*'YAR SHUGABA👑*
_page_ *33.*
_Na_
*_Rahma Kabir✍🏾_*Sun fara shirye-shiryen biki ba kama hannun yaro, Musamman Ummi ta kira wata 'yar Uwarsu daga Maiduguri tazo gyara Basma, an tsumata da turaruka sosai da dilka, dasu kayan k'arin ni'ima, Basma ta k'ara kyau sosai duk in da ta gifta k'amshi ke tashi, in ko ta zauna a wuri sai yayi damshi, an gyara mata sumanta ya k'ara bak'i, silb'i da shek'i yayi kyau sosai.
Ammi da Hajiya Murja sune suka tafi Dubai had'o kayan lefen Basma. Akwati dozin guda sha biyu tank'ame da kaya, Ango ma anyi masa nashi akwati biyar cike da kaya.
Yaya Aryan yana ta shirye-shirye, Yaya Ahmad shima ba baya ba tare suke aiwatar da komai. Dady yasa an gyara gidan da Basma zata zauna, komai sabo aka sanya a gidan. Sweeping pool d'in an sauya ruwan ciki, lanbun gidan an gyara shi sai k'amshi ke tashi.
*Biki saura kwana uku*
Gida ya gama cika da dangi, taron Mutane yafi ko wani taron biki da akayi a baya, Mutanan Kano, Kaduna, Gombe, Maiduguri duk sun hallara a gidan shugaban k'asa, ko wanne ya samu masauki.
Hajiya Kaka da Inna suka sanya Basma a gaba suna mata Nasiha, Basma sai kuka take yi, Kaka tace
"Basma, Aryan Yaro ne mai hak'uri dole sai kin ajiye rashin kunya da tsiwan ki in ba haka ba zaki rik'a shiga hakk'insa"
Nan dai su kaita mata, tashi tayi ta mik'e cikin shagob'a tace
"Ni kun tasani a gaba sai mita kuke min, ai shima ya kamata ku kira shi kuyi masa fad'an, ni kunga tafiya ta"
Kaka tace
"kinga ja'ira ko, saina sanya shi ya tsafala min ke mara kunya kawai tafi ki bamu wuri"Inna tace
"Hajiya bar Yaran yauzu, wataran nan zata zo wurin ki niman tai mako"Basma tace
"Allah ya kyauta" ta fice abinta tana dariya.*Ana Gobe Biki*
K'ayataccen walima suka had'a Maza da Mata a wani k'aton hol, aka kira wani Babban Malami yazo ya bada fatawa akan zamantakewar Aure.
Matan *Siirrin 'ya Mace* sun hallara, haka ma matan *'Yar Shugaba Fan's* sun hallara, Matan group d'in *Khaleesat Haydar Facebook* suma sun zo, matan group d'in *M Khady Fan's* suma sun iso, *QueenMamu novel group* suma sun iso, *real maidanbu novel group* suma sun halarto, *S.I Kaduna Fan's club* suma suna wurin, *Sophy an vc novel* duk suma sun iso.
Wuri ya cika ya batse da mutane kowa ka ganshi yana cikin farin ciki, Amarya ta sanya wani material mai kyau da tsada ta d'aura alkebba a sama, haka ma Ango yasha farin yadi mai kyau ya sanya alkebba a sama. Wuri d'aya suka zauna, wurin yasha decoration, Anci ansha taro yayi dad'i da armashi. Sai misalin Sallan Magrib taron ya watse kowa ya koma gida.
Amarya suna hanyar dawowa, zaune suke seat d'in Baya, Yaya Aryan ya matsa kusa da ita ya leka cikin fuskarta, runtse ido tayi alaman jin kunya, cikin murya mai dad'i yace
"Insha Allah gobe In Allah ya kaimu, uwar haka kin zama tawa ni kad'ai"
Murmushi tayi ta bud'e ido sai ya sauka akan nashi, ido d'aya ya kashe mata, sai ta rufe fuska da hannayenta tana dariya, k'unshin da aka mata a hannu ya kurawa ido kamar zai leshe su, dan sunyi masa matuk'ar kyau, cikin kasalan jiki ya kai hannunsa kan zanan, ya shiga binsu a hankali, nan take jikin Basma yayi sanyi kasala ya diran mata, cikin sauri ta cire hannun a fuskanta ta duk'un-k'une su cikin alkebbanta, murmushi yayi mai sauti.
Kansa ne yaji ya rasa masa, runtse ido yayi ya bud'e idonsa sunyi ja, janye jikinsa yayi gefe ya d'aura bayansa jikin kujera, runtse idonsa yayi yana ambaton Allah a zuciyansa, a hankali ya fara samun natsuwa, tunani ya shiga yi
"me yasa nake jin irin hakan kwana biyun nan?" basarwa yayi ya jawo wayansa ya nima wayar Yaya Ahamd suka fara magana akan hidimar biki.

CZYTASZ
'YAR SHUGABA
Romans*'Yar Shugaban k'asa ce* Queen Basma, ta hakimce a seat d'in baya ita kad'ai, sai Meena 'yar Governor Kaduna ce ita ke driving, sai Leema 'yar Sarkin Kano wacce take gefen Meena. K'aran wak'ar Music na Larabawa ke tashi a motan, dukkan su suna bin w...