*'YAR SHUGABA👑*
_page_ *34.*
_Na_
*_Rahma Kabir✍🏾_**Bayan Sallan Isha'i*
Su Yaya Ahmad sun kawo Ango Aryan, tunda suka shigo gabansa ke fad'uwa ya rasa natsuwan sa, nan su Yaya Ahmad suka yi musu d'an tunatarwa game da aure sannan suka yi musu sallama, da kyar Basma ta saki Meena sai kuka take yi, haka suka tafi tare da yi mata sallama. Yaya Aryan ya rakasu har mota saida yaga wuce wansu kana ya koma cikin falo ya zauna ya cire hulan kansa yana fifita dashi domin duk sanyin AC dake d'akin gumi yake yi, maida hulan yayi ya mik'e ya nufi d'akinsa, ruwa ya watsa tare da d'auro alwala ya sanya farar jallabiya ya fito falo, ya shiga kitchen ya d'auki plet tare da cups, hannunsa rik'e da ledoji ya nufi d'akin Basma.
Ya sameta zaune gefen gado fuskarta rufe da mayafi, zama yayi kusa da ita yaji kansa ya sara d'aurewa yayi ya yaye mayafin, d'ago fuskarta yayi cikin murya k'asa-k'asa yace
"Amaryata kinsha k'amshi, anya zaki rik'a barina ina fita kuwa? dan k'amshin ki kawai zai rik'a riki tani in kasa fita".
Murmushi tayi tace
"anya kuwa myn?"Murmushi yayi shima yace
"Eh mana, tashi ki d'auro Alwala muyi Sallah"Cikin murmushi tace
"ina da alwala ban dad'e da idar da Sallan Isha'i ba""ok tashi ki mu gabatar da Nafila" ba musu ta mik'e.
Sun idar da Sallan Nafila Raka'a biyu ya kama kanta ya mata Addu'a'o'i, kana suka yi Addu'a gaba d'aya suka shafa, kayan ciye-ciye ya zuba a plet d'in sannan ya zuba mata yoghurt a cup ya kai bakinta kamar ba zata amsa ba, ta bud'e bakin a hankali tana sha, haka ya ciyar da ita komai da hannunsa har sai da ta ce ta koshi kana ya rabu da ita yaci nashi.
Bayan sun kammala ya kwashe kayan ya maida kitchen ya rufe ya koma d'akin ya tadda Basma ta sauya kayan barci ta kuma shiga bayi ta wanke baki, kwanciya tayi akan gadon taja bargo tana dariya k'asa-k'asa tace
"Myn saida safe"
Murmushi yayi yace
"ok Allah ya tashe mu lafiya" sai ya zauna gefen gadon ya dafe kansa, tunani iri-iri yake yi amma ya gaza sanin ina hankalinsa ya dosa, jallabiyansa ya cire ya za gaya d'ayan side d'in gadon ya kwanta, kansa yana ta sarawa d'auriya kawai yake yi, cikin k'ank'anin lokaci idonsa yayi jaaa, hakanan tsoro yaji ya diran masa, Addu'a ya shiga yi dan neman yardan Allah, cikin lokaci kad'an ya samu rangwame ga yanda yake ji.Jawo Basma yayi tana k'ok'arin zillewa ya d'aurata bisa kirjinshi, gam ya rik'eta suna jin bugun zuciyan juna, cikin rad'a yace mata a kunne
"Rashinki yasa dare ya zame min rana bana iya barci, na shiga k'unci da damuwa, ya zanyi in misalta miki Son da nake miki ki fahimci zuciyana, my Queen kin zama b'angare na jikina bazan iya rayuwa ba ke ba"
Hawaye mai zafi yana fita a idonsa kansa nayi masa tsananin ciwo, Basma ta d'ago kanta tana kallon fuskansa, cikin kasala da damuwa tace
"Myn ka daina min asaran hawayenka, wannan ranar muke jira tazo, dan haka farin cikinka nake so ka nuna min a yau da mai cike da so da k'auna".
Hawayensa ta goge masa, rungumeta yayi tsam ajikinsa tare da sakin ajiyar zuciya. Daga nan kuma salon ya sauya, suka lula duniyar masoya, soyayya suke nunawa juna mara misaltuwa, sun gama kamuwa sosai, Aryan yana k'ok'arin kai ga biyan buk'atansa jikinsa ya soma rawa, nan da nan zazzab'i ya diran masa kansa yayi zafi kamar wuta nan take kwayan idonsa ya sauya kala yayi jaa kamar garwashin wuta, cike da tashin hankali ya ja jikinsa yana haki, Basma ta kamo hannunsa domin ta kama kamuwa dan maganin da tasha suna matuk'ar aiki a jikinta, fincike hannunsa yayi da k'arfi ya mik'e jallabiyansa ya maida ya koma gefen gadon ya zauna tare da dafe kai.

YOU ARE READING
'YAR SHUGABA
Romance*'Yar Shugaban k'asa ce* Queen Basma, ta hakimce a seat d'in baya ita kad'ai, sai Meena 'yar Governor Kaduna ce ita ke driving, sai Leema 'yar Sarkin Kano wacce take gefen Meena. K'aran wak'ar Music na Larabawa ke tashi a motan, dukkan su suna bin w...