2⃣3⃣

2.1K 248 12
                                    

Tunda na fito naji gaba na yana faduwa dan bansan me zan tarar gidan Hamma Mussadiq ba, Dan tabbas nasan akwai abinda ya faru Babba, idan ba Haka ba ta Yaya Anty Fadila zatayi kwanaki sama da Arbain bata neme ni ba? Ba kuma tazo gidanmu ba. Haka na cigaba da sake sake cikin zuciyata Har Nazo parking space, idanuna cikin na Aneeysa wadda ke tsaye da handbag hannunta, Tasha kwaliyya Kamar aljanna, se naji dariya na neman kubce min, amma nayi saurin maida ta saboda fitowar zaki. Tunda ya kalleni ya hade rai sannan yace

"Ke zo nan"

Babu musu naje inda yake, seda ya gama rufe seat dinshi sannan yace

"Gidan ubanwa zakije? Ba nace miki Aneeysa zata zo ba, ita kadai zaki Bari a gidan?"

Kallonta Nayi tana ta wani bubbude hanci Kamar bauna ita a dole me saurayi sannan nace

"Mama ta aikeni"

Daga Haka na juya nayi ficewata, a raina Ina ayyana da da Yanzun ba daya bane. Idan da na dauki irin wannan rainin Yanzun Bazan dauka ba, gidan ubanshi ne Kamar yadda yake gidan Ubana. Tunanin hakan se naji Kamar na zake, Kamar abinda na ayyana din ba haka bane.

Inata tafiya ran nan nawa a mugun hade, nayi kicin kicin a dole kada wani ya ganni Ya nuna interest dinshi a Kaina. A tunanina I want to cheat nature bansan cewa wani hakan da nake shi zai birgeshi a Kaina ba.

Tunda nayi sallama cikin gidan nasan more than something is wrong A'a many things are wrong and not in place. Gidan Gabaki daya a hautsine bawai babu Shara ba A'a Anyi Shara amma kwatakwata gidan tamkar babu mace a cikinshi. Babu Wanda ya amsa min sallamar a tunanina matar gidan tana dakinta, amma ina shiga parlon na tarar da ita a zaune ta zabga tagumi. Kawai se naji dariya Tana neman kubce min saboda kayan dake jikinta, Wani baggy skirt ne purple Wanda tsayinshi Har ciki ya Kai mata, saman shi riga ce ta bacci blue wadda tsayinta har gwiwa, Armless ce babu hannu, kanta wata bakar hula ce wadda tayi mata kadan duk gashin kanta ta keya Ya bayyana, ya cukurkude, in short tamkar wata sabuwar kamu Haka take, Idanunta sun kukkumbura Sunyi jawur dasu, Kamar wadda tayi kuka ko kuma babu issashen bacci. Se naji tausayinta Ya kamani because definitely something is wrong, A iya sanina da Anty Fadila ban taba ganinta a hargitse ba, she's the kwaliyya type komai in order.

Gefenta na zauna she was absent minded, deep in her thoughts da Har seda na tabata sannan tayi firgigit ta dubeni, muna hada ido ta dauke kanta tana kokarin mikewa. Hannunta na riko, amma Haka ta kwace ta shige dakinta ta kullo kofar. Mikewa nayi nai sororo Kamar doluwa. Meye nufin Anty Fadila? Me nayi mata? Shiru nayi Ina tariyo last encounter dinmu, to kodai ranar Hamma Mussadiq yayi mata wani abin akaina ne? Shiru nayi Inata tunanin possible abinda zai saka Anty Fadila yin fushi Dani, ganin babu ko abu daya dazan iya tunawa yasa kawai na cire veil dina na daura na shiga kitchen seda na toshe hancina saboda yadda yake tashi. Nade hannuna nayi na Fara wanke wanke, ina gamawa na hau share share da mopping, kafin wani lokaci kitchen din yayi tsaf Se na dakko tukunya na daura abincin dare tunda har biyar ta wuce. Ina cikin wanke shinkafa naji an rike Hannayena, dago idona nayi Ko ban kalla ba daga hannayen nasan Anty Fadila ce, kallon fuskarta nayi yadda take murtuk Kamar bata taba dariya ba, janyo ni ta dinga yi har seda muka zo kofar parlon ta sannan tace

"Fita min a gida, munafuka kawai! "

Tirjewa nayi na kwace hannun nawa nace

"Anty Fadila me yake damunki? Me ya faru? "

Hankade ni tayi, Ina iya hango hawaye yana taruwa a idonta, da yadda take battling dasu Dan kada su zuba, tayi nasara as a wannan lokacin ta maidasu, muryarta na rawa tace

"Tambayata kike? Nace ki fita min a gidannan, munafuka, macuciya kawai"

Zagin da tayi min ya bige ni saboda babu Wanda ya taba min irinshi, amma banma saka a raina ba, fatana kawai naji Meye matsalar,

HIKMAH Kde žijí příběhy. Začni objevovat