11

1.1K 68 0
                                    

*'YAR SHUGABA*👑

_page_ *11.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

Yaya Ahmad yace
"Basma auren ki da Shureym dole za'ayi shi, tunda iyaye sun riga sunyi magana, kuma da an d'aura shikenan zai daina wannan iskancin nashi" hawaye ne ya sauka a kuncinta tace
"Yaya Ahmad bana fatan auren Yaya Shureym ni ina da wanda nake so, kuma in ba a bani shima wlh Yaya zaku rasani, domin zan mutu" a razane ya kalleta yace
"Basma kina da hankali kuwa? waye kike So haka? waye shi kuma d'an gidan waye?" Cikin kuka tace
"ni Yaya Aryan nake so, kuma in ban aureshi ba zan iya mutuwa" a razane Yaya Ahmad ya mik'e tsaye yace cikin kad'uwa,

"a'a Basma, a'a Basma, karki ce za kiyi sanadin rabuwar family d'inmu, kinsan yanda Shureym yake a wajenmu, yaron Yayan Ammi ne, karki ce za kiyiwa Ammi haka, plss ki d'auka mafarki kike da sanin Aryan, ki gaggauta cire Aryan  a ranki" a razane ta d'ago ta mik'e tsaye tace
"Yaya Ahmad bazan iya ba, wlh Yaya Aryan nake so" da gudu ta fita daga d'akin tana kuka, lanbun gidan ta nufa taje ta zauna, kuka take kamar ranta zai fita ba tare da sauti sosai ba, Yaya Ahmad cikin sauri ya isketa a gun, dan yasan tabbas ba zata koma part d'in Ammi ba a haka, zama yayi gefenta ya kama hannunta shima a zuciyarta yana gasgata lallai Basma da Aryan ta dace, domin Mutumin kirki ne ga Addini da sanin yakama, a d'an zaman da yayi dashi baiga wani aibu a gunsa ba, sai dai matsala d'aya ne, su Ammi ba zasu yarda Basma ta kawo wani Mijin ba, sai Shureym, sannan kuma Aryan ba d'an kowa bane shi, baya tunanin su Ammi zasu yarda ta auri talaka.

Yace
"Basma nima ina son ki auri Aryan, amma kin san hakan bazai yuwuba a wurin su Ammi" cikin kuka tace
"Yaya zai wuyu tunda ina sonsa, kai zaka taimaka na aureshi kamar yanda zan taimaka maka ka auri Deeja" nisawa yayi yace
"karki damu zanyi wani Abu a kai, ki bani lokaci" sassauta kukan tayi ta share hawayenta tace
"Nagode Yaya Ahmad, Allah ya mana jagora"
"Ameen" yace, kana ya rakata part d'in Ammi ya koma d'akinsu cike da tunani barkatai, da damuwa fal zuciyansa. Lallai yana tausayin Basma kuma yana sonta fiye da kansa. dole yayi k'ok'arin sama mata mafita, da wannan tunanin har barci ya kwashe shi.

*Bayan kwana biyu* Basma sun cigaba da soyayyansu, wanda a yanzu basa b'oyeta ko a gaban waye, Umma ta kad'u sosai data fahimci haka, kiran Yaya Aryan tayi, ta masa fad'a akan yabi a hankali Basma ba tsaran aurensa bane, dole ya iya takunsa, hankalin Aryan ya tashi yace
"Umma wlh ina son Basma ki mana addua, domin Addu'anki yana da matuk'ar tasiri a garemu" Umma tayi ajiyar zuciya, ta sanya musu Albarka, can kasan zuciyarta tana tausayawa yaranta, domin tasan iyayansu Basma ba zasu yarda da auren su Deeja ba, saboda su d'in ba kowa bane, talaka ne futuk.

Haka Yaya Shureym ya k'araci zama a gidansu Basma bai samu fuska a gunta ba, ko ya kirata bata d'agawa, haka ya tattara ya koma Kano.

*To bari na waiwayi wajensu Leema da Meena.*

Leema tana kano a takure take, domin bata samun sakewa sosai kullun tana gida, in zata fita saida kuyangi da dogarai, hakan yasa taji duk zaman Kano ya gundureta, ta fata tunanin komawa Abuja, in sha'awarta ta motsa kamar za tayi hauka, wataran a sace take fita tayi b'adda kama taje su had'u da Jalal, su gama shek'e ayarsu ta dawo gida a gau-gauce. A daddafe ta iya kaiwa har wata hud'u a Kano, yanzu ta gama shirya kayanta da yawa domin komawa Abuja, in kuma ta koma bata tunanin dawowa, sai dai ta rik'a zuwa tana gaishe da iyayenta.

Haka ma b'angaren Meena, Alhaji Ibrahim mahaifinta mutum ne mai sanya ido sosai kan yaransa, hakan ne yasa Meena bata fita saida dalili mai k'arfi, Yaya Jamal ya sanya mata ido shima domin yaga take-takenta akwai rawar kai, Meena in son shan syrup ya motsa mata, rufe kanta take yi a d'aki taita kuka tana buk'atar abinda zata sha, dakyar barci ke d'aukanta, in ta farka shikenan ta dawo dai-dai, hakan yasa ta samu wani shed'ani d'an unguwarsu, suka tsadance yana siyo mata syrup a sace ya kawo mata, sai ta bashi kud'i mai yawa, haka zatai ta maneji dashi harya k'are, gaba d'aya zaman Kaduna ya gundureta, saita soma had'a kaya dan komawa Abuja gaba d'aya, ita sam ba zata zauna a Kaduna ba, waya sukayi da Leema, suka gayawa juna matsalansu, nan take suka yanke shawaran barin gidan iyayensu a gobe in Allah ya kaimu, domin ci gaba da rayuwan freedom da suka fara a England.

'YAR SHUGABAWhere stories live. Discover now