*'YAR SHUGABA👑*
_page_ *35.*
_Na_
*_Rahma Kabir✍🏾_**Washe Gari*
Da k'arfe bakwai na safe Yaya Ahmad ya kama hanyar gidan Yaya Aryan. Yana isa yayi hon Mai Gadi ya bud'e masa Gate, yayi parking ya isa bakin k'ofar falon yayi nocking, Yaya Aryan dake kwance a kan doguwar kujera ya mik'e cikin nauyin jiki ya isa bakin k'ofan ya bud'e, sai yayi arba da Yaya Ahmad, sai da gaban Aryan ya fad'i, matsa masa yayi ya shigo cikin falon duk suka samu guri suka zauna, sai suka gaisa, Yaya Ahmad yace
"Ina Basma fa?"
Yaya Aryan yace
"tana d'aki, lafiya na ganka da sassafe haka?""Lafiya lau, nazo nayi magana daku ne, dan haka kira min Basma tazo"
Bai ce komai ba ya mik'e ya isa bakin k'ofar Basma, sai ya ki shiga ya tsaya bakin k'ofar yana bugawa tare da cewa
"Basma, Basma ki tashi ga Yaya Ahmad yazo"Cikin magagin barci ta farka ta mik'e tare da bud'e murya yace "to".
Yaya Ahmad duk yana kallonshi, a ranshi yace
'ko me ya hanashi shiga d'akin oho' Yaya Aryan ya dawo ya zauna.Basma ta fito sanye cikin doguwar riga ta yane gyale a kanta, zama tayi a one seater ta gaishe da Yaya Ahmad ya amsa cikin kulawa, shuru ne ya biyo baya na tsayin minti Uku, daga bisani Yaya Ahmad yace
"Aryan, Basma nazo domin muyi magana ne, a gaskiya ban yarda da bayanin da kuka min ba jiya, shiyasa na zo Yau dan jiya na kasa barci, Dan Allah karku b'oye min komai"
Basma da Aryan suka kalli juna suka had'a ido, Basma zata yi magana Aryan ya riga ta yace
"ka yarda da abinda muka ce maka mana domin ba komai"
Yaya Ahmad yayi murmushin k'arfin hali yace
"Basma in shi ba zai gaya min ba ke nasan ba zaki b'oye min ba, dan haka gaya min me yake faru?"Hawaye ne ya soma zarya a idon Basma, ta d'ago ta kalli Yaya Aryan, sai ya fara gir giza mata kai alamar karta gaya, Yaya Ahmad ya kira sunanta sai ta mai da kallonta gare shi yace
"Basma ina jinki"
Basma ta share hawayenta ta gaya wa Yaya Ahmad abinda ke damun Aryan, sai dai bata gaya mishi matsalan da suke fuskanta ba yayin saduwa sai ta boye wannan.
Yaya Ahmad ya kurawa Aryan ido sai ya sun kuyar da kai zuciyarsa na masa zafi, nan take idonsa suka yi ja. Yaya Ahmad yace
"Basma d'auko key d'in motanki ki shirya ki tafi gida"
Da sauri duk suka zuba masa ido, d'aure fuska yayi yace
"Nace ki tashi kiyi abinda na sanya ki" ya fad'a maganar cikin tsawa, jikinta na rawa ta mik'e tare da fashewa da kuka.Aryan mik'ewa yayi cikin fushi yace
"Me kake nufi da ta tafi gida ba tare da izini na ba?"Murmushi yayi yace
"Saboda ba kada lafiya, ba zata zauna ba domin tabbas matsalan ka zai iya shafanta" yaya Ahmad ya fad'i hakan ne domin ya tunzura Aryan dan ya tabbatar da ciwon nasa. Aiko Aryan ransa ya k'ara baci.Basma sai gata ta fito tana ta kuka, Yaya Aryan ya tare mata hanya ya kama hannunta gam, kansa ne yayi mugun sarawa sai ya rik'e Kan da d'ayan hannunsa, Basma tace
"Yaya Aryan ka barni na tafi ko zaka ji sauk'in abinda ke damunka"
Yaya Ahmad ne ya matso wurin ya fintsike hannun Basma, ya kama Aryan ya zaunar dashi tare da kama kansa da k'arfi, Addu'a ya fara tofa masa nan take ya ture Yaya Ahmad suka fara dambe. Basma ihu ta soma security da suke gidan suka fad'o falon a sukwane suka kama Yaya Aryan yana cijewa.
STAI LEGGENDO
'YAR SHUGABA
Storie d'amore*'Yar Shugaban k'asa ce* Queen Basma, ta hakimce a seat d'in baya ita kad'ai, sai Meena 'yar Governor Kaduna ce ita ke driving, sai Leema 'yar Sarkin Kano wacce take gefen Meena. K'aran wak'ar Music na Larabawa ke tashi a motan, dukkan su suna bin w...