*'YAR SHUGABA*👑
_page_ *8.*
_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾*Bayan mako guda*
Yaya Aryan yanata zuba ido yaga zuwan Basma amma shuru, wani lokacin har tashi yake a kasuwa da wuri domin yazo ko zasu had'u, cikin da bara yake tambayan su Umma akan Basma tazo? sai suce bata zoba, wasa-wasa har aka shafe sati d'aya, sai rashin zuwan nata ya fara sa shi damuwa, Addu'a yake Allah yasa lafiya.
Ta b'angaren Basma kula kalau take, domin a cikin satin Yaya Shureym yazo, sun sha soyayya shiyasa bata samun lokaci sosai ba na zuwa gidansu Deeja, domin kullun yamma suna fita da Yaya Shureym dasu Na'im, sai Magrib suke dawowa.
Hakan yasa bata samu damar zuwa ba, amma fa tana tunaninsu da kewar Umma sosai, ta d'auki aniyar siyan musu waya, in bata samu zuwa ba ta rik'a kirasu.
Yau ya kama ranar Juma'a, bayan Sallan La'asar Basma da Yaya Ahmad suka shirya zuwa gidansu Deeja, Basma tayi shigan lafaya mai kalan fari da green, Yaya Ahmad kuma ya sanya sky blue na shadda hula bak'in dara da takalmi bak'i, sunyi kyau sosai. suka kama hanya suka tafi a mota ba tare da escot ba, hira suke cikin nishad'i tare da kwanciyar hankali, a haka suka isa gidan.
Bayan sun isa Basma, ta fito tace
"Yaya bari na gaya musu tukunna saika shigo" ya kalle ta da murmushi yace
"ba damuwa ina jira".Cikin natsuwa ta Shiga gidan, duk kan su suka amsa, cike da fara'a Umma ta tarbeta, Deeja kuwa tasowa tayi ta amshi jakan hannunta tana mata sannu, Yaya Aryan kuwa basar da ita yayi tamkar bai ganeta ba, Amma fa a zuciyansa yana yaba kyawun da tayi, dauriya kawai yayi ya matse, zama tayi a kan tafarma sai da suka gaisa da Umma kana suka gaisa da Deeja, ta kai kallonta wajen Yaya Aryan tace
"ina yini Yaya Aryan?" farin cikin ne ya mamaye zuciyansa jin yanda ta kira sunansa yayi masa matuk'ar dad'i, a fili kuma ya amsa fuska ba yabo ba fallasa a dak'ile, daga nan bata k'ara cewa komai ba domin jikinta yayi sanyi yanda taga ya amsa mata, sai duk ta jita a takure, Waigawa tayi wurin Umma tace
"da Yaya Ahmad muke yana waje, nace bari na sanar muku kafin ya shigo" Umma ta fad'ad'a fara'an fuskanta tace
"Allah Sarki ai da ya shigo tunda duk gida ne, Kai Aryan tashi ka shigo dashi" da sauri ya mik'e ya fita, cikin minti uku saiga su sun shigo, ya zauna a tabarman da Yaya Aryan ke zaune shima ya zauna gefensa, cikin natsuwa ya gaida Umma, ta amsa cike da farin ciki, Deeja ne ta fito daga d'aki sanye da gyale ta kawo masa ruwan pure water a cikin plet ta aje a gabansa, sannan ta gaishe shi, cikin kulawa ta amsa, Basma na satan kallonshi, taga sai wani kallon Deeja yake kamar zai had'iyeta, ita ko Deeja batasan yana yiba, nan ya shiga yiwa su Umma bayanin zuwansa, yace"Umma kan zancen makarantar Deeja ce, insha Allah ranar Monday zasuje tare da Basma tayi mata registration, saboda yanzu ana farkon fara d'aukan sabbin dalibai, sannan kuma na d'auki Aryan zai yi aiki a company Abbanmu, In ba damuwa"
Aryan cikin natsuwa yace
"Ayi haka kuwa? wannan dawai niya ai zata yi yawa, ga Deeja ga kuma ni" murmushi Yaya Ahmad yayi yace
"d'an uwa karma damu duk yiwa kaine" Aryan yace
mun gode Allah ya saka da Alkhairi" Umma ma godiya tayi harda yan kwallanta, Deeja ko murna ne kan murna, itama godiya tayi.Nan fa hira ya b'arke sunata zan tawa, Amma fa banda Basma data takure, saboda irin nuna ko in kula da Yaya Aryan yayi mata, bayan minti talatin da zuwansu, Yaya Ahmad yace zai je wani wuri inya dawo zaizo ya d'auki Basma, nan yayi musu sallama Yaya Aryan ya rakashi waje, Basma ne ta juyo wurin Deeja tace
"saiki shirya ranar Monday da wuri zanzo domin mu tafi makarantan, ina so mu gama registration a ranar ne" cikin farin ciki tace
"insha Allah tun Asuba zan tashi na shirya da wuri" Umma tace
"da dai ya fi miki da wannan shegen barcin asaran da kike yi, to yanzu ga makaranta nan saiki cigaba da barcin mu gani" duk suka sanya dariya, Yaya Aryan ne ya shigo yace
"Umma wai ina furan ne? wallahi yunwa nakeji" da sauri tace
"af kaga na manta, da an dama Ahmad yasha kan ya tafi, ke Deeja d'auko min kwanan furan nan da kuma kindirmo had'e da sugar" taje ta d'auko, nan Umma ta dama fura da nono da yawa, ta fara zubawa Basma a cup ta aje a gabanta, sannan sauran ta zuba musu.
YOU ARE READING
'YAR SHUGABA
Romance*'Yar Shugaban k'asa ce* Queen Basma, ta hakimce a seat d'in baya ita kad'ai, sai Meena 'yar Governor Kaduna ce ita ke driving, sai Leema 'yar Sarkin Kano wacce take gefen Meena. K'aran wak'ar Music na Larabawa ke tashi a motan, dukkan su suna bin w...