana da Boobs dai-dai da jikinta maca ce mai hips sosai, mazaunanta yayi dai-dai da jikinta, cikinta a ɗame yake tamkar bata cin abinci, Basma akwai shape mai kyau da diri. Fuskarta ɗauke yake da dara daran idanu, bakinta ɗan ƙarami ne pink color, sai dogon hanci da yayi tsini har baka, in tayi dariya dimple ɗinta sai ya lotsa, gashin giranta tamkar anyi mata kabin, Basma tanada yalwataccen gashi har gadon baya, mai silɓi da baƙi sosai, Basma ta haɗu domin ko ba makeup fuskarta a haɗe take, Allah ya gama halitta anan. A fili in ka ganta za kayi zaton za tayi nauyi amma ana ɗaukarta shagwal take, kyau dai ta haɗa na Barebari da kuma Fulani. Masu karatu ya kuka hango kyawun Basma, abin ba acewa komai lol😃.
YOU ARE READING
'YAR SHUGABA
Romance*'Yar Shugaban k'asa ce* Queen Basma, ta hakimce a seat d'in baya ita kad'ai, sai Meena 'yar Governor Kaduna ce ita ke driving, sai Leema 'yar Sarkin Kano wacce take gefen Meena. K'aran wak'ar Music na Larabawa ke tashi a motan, dukkan su suna bin w...