1⃣

9.6K 528 25
                                    


                        💕*HIKMAH*💕
                                  1⃣

✍️SHATUUU

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

😍Shatuuu095@wattpad.....show some love 💕

*Hey lovelies..... HIKMAH is here, lemme know your opinions about it*


October 1995

"Lokuta da dama Allah yakan rufe mana wata kofar saboda ya bude mana wata kofa, Aminu me yasa bazaku manta da wannan rashin haihuwan ba ku rungumi kaddara? Komai na rayuwa MUKKADARI NE "

Wani mugun kallo Wanda aka Kira da Aminun Yayi, yana Sanye cikin Grey suit, wadda ta Kawata farar fatarshi, kana kallonshi kaga Wanda yake cikakken Dan Boko me akida, Dan gayu Wanda rayuwa tayi musu Afuwa, yace

"Kasan dalilin da yasa na fada maka plan dina? Saboda you are more than a friend to me! Amma Meye zaka dinga Wasu maganganu, seda nayi tambaya abinnan ba Haramun bane ko? Habibu Baka San ciwon Infertility ba, especially idan problem din daga gurinka yake, bazaka gane kuncin da zuciyata ke "

Zama Habibun Ya gyara bayan Ya rage volume dim TV dake parlon, inda ake Watso labarai daga AIT channel, the discussion is getting hot! Habibun ya furta a sanyaye kafin yace

"Bansan ciwon rashin haihuwa ba, amma inajin a jikina it's a painful thing, Abu daya nake son ka gane Aminu, Allah kadai yasan dalilin hanaku haihuwa, may be babu alkhairi a ciki"

Wani tsaki Aminu Ya saki tareda fadin

"See you! Ta Ina 'Ya'ya suke zama matsala, bantaba ji ba Habibu, its final jibi jirginmu zai tashi zuwa Germany"

Kai Habibu Ya girgiza Don yafi kowa sanin kafiya da kuma akida irin ta Aminu amma Yaya Zaiyi? Hakan yasa yace

"All the best aboki, to kui adopting mana"

Kai ya girgiza yace

"No! "

Handshake sukai daidai shigowar Lubabatu matar Habibu, cikeda faraa ta karaso sitting room din inda ta zauna gefen mijinta Wanda Tun shigowarta dukkan hankalinshi ya koma kanta.

"Tsoka daya a miya! Uwargida ran gida, kiyi yadda kikeso matar Habibu!"

Ta rigada ta saba jin kirarin Aminu akanta, shiyasa take sonshi a abokan mijinta, Har cikin zuciyata kirarin ke kaiwa, Murmushi ta saki tareda kwantar da kanta kafadar Habibu Wanda yake kallon yadda farinciki ke kwance fuskarta tace

"Barka da zuwa Aminu, irin zuwa babu sanarwa Haka? "

Dan Murmushi Aminun Yayi yace

"Ki Bari kawai, gidan Yayi Shiru Ina Yaran suke "

Wannan Karon Habibu ne yace

"Suna can gurin grannies dinsu, we need a break, ko ba Haka ba darling? "

Ya fada yana kashewa Lubabatu ido tareda sake matso ta da jikinshi. Tsaki Aminu Ya saki tareda fadin

"Allah Ya sawwake muku, I wonder yadda zan dauki Dana na kaishi Hutu wani gurin, that's impossible I guess! Kukansu ma Rahama ne! "

Cikeda tausayawa Lubabatu tace

"Ayya, lokaci ne Aminu, a jikina inajin zaku haihu Kasan Allah is the perfect planner, Ku cigaba da addua"

Take fuskar Aminu Ta kara liting da wani murmushin, tabbas duk duniyar nan yana girmama Wanda zaice Yana da hope akan zasu haihu, shima kanshi yana ji a jikinshi zai haihu to amma he can't wait anymore, yana bukatar jin kukan jariri Ko jaririya a gidanshi.

HIKMAH Where stories live. Discover now